AN ci moriyar ganga an yada kwauren ta kenan? Wannan tambayar ce wasu ke yi bayan da mawaƙiya Fati Nijar ta fito ta koka kan yadda ta ce an yi masu “kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi” wajen tallar ‘yan siyasa.
A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, Fati, wadda cikakken sunan ta Binta Labaran, ta yi nuni da cewa “idan mutum bai yi a hankali ba sai ‘yan siyasa sun kai shi sun baro shi.”
Ta ce ‘yan Kannywood sun sha wahala lungu da saƙo su na tallar wasu ‘yan takara amma da ta je gidan ɗaya daga cikin su sai aka hana ta ganin sa.
Ta ci gaba da cewa amma kwatsam sai ga shi an ajiye su a gefe ana yi da waɗanda su ka zo a bayan bayan su, ba su san ma wahalar da su ka sha ba.
Fati ta ƙara da cewa a jira ta za ta yi hira da ‘yan jarida inda a nan ne za ta fayyace abubuwa da yawa.
Wasu na ganin wannan badaƙalar ba ta rasa nasaba da dawowar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da jama’ar sa tafiyar ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Gawuna, bayan ya ga kamar zai yi nasara a zaɓen da za a yi ran Asabar mai zuwa. Rarara ya watsar da tallar Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharaɗa.
A ganin masu nazarin lamarin, hakan ne ya sa mawaka irin su Fati Nijar su ke ganin an watsar da su an kama Rarara.