ALLAHU Akbar! A duk lokacin da aka yi rashin mutum, a kan yi tunanin ba za a taɓa mantawa da shi ba. Amma cikin ƙanƙanen lokaci, a kwana a tashi, dukkan abubuwan da ya yi a lokacin rayuwar sa zai zama tarihi.
An yi rashin ‘yan fim da dama a masana’antar Kannywood. Sun haɗa da darakta Tijjani Ibraheem, Balaraba Mohammed, Katakore, Shu’aibu Ƙulu, Ahmad S. Nuhu, Hussaina Tsigai, Jamila Haruna, Ɗanwanzan, A’isha Musa, Zulƙiflu Muhammad, Safiya Ahmad, Amina Garba (Dumba), Hawwa Ali Dodo, Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro), Lawal Ƙaura, A’isha Ɗankano, da dai sauran su.
Dukkan waɗannan ‘yan fim ne da su ka shahara, kuma su ka bada gagarumar gudunmawa ga cigaban Kannywood, amma a cikin su ɗaiɗaiku ne ake iya tunawa da ranar da su ka rasu. A ciki akwai Ahmad S. Nuhu, wanda ya rasu a ranar Litinin, 1 ga Janairu, 2007 sanadiyyar haɗarin mota a wajen Azare da ke Jihar Bauchi, a kan hanyar sa ta zuwa Jihar Barno. Sai kuma Hawwa Ali Dodo, wadda ta rasu a ranar Juma’a, 1 ga Janairu, 2010, ita ma sanadiyyar haɗarin mota a wajen Saminaka cikin Jihar Kaduna, a kan hanyar ta ta zuwa Kano daga Jos. Sai kuma Ibro, wanda shi kuma Allah ya ɗauki ran sa a kwanan wata mai kamar ta yau, wato Laraba, 10 ga Disamba, 2014 sanadiyyar ciwon ƙoda. A yau Talata, 10 ga Disamba, 2019 Ibro ya cika shekara biyar cur da rasuwa.
Tun jiya Litinin masoya da wasu daga cikin abokan sana’ar sa su ka fara yaɗa hotunan sa a soshiyal midiya su na rubuta gobe 10 ga Disamba, 2019 Ibro zai cika shekara 5 da rasuwa.
Marigayin ya samu addu’o’i daga masoyan sa bila’adadin har zuwa yau.
A soshiyal midiya kusan kullum tun bayan rasuwar Ibro ba a rasa wanda zai saka hoton sa ya yi masa addu’ar neman rahamar Ubangiji. Wannan ya nuna cewa kullum ya na cikin zukatan masoyan sa, ba su manta da shi ba, kuma shi ne jarumin da aka fi tunawa da shi bayan shi. Kuma har gobe mutane su na bibiyar finafinan sa, musamman irin su ‘Andamali’, ‘Na Mamajo’, ‘Ƙarangiya’, ‘Naira’, ‘Oga Abuja’, ‘Wuta Sallau’, da sauran su.
Duk a cikin jaruman da su ka rasu, har yanzu babu jarumin da aka samu makwafin sa. Duk wanda ya amsa kiran Allah da basirar sa ya ke tafiya.
Ibro jarumi ne da ba a taɓa yin irin sa ba a ɓangaren wasan barkwanci. Shi ne jarumin da ko juyi ya yi sai ya ba ka dariya, don shi ba sai ya yi magana ba zai saka mutum dariya. Duk da cewa bayan rasuwar sa akwai jarumai masu wasan barkwanci irin su Sulaiman Bosho, Rabi’u Daushe, Nura Ɗandolo, Ibrahim Gatari da sauran su waɗanda duk sun yi wasa tare da marigayin, amma har yanzu a cikin su an kasa samun wanda zai gaje shi; ko irin a samu wanda zai iya kwaikwayon salon wasan sa an rasa. Wannan ya nuna cewa Ibro ya tafi da baiwar sa har abada.
Allah Ya jiƙan sa da sauran mamata ‘yan Kannywood da rahama.
![]()







