MATAIMAKIN shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Malam Suleiman Sha’ani, ya bayyana cewa shugabannin baya ba su bar ko sisi a asusun ƙungiyar ba.
A ranar Asabar, 27 ga Nuwamba, 2021 ne MOPPAN reshen Jihar Kaduna ta gudanar da zaɓen shugabannin ta, inda aka zaɓi Alhaji Hamisu Jibril Goma ya zama shugaba. Shekara biyu da aka yi zaɓen, membobin ƙungiyar su na ta ƙorafin cewa har yanzu babu wani abin a zo a gani da zaɓaɓɓun shugabannin su ka yi.
Sha’ani ya na magana da mujallar Fim ne kan wannan ƙorafin, ya na cewa a yanzu su na yin dukkan mai yiwuwa ne domin ganin sun sama wa ƙungiyar kuɗi don su ci gaba da aiki, tunda su na da sauran lokaci.
Ya ƙara da cewa: “Duk mulkin duniya ƙorafe-ƙorafe ba a rasa shi. Ba zan manta ba, tun mu na kwana goma wani ya fara ƙorafi. To ka san duk abin da za a yi sai da kuɗi.
“Ba irin mulkin Nijeriya ba ne da za a ce ƙila akwai hanyoyin da kuɗi su ke shigowa ko kuma ka samu wasu kuɗi a ƙasa. Ka ga sai ka fara tafiyar da ayyuka. Duk abin da za ka yi sai da kuɗi, don haka ba wani kuɗi gwamnatin baya ta bar mana ba ko wata hanyar kuɗi, mu ne za mu nemo, mu san yadda za mu yi.”
Sha’ani ya ci gaba da cewa, “A lokacin da mu ka karɓi mulki, babu komai a asusun MOPPAN na Jihar Kaduna. Ka ga yanzu ba kowa ba ne zai san ya za ka yi ka samu kuɗi ba, domin ka zo ka fara gudanar da ayyuka.
“Kowa ya san yanayin yadda harkar ta ke. Amma ka san abu ne a buɗe, shekara biyu ne ba maganar shekara huɗu ba ne. Ko gwamnatin Nijeriya sai da ta shekara huɗu ba a yi komai ba, sai a na biyar zuwa na takwas aka fara ganin ayyuka, ballatana MOPPAN da ba ta da ko sisi a ƙasa.
“Ni wannan maganar da na ke yi maka, ina yi tsakani da Allah ne. Shekara biyu, to ko shekara biyun ma bai yi ba. Amma idan ka duba, za ka ga wani masoyi ne ya ƙosa ya ga ka yi abin da zai sa shi farin ciki, wani kuma maƙiyi ne, da ma haka ya ke so, tunda da ma ba da shi aka zaɓi gwamnatin ba. Amma sai mu ka ɗauke shi ‘challenge’, ka ga in ka ɗauke shi haka, sai ku yi shiru ku riƙa shirye-shiryen ku a hankali.
“Yanzu ga shi kuma abin ya zo mana a lokacin siyasa, sai abubuwan kuma gaba ɗaya su ka rikirkice mana. Ni nan Suleiman Sha’ani ni na kawo shawara na ce tunda su na ta ƙorafi, har da wasu ciyamomi na ‘guilds’, wanda kusan su su ka assasa waɗannan maganganun, sai na ce kada su manta su ma ciyamomi ne, kuma masu zaman kan su, su dai su ka haɗu su ka yi mu, amma su ma su na iya zuwa su je su nemo kuɗin su su je su yi wani abu daban. Ba dole sai sun jira MOPPAN ba. To amma tunda sun yi ƙorafi bari a kira su a ba su ‘assignment’: ‘kai wane mu na so mu ga membobin ka, domin mu san yawan su, kafin mu san ta inda za a fara’. Har yanzu dai shiru ka ke ji. Bban san ko sun gama tantancewa ta ɓangaren su ba.
“Ka ga dai MOPPAN su su ka haɗu su ka yi mu. Ka ga babu wani abu da za mu yi sai da yawun su. Har yanzu ban ji an ce ga wata ‘guild’ ta gama tantancewa ba. Mu kuma sakamakon da za su kawo, shi ne za mu san abin da za mu yi.
“Ƙorafin su kullum shi ne har yanzu ga shi ana samun ‘loan’ a ko’ina da sauran su. Abin da su ke so kawai ina za a samu kuɗi, a kawo kuɗi. Kuma duk abin da ba kai ba ne a wurin dole za ka yi surutu.”
Sha’ani ya ce, “Shirin na MOPPAN reshen Jihar Kaduna, mun fara shiga gwamnati ne, domin gwamnati ta san da mu, wanda in mu ka kawo tsare-tsare da dokoki gwamnati ta san mu na tare da ita, ta na tare da mu.
“Duk abin da babu gwamnati a ciki akwai shirme ake yi.
“Mu dai yanzu mu na ta shiga da fita a gwamnati har sai ta san da mu. Idan ka shiga gwamnati, in wasu kuɗi za su fito ko wata harka za a yi da kai. Duk baƙi masu zuwa daga wani wuri su na yin abin da su ka dama, gwamnati su ta sani, kuma ita ke neman su. Wannan shi ne shirin da mu ka tunkara yanzu.”