• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shin ƙungiyar 13×13 ta yi tuntuɓe a tafiyar ta ne?

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 3, 2022
in Nijeriya
0
Aminu Alan Waƙa

Aminu Alan Waƙa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TUN bayan shigowar kakar zaɓen 2023 da a yanzu aka fara ake ganin kamar tafiyar ƙungiyar mawaƙa ta 13+13 ta samu matsala. Tunanin hakan ya faru ne saboda ganin yadda jiga-jigan tafiyar kowa ya kama gaban sa a wajen tafiyar siyasa.

Da man dai ba tun yanzu ba ake ganin idan har aka zo wannan lokacin to ƙungiyar za ta samu kan ta a cikin irin wannan yanayin saboda bambancin ra’ayin siyasa da ya ke tare da ‘yan ƙungiyar tun a baya, don haka ake ganin wannan tafiyar da za ta je ko’ina ba, duk da yake ta wuce lokacin da ake tunanin wargajewar ta.

A yanzu idan aka dubi tafiyar ‘yan ƙungiyar, za a ga kamar ta mutu ne ko kuma ta yi doguwar suma, saboda babu wani abu da ake gabatarwa da sunan 13+13 kamar yadda aka riƙa yi a baya. Haka ma sauran ‘yan ƙungiyar, kowa da inda ya sa gaba a harkar siyasa. Kamar shi jagoran tafiyar, Dauda Kahutu (Rarara), ya yi wani haɗin gambiza inda a matakin ƙasa ya ke tafiyar Bola Tinubu na APC, a Kano kuma ya na cikin tafiyar Sha’aban Ibrahim Sharaɗa na ADP. 

Mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala da jarumi Daddy Hikima sun fito takarar Majalisar Tarayya a ADP, amma a mataki na ƙasa ba mu ji su na tafiyar wani ɗan takara ba.

Umar M. Shareef tuni ya haɗe da Abdul Amart a tafiyar YBN su na ta tallar Tinubu, ƙungiyar da ba sa zama inuwa guda da 13+13  a baya, yayin da shi kuma Ali Isa Jita ya kama tallar Atiku Abubakar a mataki na ƙasa, a Jihar Kano kuma ya na cikin tafiyar NNPP ta Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ganin halin da tafiyar 13+13 ta ke ciki a yanzu, mujallar Fim ta tambayi ɗaya daga cikin shugabannin ta, Aminu Ala, idan ƙungiyar ta samu matsala ne a yanzu. 

Sai Ala ya ce: “To gaskiya ba wata matsala mu ka samu ba. Kamar yadda kowa ya sani, ita wannan ƙungiyar ta mawaƙa ce, kowa ya na da nasa ra’ayi na siyasa. To sai mu ka ce mu ajiye ra’ayi, a zo a haɗa kai don a taimaki juna a kuma taimaki jama’a. Kuma haka aka yi. 

“Kowa ya ga abubuwan da mu ka yi. Ba a taɓa samun wata ƙungiya da ta taimaka wa ‘ya’yan ta da kuma jama’a ba kamar 13+13.

“To a yanzu an zo wata gaɓa ne ta siyasa, kuma kowa da nasa gwanin. Don haka sai ƙungiya ta bai wa kowa dama ya je ya yi ra’ayin sa na siyasa, idan an gama, to kowa sai ya dawo a ci gaba da tafiyar ƙungiyar. Amma dai ba matsala aka samu ba, da amincewa aka yi wannan; kowa ya je ya yi ra’ayin sa.

“Don akwai wasu ma da za ka ga ba su da wani zaɓi a siyasa. Kamar ni, duk da ina takarar Majalisar Tarayya, amma da watan Mauludi ya kama sai kuma na koma waƙoƙin da na ke yi na Mauludi ne da ake gayyata ta gari-gari. To ka ga kowa da inda ya sa gaba.

“Don haka 13+13 ta na nan, kuma za mu dawo mu ci gaba da tafiyar da ita.”

Loading

Tags: Aminu AlaAtiku AbubakarBola TinubuDaddy HikimaDauda Rararaƙungiyar 13x13Majalisar TarayyamawaƙaRabiu Musa KwankwasosiyasatafiyaZaɓen 2023
Previous Post

INEC ta fito da matakai 4 na hana maguɗi a zaɓen 2023

Next Post

Amira Souley, ‘yar shekara 24, ta lashe Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Malama Amira Souley ta na karɓar kyautar karramawar ta a matsayin Gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 daga hannun Hajiya Gumsu Abacha Buni, matar gwamnan Jihar Yobe (Hoto: BBC Hausa)

Amira Souley, 'yar shekara 24, ta lashe Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!