WATO finafinan Hausa sun yi nisa wajen jan hankalin al’umma. Ko shakka babu wannan dama ce da za a yi amfani da ita wajen sauya tunanin al’umma zuwa ingantacciyar rayuwa da bin dokoki.
Kwanakin baya a kafofin sada zumunci har majalisu na unguwanni, maganar da na ji ana ta yi ita ce wai raba gardama ya bayyana. Da yake na kwana biyu ba na kallo, na ce wane ne wannan raba gardama? Ashe a cikin shirin ‘Labarina’ ne na Aminu Saira.
A satin nan da muka fita daga shi, sai na ji sabon batu. Ko’ina maganar Al’amin da Maryam ake, wasu na cewa ashe Al’amin babban attajiri ne ya yi ɓadda-bami don ya samu macen da take son sa.
Wasu kuma ji na yi suna cewa idan suka ga akasin haka, ma’ana marubuci da daraktan shirin sun nuna mafarki ne, ko Al’amin ya sayar da soyayyar sa to sun daina kallon series ɗin.
Nan na gyaɗa kai na ce lalle finafinan Hausa sun fara balaga. Domin wannan zai nuna yadda shirin ‘Labarina’ ya kama zukatan jama’a. Haka abin yake da shirin ‘Daɗin Kowa’ da ‘Kwana Casa’in’ tare da Gidan Badamasi.
Amma wataƙila mahukunta da masu ruwa da tsaki a cigaban ƙasa da tattalin arziƙi ba su fahimci lokaci ya yi da za su shiga harkar fim ɗin Hausa ba don saita tunanin al’umma.
Duk da ɗimbin masu kallon finafinan, har yanzu ana kyamar sana’ar ko harkar. Bayan ta zama kusan gidan kowa akwai.
Shekarun baya Gwamnatin Tarayya ta so ta yi sansanin shirya finafinai (Film Village) a Kano, amma aka yaƙi ƙudirin. Duk da cewa ba a daina fim ba a Kano, kuma masu kallon ƙaruwa suke a saƙo da loko.
Sai na ke ganin idan da an yi film village ɗin, wataƙila da an killace masu yin fim, tare da tsara musu dokoki bisa al’ada da addini.
Yanzu ba a daina fim ɗin ba. Asali ma kwararo da loko idan ka shiga, za ka tarar ana ɗaukar fim, inda za ka ga yara sun taru ana kallon taurarin fim duk da yadda wasun su ke ɓarin zance da mugun wasa.
Fitaccen shirin ‘Daɗin Kowa’ ana shirya wani ɓangare a Kawo da ke garin Kano. Kwanaki can ina kallon shirin, sai na ga an nuno wani gida da wasu taurarin shirin suka yi aure a ciki. Ko da aka shiga falon, nan na tabbatar ɗakin ƙanwar mahaifiya ta ne!
Wannan zai nuna cewa shirin ya shiga jama’a sosai. Shirin ya zama wani ɓangare na rayuwar su. Idan da wani abin ƙi, to an gudu ba a tsira ba. Tun da ba ta sake zani ba.
Shirin fim ba mai gushewa ba ne nan kusa. Ya kamata a karɓe shi hannu bibbiyu tare da tunanin yadda zai amfani jama’a ta hanyar da ta dace.
* Malam Zaharaddeen Ibrahim Kallah shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano