A CIKIN ‘yan kwanakin nan biyu, wata rigima ta ruru a tsakanin wasu sanannun mawaƙa biyu da ke Kaduna, wato El-Mu’az Muhammad Birniwa da Amina Abdullahi, wadda aka fi sani da Ummi B.Y.
Dukkan su sun jefi juna da magana, ciki har da zargin kawalci da mawaƙiyar ta yi wa fitaccen mawaƙin.
Amma dai shi ya musanta zargi, ya ba da nasa labarin na abin da ya ce ya faru a tsakanin su.
Taƙaddamar dai ta samo asali ne tun kimanin wata biyu da su ka wuce, lokacin da El-Mu’az ya wallafa wani saƙon shawara ga jama’a a WhatsApp, wanda Ummi ta yi zargin ita ya ke yi wa habaici saboda ta taɓa neman taimako daga gare shi. Hakan ya sa ta mayar masa da baƙar magana.
Mujallar Fim ta tattauna da kowannen su kan yadda abin ya faru.
Ummi ce ta fara ba mu labarin, ta ce sakamakon abin da ya faru tsakanin su, El-Mu’az ya yi barazanar cewa zai yi “maganin ta, sai dai in za ta daina yawo a gari gaba ɗaya.”
Tun da farko dai Ummi ta shaida wa mujallar Fim cewa akwai wani lokaci da ta yi wa Janar Tukur Buratai waƙa, sai ta nemi El-Mu’az ya haɗa ta da shi, amma sai ya ce mata sai dai ta ba shi waƙar ya kai masa, in ya buƙaci a kawo masa ita, sai ya kai ta. Ta ba shi waƙar.
Ana nan, rannan ta na makaranta sai El-Mu’az ya kira ta, ya ce ta zo. Ta tafi ta same shi tare da wani mutum a Asaa Pyramid Hotel, Kaduna. Da ta tashi tafiya, sai El-Mu’az ya ce mata ai a nan za ta kwana tare da wannan mutumin. Sai ta ce masa ita wannan ba aikin ta ba ne, don haka ba za ta iya ba.
Ta ce a tunanin ta, tun daga wannan lokacin ne El-Mu’az ya ƙullace ta, shi ya sa ya ƙi taimakon ta.
Ana nan, ta na riƙe da abin a ran ta, rannan sai ta samu damar yi masa magana. Wani rubutu ya yi wanda ta ke ganin da ita ya ke.
Ta ce, “Akwai ‘posting’ da ya yi a ‘status’ ɗin sa na WhatsApp, ya na irin habaici, ya na cewa irin ka nemi na kan ka, in ka zauna sai an ba ka, ka na ruwa, irin dai Hausan nan. Ni kuma sai na rubuta masa (martani), na ce, ‘Alhamdu lillah, ko shugaban ƙasar mu, Muhammadu Buhari, idan talakan shi na ƙasa da shi ya ɗauko kyauta – ko da naira biyar ne – ya ce, ‘Ga shi na ba ka domin kyautatawa’, zai yi alfahari, duk da ya na da arzikin, ba wai bai da shi ba, amma ƙauna ce ta sa har aka ɗauka aka ba shi.
“Na ce kuma, ‘Ya kamata duk inda babba ya ke, ya ji tausayin na ƙasa, ya taimaka wa na ƙasa; taimako ba wai na kuɗi ba, taimako ko na aikin nan. Ka na da hanyar da za ka samu ka taimaki na ƙasan da ya ke aikin nan da bai san mutane ba, ka taimaka masa, ba sai ka ba shi duniya ba. A harkar bizines ma akwai taimako’.
“Na ce, ‘In ka taimaka wa mutum, kai ma Allah ya ba ka, kuma ka ji daɗi, in ya ba ka kuma kai ma ka kyautata wa wani, sai ya ƙara maka’.
“Na kuma ce masa, ‘Kai ma karan kan ka, da babu taimako da ba za ka je ko’ina ba’.”
A cewar ta, El-Mu’az na ganin saƙon ta sai ya buga mata waya. Idan kun tuna, da man ta na ƙullace da shi.

Ta ce: “Shi ne sai ya kira ni, ya ce min, ‘Menene tsakani na da ke da ki ka cusa min wannan magana?’ Sai na ce, ‘Alhamdu lillah, da ma na yi tunanin za ka kira, kuma sai ga shi ka kira!’
“Sai na ce, ‘Ka manta da aka yi kaza, aka yi kaza?’ Kawai buɗe bakin sa sai ya ce, ‘Sai na ci kaza-kazan ki, don kaza-kazan ki!’
“Ni ma sai na ce, ‘Ba dai kaza na ba, sai dai kazan ka!’
“Misali, in bai zage ni ba, zan zage shi? Ita rayuwa, idan ka na tare da mutum, kuma ya na mutunta ka… Shi karan kan shi ba zai ce ba na mutunta shi ba; ina tura masa saƙo duk ranar Juma’a.
“Na ce, ‘Ci da ni ka ke yi ko kuma shayar da ni ka ke yi ko kuma ka na taimako na ta wani fanni na bizines ɗi na?’ Shi ne ya ce sai dai in ba zan yi yawo ba, ya faɗa wa yaran shi, sai dai in zan dauwama a cikin gida. Ya turo min ‘voice’ ta WhatsApp, har ya na rantsuwa da Ubangiji (cewa) sai dai in ba zan yi rayuwa in fito waje ba, sai na ga abin da zai aikata min!”
Ummi ta ce sakamakon wannan barazanar ga rayuwar ta da mawaƙin ya yi, ta kai rahoto ga hukumar ‘yan sanda ta Kaduna saboda kada a wayi gari wani abu ya faru gare ta, musamman tunda ya nuna cewa ya sa yaran sa su ɗauki mataki a kan ta.
Ta ce: ” “Na kai ‘report’ wurin kwamishinan ‘yan sanda; na faɗa wa mahaifi na, ya ba ni lambar kwamishinan ‘yan sanda in yi ‘report’. Saboda rayuwa ta lalace, kuma ka ga yadda rayuwa ke tafiya. Ɗan’adam ne, ba ka san me ke cikin zuciyar sa ba.”
Shin ko ta kai ƙara wurin shugabannin masana’antar Kannywood don su shiga tsakani kuwa? Sai ta amsa da cewa, “Gaskiya ni ban faɗa wa kowa ba.”
Mawaƙiyar ta ce El-Mu’az ya ba wasu mutane da ke tare da shi lambar ta, su na kiran ta su na cewa “wai in ba shi haƙuri.”
A cewar ta, irin waɗannan mutanen sun haɗa da jaruma kuma furodusar nan da ke Kano, Hannatu Bashir, wadda aminiyar sa ce.
Ummi ta ce: “Hannatu Bashir ta kira ni, sai kuma wani Sulaiman daga Zariya, wai dole, dole sai dai in kira shi in ba shi haƙuri. Ni kuma na ce ba zan ba shi haƙuri ba in za a mutu ana abu ɗaya. Wannan iƙirarin da ya yi min, mummunan iƙirari ya yi.
“Sannan na ce masa ni da Ubangiji na dogara. Sai ya ce sai ya ga uban da ya sa ni, kuma sai ya ga uban da ya tsaya min.”
Shin me Ummi ta ke so duniya ta sani game da wannan abu? Ta ce ta na so ne duniya ta san halin da ta ke ciki, “saboda iƙirarin da ya yin ya nuna cewa ko da wani abu zai same ni, shi ne.”
Da mujallar Fim ta tuntuɓi El-Mu’az game da wannan lamari, sai ya ce, “Ni ba ni da wani kes da ita. Abin da ya faru ya faru ‘for the past two months’, kuma an ba ni haƙuri, ya wuce. Ka ga in da wani abu, ita ce ta ke so ta tada shi.
“Yanzu kamar ni, Allah na tuba, astagafirullahi, wannan yariyar sai a ce ni ina kes da ita ko na ce wani abu? Ai Malam Abba da mata da maza a ofis ɗi na babu wanda bai fi ƙarfin wannan yarinyar ba. Babu wanda Allah bai yi wa luɗufi da ɗaukakar da ya fi na wannan yarinyar ba. To, ko su a cikin su wani ya tsaya zai yi wani abu da ita zai zama wani iri; ni kai na ba zan yarda ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da abin ya faru, ‘posting’ na yi a kan mutane su yi ƙoƙarin dogaro da kai, kar ka jira a ba ka, daga lokacin da ka ke jira a ba ka za ka samu matsala.
“Sai ta yi min ‘comment’, ta ce ni ma jira na ke ana ba ni. Sai na ɗaga ɗayar waya ta – ba ta da layin da na kira ta da shi – na ce mata, ‘Meye haɗin ki da ni?’ Sai ta ce ai ta nemi taimako na ban taimake ta ba, mahaifiyar ta ta na asibiti. Na ce, ‘Ni yaushe na san ki?’ Ta kuma ce ta yi wa Zailani waƙa ya ce in kai ta. Na ce, ‘Sifikan?’ Sai na ce, ‘Me ya sa shi bai kira ni ya ce in kai ki ba, ke ya kira, ya ce ki kira ni in kai ki?’ Na ce, ‘Ni in wurin ‘Speaker’ ne, wanda bai ce in kai shi ba ma ina kai shi, ballatana wanda ya ce in kai. Akwai wasu abubuwan ma da idan aka yi masa, ni na ke ɗaukar nauyin abin, in dai bai fi ƙarfi na ba.’
“Sai ta nemi ta yi min rashin kunya. Sai na ce mata in akwai wanda ya fi ƙarfin ta ma, ni na fi ƙarfin sa, na zazzage ta. Ta rama zagi, ta yi min cin mutunci, duk ina jin ta.
“Da ma can ta na zuwa wurin Hannatu Bashir ta ce ta saka ta a fim, har ta na ce wa Hannatu ita ‘yar Birnin Yero ce, ‘yar Kaduna ce, daga nan ta ke. In ta ce daga wurin mu ta ke, ka san za a yi mata alfarma, ka dai san yadda abin ya ke a sa mutum a ‘scene’.
“Na kira ta (Hannatu) na ce mata, ‘Ko za ki iya tuna wannan yarinyar kaza, kaza, kaza?’ Ta ce, ‘E.’ Sai na ce mata, ‘Ni na fita harkar ta ne saboda wani ‘chat’ da ta yi min. Ta yi min ‘chat’ ta ce in haɗa ta da wanda za ta samu kuɗi.’ Sai na ce wanda za ta samu kuɗi, ‘as in how?’ Wai ni in gane mana!
“Wannan labarin da na ke ba ka, ‘voice note’ ne ta yi min, amma irin ‘voice note’ ɗin nan ne da yanzu in ka danna zai ce maka an goge, ‘ask wanda ya turo maka ya sake turo maka.’ Amma ni da ya ke amsar da na ba ta da rubutu ne, ya na nan. Na ce mata, ‘Ni ba kawali ba ne, ban taɓa yi ba, kuma ba zan yi ba.’
“Sai ta sake yi min ‘voice note’. Sai ta sauka daga wancan layin. (Ta ce) akwai waƙa da ta yi wa Zailani, kaza, kaza, kaza, ‘kuma ban samu ganin shi ba; so, ko za ka haɗa ni da wani in yi masa?’
“Duka na yi ‘snapping’ na tura wa Hannatu. Amma dai wancan ‘voice’ ɗin babu shi.
“Tun daga wannan ban sake kula ta ba a rayuwa. Ko da ta turo min wani bidiyo maman ta ba ta da lafiya, kawai na manta da ita. Wanda bai nemi ka taimake shi ba ya zo da wannan sigar ai ka ga ba abokin hulɗa ba ne!
“Na ce mata (Hannatun): ‘Wannan shi ne abin da ya faru. Amma ki kira ta ki yi ‘advising’ ɗin ta, wallahi tallahi ko yara na su ka ji irin wannan cin mutuncin da ta yi min sai fita ya gagare ta!’
“Na kira Salisu nawa, na ce ya yi ‘addressing’ ɗin ta. Shi ne ‘chief security officer’ a ofis ɗin mu. Na yi masa ‘voice note’, na ce ya tura mata ta ji, ‘in ta ce ni za ta yi wa iskanci ne ko za ta yi wa rashin kunya, wallahi fita ta yi yawo sai ya gagare ta!’
“Ya kira ta su ka yi magana, har lokacin ma ta ce masa ba ta gari. Da ya ke lokacin duk su Baban Kausar su na nan, za mu yi tafiya ne, mu na da yawa, sai kowa ya ke cewa don Allah a yi haƙuri, a bar maganar nan ya wuce. Na ce wallahi ya wuce, shi kenan.
“Ashe Baban Kausar ya na da ‘chat’ da ta tuttura masa da waƙoƙi, cewa don Allah ta na roƙon arziƙi ta dawo ofis ɗi na ta zauna. Ni kuma na san ta ‘for the past ten years’, kawai dai ni ban yarda da natsuwar ta ba ne da kamun kai da tsari. Wanda su ka zo daga baya ma wallahi duk ina tare da su, duk ga su nan, su Farida Ajebo, su Zarah, duka su na nan. Ka ga a tsawon shekarun nan ai ya kamata a ce ta na tare da mu. So, aka dai ce in yi haƙuri, na ce wallahi ya wuce. Shi ya sa na ce wa Baban Kausar yanzu kuma daga baya a zo a ce na ce wani abu? Ni, Allah na tuba, astagafirullah, yanzu ko ba Ummi ba, Baban Kausar, duk wanda na ware wa minti talatin ina neman shi in dai ya na numfashi zan same shi, domin daidai gwargwado ina da ‘influence’ ɗin da zan iya sawa a kama min mutum ko a ina ya ke. Na ce ba ni da wani bizines da ita, amma in ba haka ba an yi abu wurin wata biyu, kuma yanzu a zo a tado da magana?
“Amman a yi mata uzuri, ƙila ko ta na so ne ta yi suna ko wani abu makamancin wannan, a ce ta yi abu da wani wanda fitacce ne. Amma ni ai yanzu abin kunya ne a ce ta yi wani abu ina ‘responding’ a kai. Amma na ce dai ba damuwa, in Abba ya kira ni, ko ni na kira shi zan faɗa masa ni ba ni da wani ‘response’ a kan ta. Sai dai in ita ce ta ke da wata magana da ta ke so. Amma wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru.
“Kuma ba buƙata ta ba ne a ce, an ce na ce wani abu. Abin da ta yi min dai ya faru, ya wuce, sai in ita ce ta ke so lallai-lallai sai ta ja abin, sai in ɗauki ‘legal action’ saboda in yi ‘protecting’ mutunci na.”
Bayan kimanin minti biyar da mujallar Fim ta yi magana da El-Mu’az, sai ga kiran Ummi, ta na faɗin cewa ga El-Mu’az nan ya turo wasu mutane, sun ce su ‘yan sanda ne, waɗanda aƙalla sun kai su goma, wai sun zo kama ta, amma dukkan su babu wanda ya saka yunifom a jikin sa, har da mace ɗaya a cikin su.
Nan take wakilin mu ya sake kiran El-Mu’az don ya ji ko ya na da masaniya a kan hakan. Da ya ɗaga wayar, wakilin mu ya ce masa, “Ummi ta kira waya ta na cewa ka tura ‘yan sanda su kama ta.” Sai ya ce, “Ba ni minti ɗaya, zan kira ka.”
Daga baya ya kira, ya ce, “Bayan mun yi magana da Baban Kausar, na ce masa ya kira Hannatu tun wancan lokacin. Ita ta kira ta ta yi ‘addressing’ ɗin ta, tunda wurin ta ta ke zuwa ta ɗan saka ta a fim. Ta ce mata, ‘Ke yanzu in ban da abin ki, yadda Baban Zarah ya ke ƙoƙarin ya taimake ku ku ‘yan Kaduna, har za ki iya buɗe baki ki zage shi kowane irin zagi zai yi miki? Kin yi rashin kunya!’
“Wannan ne ya sa na ce Baban Kausar ya kira ta. Sai Baban Kausar ya kira Hannatu. Hannatu ta ce, ‘Baban Kausar riƙe waya bari in kira ta in ji me kuma yin hira ko cewa wani abu.’
“Saboda haka da aka kira ta, sai Hannatu ta ce mata, ‘Me ya sa za ki yi haka, magana ta riga ta mutu?’ Sai ta kufce, sai ta ce, ‘Ai kawalcin ki ya ke yi, shi ya sa za ki kare shi! Ai kawalin ki ne, ya na kai ki ki na samun kuɗi!’
“Duk Baban Kausar na ji (ta na cewa): ‘’Yar kaza-kaza!’ Sai zagi: ‘Ai ni ma ran da na fara sanin shi a duniya kawalci na ya yi, ya kira ni Asaa Pyramid Hotel. Akwai wasu masu gidan shi a wurin. Na tashi zan tafi, sai ya ce, ‘Ke da za ki zauna a nan’. Sai na ce, ‘Ni ba sana’a ta ba ce’.
“Wannan labarin da na ke ba ka, akwai a wayar Baban Kausar duka.
“So, a wurin shi Sani ya fita daga ofis ɗin mu, ya je ya samu Difi’o a Maraban Jos, Difi’o ya ba shi ‘team’ na ‘police’ ya ce a je a zo da ita.
“Amma kamar ta ce ba za ta fito ba. An kira baban ta, ya ce ya na Maraban Jos. An ce to ya zauna a ‘police station’ kafin ta zo.
“So, baban ya ce zai yi magana da ita ta zo ta same shi.
“Ya na da kyau ta je kotu ta yi “defending’ waɗancan maganganun: an so a yi kawalcin ta, kuma ita ma waccan ana yi mata. Ya kamata ta je duk ta yi wannan bayanin. Yanzu na kira shi Sani, ya ce min da gaske ne.”
Sai El-Mu’az ya ce: “Ga Baban Kausar.”
Sagir Baban Kausar ya ce wa mujallar Fim: “Kamar yadda ya faɗa maka, abin da ya faru kenan. Ita Hannatu da ta kira ta da tunanin cewa a samu mafita, sai kuma ta koma duk ta bi kowa ta zage. Ta ke cewa ita kawalcin ta ma aka nemi a yi. Wannan dalilin ita Hannatu ta ke cewa wallahi ko shi ya bari, ita sai ta ɗauki mataki. Wannan shi ne abin da ya faru.”
Wato kes ɗin ya koma kan Hannatu kenan?
“E to, ya koma kan Hannatu, tunda ga ta ga Hannatu,” inji Baban Kausar. Ya ƙara da cewa, “To shi ɗin ma in ka ji wani zagi da ta yi masa, sai da ta kira sunan shi ma ta zaga, a yanzu ɗin ma. To ka ga yanzu gaba ɗaya ba ma maganar sulhun ta ke tunani ba ko nadamar wani abu, ba shi ta ke yi ba. To shi ne abin da zai ɓata maka rai. Kai da ake neman mafita, kuma ka koma ka ɗebo wani zafi. Kowa ta haɗa ta zage, har ta na maganar ta ma kai kes ɗin wurin kwamishinan ‘yan sanda. Ka ga kenan ta riga ta yi wa abin tanadi.
“Mu dai yanzu za mu nemi shawarar lauyoyi tukuna. Ko za mu yi magana da ku za mu nemi shawarar lauyoyi. Idan sun ce a yi, za mu kira ka mu yi hirar. Mu na da abin cewa. Amma tunda mu na shirin tafiya kotu ne, bari mu ji abin da lauyoyi za su ce.”
Da wakilin mu ya tambayi Ummi B.Y. ta idan za ta yarda a sulhunta ta da El-Mu’az, sai ta amsa da cewa: “Maganar sulhu, wannan magana ce daban, saboda ai sulhu kala-kala ne. Ni duk abu da cin mutunci ba ƙaunar sa na ke yi ba. Zan iya ce maka kaf industiri babu wanda zan ce maka ga shi ya wannan ɗi na, akwai abin da ya haɗa ni da saura. Ai idan mutum bai taimake ka ba, Ubangiji bai kawo lokaci ba ne, in Allah ya kawo lokaci wannan ‘normal’.”
Tambaya: “In shugabanni su ka shiga cikin maganar, su ka nemi a zauna ku yafe wa juna, za ki saurare su?”
Ummi ta ce, “Ba ka ji ba ka ce shugabanni? Ai duk inda aka ce wannan shugaba ne, kuma in shugaba mai adalci ne, dole za ka saurare shi, in dai shugaban ya san abin da ya ke yi, don haka dole ka tsaya ka saurari shugaba. Ko’ina akwai shugaba. Ubangiji ma cewa ya yi mu yi biyayya ga shugaba.”
![]()







