• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shugabancin MOPPAN: Gidauniyar Kannywood da Kwamitin Zartaswa sun taya Habibu Barde murna

by ABBA MUHAMMAD
February 5, 2024
in Labarai
0
Shugabancin MOPPAN: Gidauniyar Kannywood da Kwamitin Zartaswa sun taya Habibu Barde murna

Daga hagu: Kabiru Maikaba, Habibu Barde, da Ahmad Hashim

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GIDAUNIYAR Kannywood, wato ‘Kannywood Foundation’, tare da Babban Kwamitin Zartaswa na MOPPAN, sun taya sabon shugaban riƙo na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Habibu Barde Muhammad, murnar samun shugabancin ƙungiyar da ya yi.

Jami’in hulɗa da jama’a da kyautata al’amuran sadarwa na Gidauniyar Kannywood, jarumi Alhaji Muhammad Kabiru Maikaba, shi ne wanda ya ba da sanarwar taya murnar a madadin gidauniyar.

Maikaba ya ce, “Shugabanci da illahirin al’ummar wannan gidauniya mai albarka na farin cikin taya babban Kwamitin Dattawan Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Sana’ar Finafinan Hausa ta Ƙasa, wato MOPPAN, da irin zuzzurfan tunani da dogon hangen nesa da su ka yi amfani da shi wajen zaƙulo Alhaji Habibu Barde don zama shugaban riƙo na wannan gagarumar ƙungiya ta ƙasa (MOPPAN).

“Haƙiƙa shugabancin wannan gidauniya da mafi yawa na al’ummar wannan masana’anta mai albarka sun yi na’am da marhabin da wannan zaɓi.

“Sanin kowa ne cewa Alhaji Habibu mutumin ƙwarai ne, adali kuma zaƙaƙuri.

“Don haka mu na taya ka murna kuma mu na yi maka addu’ar Allah (SWT) ya taya ka riƙo, kuma ya albarkaci wannan nauyi da ya ɗora maka kuma ya sa ka sauke lafiya.

“Gaba ɗayan mu daga Kannywood Foundation mu na yi maka fatan alkhairi. Mun gode.”

Shi ma a nasa ɓangaren, Babban Kwamitin Zartaswa na MOPPAN (National Central Working Committee, NCWC) ya taya murna ga sabon shugaban riƙon ƙungiyar.

Saƙon taya murnar da ya fito ta hannun sakataren kwamitin, Dakta Ahmad Hashim, ya ce, “A madadin wannan kwamiti mai suna a sama mu na taya sabon shugaban riƙo na MOPPAN, Alhaji Habibu Barde, murnar samun wannan matsayi.

“Mu na yi masa addu’ar Allah ya yi riƙo da hannayen sa, kuma ya ba shi ikon sauke wanann nauyin da aka ɗora masa.

“A matsayin mu na kwamiti wanda shugaban MOPPAN na ƙasa ya ke shugabanta, za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sabon shugaba don ganin an ciyar da wannan ƙungiya gaba da ikon Allah da amincewar sa.

“Daga ƙarshe, mu na miƙa saƙon godiyar mu zuwa ga shugaba mai murabus, wato Dakta Ahmad Sarari, bisa kyakkyawan shugabancin wannan kwamiti da kuma MOPPAN baki ɗaya. Mu na masa fatar alheri.”

Loading

Tags: Ahmad HashimHabibu Barde MuhammadKabiru MaikabaKannywood Foundation
Previous Post

‘Yan Kannywood za su yi wa Ali Nuhu dinar taya murna a yau

Next Post

Naɗin Ali Nuhu shugaban NFC babbar dama ce ga Kannywood, cewar Abdulkareem Mohammed a wurin dinar taya murna

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Naɗin Ali Nuhu shugaban NFC babbar dama ce ga Kannywood, cewar Abdulkareem Mohammed a wurin dinar taya murna

Naɗin Ali Nuhu shugaban NFC babbar dama ce ga Kannywood, cewar Abdulkareem Mohammed a wurin dinar taya murna

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!