TUN bayan zuwan sabuwar gwamnatin jam’iyyar NNPP a Kano jama’a a masana’antar finafinai ta Kannnywood su ka zuba idon su ga wanda za a naɗa shugaban Hukumar Tace Finafinai ta jihar domin maye gurbin Isma’il Na’abba (Afakallahu).
Akwai raɗe-raɗin daga majiya mai tushe da su ka tabbatar da cewar tuni har an yi wata ganawa tsakanin ‘yan fim da su ka yi tafiyar Kwankwasiyya da kuma gwamnati kan maganar shugabancin hukumar inda aka nemi su bayar da sunayen waɗanda su ke ganin sun dace da shugabancin domin gwamnati ta duba.
Haka kuma majiyar mujallar Fim ta tabbatar da cewa daga baya ma an amince da jerin waɗanda za a duba a zaɓi wanda ya cancanta a cikin su.
Fitattun waɗanda mujallar Fim ta gano cewar su na son a ba su kujerar sun haɗa da Abba El-Mustapha, Sunusi Oscar, Hamisu Iyan-Tama, Alhassan Kwalle, da Salisu Officer.
Don tabbar da maganar wakilin mu ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin su, amma dai wasu ba su ce da mu komai ba, ciki har da Abba El-Mustapha wanda ya na cikin sahu na gaba na waɗanda ake yi wa zaton za su iya samun kujerar. Shi ma Oscar da mu ka tuntuɓe shi cewa ya yi bai san da maganar ba, kuma ma shi ba ya buƙatar samun kujerar.
Shi kuma Alhassan Kwalle, cewa ya yi: “Ni a gani na ya fi kamata a samu wanda zai kawo cigaban harkar fim da kuma Jihar Kano ko a cikin ‘yan fim ne ko a waje. Amma dai in son samu ne ya zama ba a cikin ‘yan fim ɗin za a samar da wanda zai zama shugaban Hukumar Tace Finafinai ba.”
Da yake abin da ya shafi masana’antar fim ne, mun ji ta bakin wasu daga cikin dattawan harkar. Ɗaya daga cikin su, Malam Ahmad Salihu Alkanawy, ya bayyana mana cewa: “Ya kamata a samar da wanda ya san masana’antar fim kuma ya ke da ilimi a kan harkar fim da kuma ilimin zama da jama’a ko a cikin ‘yan fim ɗin ko a waje.”
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, cewa ya yi: “Abu mai muhimmanci shi ne a bai wa mutumin da ya ke da kyakkyawar alaƙa da mutane, kuma ya ke da kishin masana’antar fim ɗin don ya kawo cigaba a cikin ta. Don haka ya kamata ya zama ɗan fim ne zai zama shugaban hukumar. Amma ya zama mai ilimi da kuma wayewa, sannan ya zama mai iya mu’amala da waɗanda ya ke shugabanta”.
A yanzu dai magana mafi ƙarfi ita ce ‘yan fim uku ne su ke kan gaba wajen neman zama shugaban hukumar: Abba El-Mustapha, Hamisu Iyan-Tama da Salisu Officer. In dai ɗan fim za a bai wa kujerar, to a cikin su ne ake kyautata zaton Gwamna Abba Kabir Yusuf zai ɗauka.
Ta yiwu kuma wani daban – a cikin industiri ko a wajen ta. Yanzu dai ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.