• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shirin ‘Makaranta’ da matsayin tace finafinai a Jigawa

by DAGA HASHIM ABDALLAH
January 15, 2022
in Tsokaci
0
Wani sashe daga cikin fim ɗin 'Makaranta' mai dogon zango

Wani sashe daga cikin fim ɗin 'Makaranta' mai dogon zango

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUK masu biye da labaran Sashen Hausa na BBC ya saurari yadda shugaban Hukumar Tace Finafinai, Adabi da Ɗab’i na Jihar Jigawa ya nuna damuwar sa kan yadda wasu ‘yan fim su ka mayar da Jigawa wata maɓoyar su. Gwamnati ta yi alwashin samo bakin zaren abin da wasu su ka ɗauka kamar sharar da abin ta yi a baya. 

A wannan rubutun, bari in fara da yabon irin wannan takwarar hukumar ta Jihar Kano kan yadda ta tsaya tsayin daka ganin cewa sun kare martabar al’umma ta hanyar tace ayyukan fasaha da yaɗa labarai da adabi. 

Kasantuwar Kano cibiyar Hausawa da al’adun su da adabin su, ita ce kan gaba wajen kiyaye wannan martaba kuma abin ya na aiki sosai. 

Wannan rubutun kar ya sa a ɗauka ina goyon bayan daƙile ayyukan hikima da basira ko fasaha ko yi masu linzami ɗaya har a ga kamar ina yin baki biyu ne. A’a, ina nan a kan baka na na cikakkken mai fafutukar ciyar da adabi gaba kuma ina jagorancin ƙungiyar marubuta, kuma zan ci gaba da koyar da adabi har kwanan gobe. Wato dai abubuwa daban-daban ne, fafutukar cigaban adabi, da kuma neman ganin ba a bar adabin haka sakaka ba. Ina neman sai an yi masa alƙibla ne domin dacewa da al’ummar da ya fito daga cikin ta. 

Kai ma mai karatu za ka yarda da ni, kuma ka fahimce ni, in na ce maka ni mutum ne da ya tsayu a kan dole adabi ya zama madubin rayuwar al’uma, yayin da kafar yaɗa labarai ta kasance wakiliyar al’ummar ta, fasaha kuma ta tabbata ta wakilci hikimomin inda ta fito. 
A wannnan yanayi da ake ciki na gurɓacewar tarbiyya ta zama babbar barazana ga al’umma irin tamu, ‘yancin kafofin sadarwa ya zama hatsari fiye da irin hatsarin da ake gani in an yi masa iyaka. Dole malamin makaranta kamar ni ya goyi bayan matakan hukumomi in ma ban sa hannu a daƙile fitsara da sunan wayewa ba, wadda ta fi komai zama babbar barazana ga al’umar mu fiye da komai, musamman al’ummar mu da ta sa neman alfanu ko darasin tarbiyya a aikin adabi ko fasaha a gaba fiye da nishaɗi da komai, ba za ta lamunci baɗala ba.

Jigawa a shirye ta ke ta yi maraba da baƙi ko masu yawon buɗe ido da kuma ‘yan fim amma waɗanda za su bi ƙa’idoji da doka da oda, kuma bisa tafarkin addini da al’adu

Mu kwana da sanin cewa in dai har Kano ce cibiyar Hausawa, ai kuwa Jigawa ce ta biyun ta, kasantuwar Jigawa yankin Kano ne masu al’uma da ginshiƙan su kamar addini da al’adu da harshe iri ɗaya, balle kafar sadarwa wadda ita ke isar da waɗannan ginshiƙan wanzuwar al’uma kamar yadda na ambato su.

To yayin da Jihar Kano ta dage wajen tsaftace ayyukan fasaha da sadarwa, sai wataƙila waɗanda ba su yarda da kan su ba su ka riƙa ƙaura zuwa Jigawa su ɗauki shirin da wataƙila su na ganin Kano ba za ta lamunta da shi ba. Da tunani mai kyau, mutanen Jigawa da gwamnati, har ma da mutane kamar ni mu ka yi maraba da su. Ta kai har muhimman wurare da ofisoshi manya da gine-gine masu tsada su na samun yin amfani da su a kyauta. An yi marabar ne tunda jihar ta zama wurin ziyarar al’uma a wata mahangar, wato da tunanin ko sun zo da wasu damarmaki da alkairai da hanyoyin samun kuɗin shiga domin akwai abubuwan nunawa a Jigawa da yawa na daga tarihi da wuraren ban-ta’ajibi, musammman a babban birnin zamani mai duwarwatsu da tuddai da dabinai irin Dutse.

Amma sai wannan ya kasance duk mafarki ne ake yi. Ko lokacin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Jigawa ta yi ta ƙoƙarin tsara komai, musammman ta fuskar neman masu shiryawar da su riƙa rajista da hukumar, sai su ka riƙa yin kunnen-uwar-shegu. Sai dai da faruwar wannan abin takaici, wato da fitowar sabon fim mai suna ‘Makaranta’ da aka yi shi a Jigawa, fim da ake ƙoƙarin koyar da jima’i da fitsara, hukumomi sun hasala, sun nuna fusatar su tare da shan alwashin tseratar da al’ummar Jigawa daga yunƙurin gurɓatarwar wasu tsiraru.

Duk da haka, Jigawa a shirye ta ke ta yi maraba da baƙi ko masu yawon buɗe ido da kuma ‘yan fim amma waɗanda za su bi ƙa’idoji da doka da oda, kuma bisa tafarkin addini da al’adu. Don haka, Jihar Jigawa da al’ummar ta a shirye su ke su karɓi baƙuncin waɗanda za su iya kawo waɗannnan abubuwa a Jigawa:

1. Ayyukan yi;

2. Nishaɗantarwa;

3. Kuɗin shiga ga ma’aikatu;

4. Bankaɗo tatrihi da kayan tarihin a jihar;

5. Baje-kolin kyawawan birane da garuruwa da albarkatun jihar;

Fostar fim ɗin ‘Makaranta’ na darakta Aminu Nasara

6. Bayyana wa duniya wuraren kallo da gine-gine da ma’adinai, misali irin su kogin da ya fara daga Ringim har ƙarshen Jigawa a Kirikasamma, da tuddai da duwarwatsun Kazaure da Dutse da zanen mutanen da na Birnin Kudu da koren dajin Baturiya mai tsuntsaye daga nisan duniya, irin su tsofaffin gine-gine da hanyoyin jirgin ƙasa a ma’adanar dalar gyaɗa da ke garuruwa irin su Malammadori;

7. Nuna tarihe-tarihen jihar daga ƙananan hukumomi 27 da ake da su; da kuma

8. Taimaka wa hukumomin da abin ya shafa wajen gudanar da ayyukan su.

* Hashim Abdallah Malamin adabi da harshe ne a Kwalajin Fasahohi ta Binyaminu Usman, Haɗeja, a Jihar Jigawa. Marubuci ne kuma mai shirya finafinai da bada umarni. Lambar waya: 08038662494; Imel: hashimabdallah38@gmail.com

Loading

Tags: Aminu NasaraFilm censorship in Nigeriailimin jima'iJigawa State Censorship BoardKannywoodKano censorshipMakaranta filmsex educationtourist attractions in Jigawawuraren buɗe ido
Previous Post

Layar zamani: An ƙi cin biri an ci dila

Next Post

INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabe a jihohi 4 a ranar 26 ga Fabrairu

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Mista Festus Okoye

INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabe a jihohi 4 a ranar 26 ga Fabrairu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!