ASALIN KALMAR ‘FULANI’
MALAM Ahmad Usman Bello, shugaban ƙungiyar Fulani ta ƙasa mai suna ‘Fulani Development Association of Nigeria’ (FULDAN), Bafullatani ne Batoranke, kuma masani a kan tarihin jinsin sa. A wata zantawa da mu ka yi da shi, ya faɗa mana wasu ƙarin mahangai game da tarihin Fulani.
Da fari dai, masanin ya faɗa cewar tabbataccen tarihi shi ne wanda ya zo a Alƙur’ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shi ba kan iya zamowa gurɓatacce, don haka bai ɗoru a kan cewa wajibin duk abin da ya faɗa shi ne na gaskiya ba.
A cewar sa, asalin sunan Fulani shi ne Futa (Futa Toro), kuma suna cikin tsofaffin ƙabilun duniya ne. Shi sunan “Futa” ɗin sun samo shi ne daga kakan su/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajen sa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka faɗin Ta’ala a Alƙurani, “Irama zatul Imaad”, da ƙabilar su ake, domin an samu cewa an taɓa kiran su da suna Iramawa.
Daga bisani, saboda yawaitar su ga yaƙe-yaƙe, sai aka riƙa kiran su da suna Fatah, ma’ana “jarumai”. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.
Yanayin zaman su a wurare kuwa shi ne silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma’ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina, Futa Jallo, Futa Falgo da sauran su.
A cewar masanin, shi wannan sunan na “Fulani”, ya samo asali ne a yammacin Afirka, sa’ilin da su ka haɗu da ƙabilar Mandinka wajen zama, waɗanda su ma kusan Fulani ne a halaye da ɗabi’u.
Malam Ahmad ya tafi a kan cewa Fulani ƙabilar farko ce da su ka soma zaman Afrika, kuma su ne su ka zo da addini yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shi kuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.
Don haka idan Fulanin sun tara ‘ya’yan su, su kan sanar musu da cewa, “Ana Hulɓe (Fulɓe) Allah”, ma’ana “mu masu tsoron Allah ne, kada ku yi abin da Mandinkawa abokan zaman mu su ke aikatawa.”

Daga nan sai Mandinkawa masu zuwa ganin su su ka riƙa kiran su da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya riƙa sauyawa zuwa Fullata da Fulɓe.
MAHANGA TA ƊAYA
Malam Ahmad ya sanar da mu cewa Bafillatani ya samu ne daga jikin Annabi Nuhu (a.s.). Asalin zuriyar sa kuma a yankin Ɗurisinin ta ke da zama. A nan ne har Annabi Musa (a.s.) ya riske su a zamanin sa lokacin da aka saukar masa da Attaura. A lokacin su na masu bautar shanu, don haka sai ya kira iya ƙabilar sa da Bani Isra’ila zuwa bautar Allah makaɗaici.Shi ya sa sai Bani Isra’ila su ka yi kwaɗayin a sanya masu abin bauta kamar yadda Futawa su ke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar da su tare da sanya masu ɗan maraƙi a matsayin abin bautar Annabi Musa (a.s.). Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugaban su mai suna Tori ya karɓi addini, shi ne har aka yi bikin karɓar sa ranar Asabar a jikin dutsen Ɗurisinina. Fulani na kiran bikin ‘Larki’. Har kuma su kan ce “Radu Tori Sinin”, watau “ga inda Tori ya musulunta” tare da nuni da Ɗurisinin.
A zamanin, sai ƙabilar Futah ta kasu, wasu su ka karɓi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma su ka bijere, inda su ka yi hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikin su ƙabilun Chusi da ake kira Tutsi yanzu su ka fita, da sauran ƙabilun da su ka mamaye yankunan.
MAHANGA TA BIYU
A wannan mahanga, an ce asalin Fulani tare da Yahudawa su ke da zama, don haka kusancin su ke sanyawa ake kiran su da sunan Yahudawa. Kuma su mayaƙa ne marasa tsoro, waɗanda ba sa rabo da makami, sannan su na matuƙar ɗaukaka ranar Asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da Yahudawa. Sannu a hankali su ka famtsamazuwa yankin Afrika ta Yamma.
MAHANGA TA UKU
Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba (a.s.). Aka ce a lokacin da ya zama dattijo ya na wa’azi a gefen tekun Indiya, sai aka ba shi wata mace aure wadda ba ta son sa. Don hakan idan dare ya yi sai ta guje masa zuwa bayan ɗaki, a can kuma sai sheɗan ya riƙa zuwar mata ya na tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda ba ya magana da kowa.
Aka yi magana a kan yadda ta samu wannan yaro, ganin rashin tarayyar ta da maigidan ta, amma Annabi Ayyuba ya ce a ƙyale ta a matsayin matar sa.
Daga bisani hakan ya ci gaba da faruwa har ta sake haihuwar yarinya mace.
Don haka waɗannan mace da namijin da su ka girma su ne su ka fara amfani da yaren su sabo na Fulatanci.
NASABAR TORONKAWA
A littafin ‘Tarihin Fulani’ na Wazirin Sokoto, wanda kamfanin ɗab’i na NNPC ya wallafa a cikin 1956, ana ce masu Toronkawa ne saboda sun zauna a ƙasar Toro. Ita Toro ƙasa ce a yankin yamma-maso-kudu na Afrika ta Yamma.
Sun taso ne daga wajajen Ɗurisina cikin ƙasar Sham (Syria a yau), su kabiyo daga gefen arewa ta Afirka ta Yamma har su ka sadu da Toro, su ka zauna a wurin.

A nan su ka yi yawa ƙwarai, har lokacin da aka aikiUƙubatu yaƙi Afrika, ya sadu da su. Sai su ka shigaaddinin Islama ba tare da an yi faɗa ba. Uƙubatu ya auri ɗiyar sarkin su, sunan ta Bajjo Mangu. To su Toronkawa jinsi ne da su ka fito daga zuriyar Ramo, ɗan Isa, ɗan Ishaku, ɗan Annabi Ibrahim (a.s.).
Bajjo Mangu ta haifi ‘ya’ya huɗu da Uƙubatu, su ne: Deita, Woya, Roruba da Nasi.
Waɗannan su ne asalin dukkan Fulani da su kafara magana da Fulatanci. Toronkawan dauri, harshen su Wakuru ne.
Daga baya zuriyar Uƙubatu ta yawaita kamar haka:
1. Daga ɗiyan Deita ƙabilar Songhay ta fita.
2. Daga ɗiyan Nasi dangin Ba’awina da Wolorbe su ka fita.
3. Daga ɗiyan Woya dangin Forbe su ka fita.
4. Daga ɗiyan Roroba dangin Woloɓe su ka fita.
Bayan sun yi yawa, sun zauna a wuri mai suna Falgu. Daga nan sai su ka rabu da sauran Toronkawa na Futa Turo.
Lokacin da su ka yi ƙarfi, sai su ka ɗauki yaƙi babba. Su ka tasar wa Futa su ka ci amanar SarkinFuta su ka kashe shi ya na sallar Idi. Su ka kama ƙasar Futa su ka zauna su na ɓarnace-ɓarnace.
Sannan sai wani malami daga cikin Toronkawa ya tashi ya yi jihadi da su, ya rinjaye su, ya gyara ƙasa, ya zuba adalci, ya kyautata zaman Toronkawa.
To, bayan rasuwar sa sai Fulani jinin Uƙubatu su ka sake kawo yaƙi ga Toronkawa, su ka kore su daga Futa, su ka sake kama ƙasa tare da shigaɓarnace-ɓarnace.
Bayan haka kuma sai Fulani Toronkawa su ka yi shirin yaƙi da Fulani jikokin Uƙubatu. Su ka taho da yaƙi, su ka yi faɗa da su mai tsanani har su ka rinjaye su mugunyar rinjaya.

Saboda haka sai Fulani ɗiyan Uƙubatu su ka kasu uku: kashi ɗaya su ka saduda su ka bi Toronkawa; kashi na biyu su ka koma Falgu inda su ka soma zama da fari; kashi na uku su ka yo gabas su ka tsammaci za su riski ‘yan’uwan su Larabawa saboda uban su Balarabe ne. Wasu cikin su sun iya komawa ƙasar Larabawa, wasun su kuma sun kasa, ba su ƙarasa ba. Sunan babban su Dunurundi.
To waɗannan da ba su ƙarasa ɗin ba, daga cikin su ne zuriyar Beni Yalalɓe da Sissilɓe da Walanɓe da Gumborawa da Gwalankwa’en da Fulanin Adamawa su ka fito.
Waɗannan su ne dangogin da su ke daga cikin zuriyar da su ka taho daga Naskanga tare da Dunurundi.
Su waɗancan sun fi Toronkawa yawa, domin an samu kashin farko da su ka koma Falgo daga baya sun ƙara kawo wa Toro yaƙi su ka cinye ta tare da sake komawa ɓarna, har sai da aka samu wani daga cikin Toronkawa mai suna Sulaiman ya yi yaƙi da su ya kore su ya watsa su, ya naɗa sarki Abdulƙadir.
Bayan sa kuma sai aka naɗa Muhammadul Amin, aka zauna lafiya, Toronkawa su ka amince da Fulani ɗiyan Uƙubatu.
Bayan waɗannan al’amura da mu ka faɗa, lokacin nan Musa Jakollo kakan Shehu Usmanu ya taso da jama’ar sa don gudun fitina, ya fuskanci gabas har ya ƙaraso Ƙwanni a shekara ta 500 Bayan Hijira. Shi kuma ɗiya nai sai su ka warwatsu.
Kaso ɗaya su ne ɗiyan Ali, na biyu ɗiyan Ɓininga,sai ɗiyan Kogga, sai ɗiyan Ɓaleni da ɗiyan Raneni. Ɗiyan Ɓininga ne su ka tashi daga Ƙwanni sa’ilin da Sarkin Ƙwanni Damka ya zambace su yakarkashe su, ya kama ɗiyan su ya yasashe dukiyar su. Ɗiyan Ali sun sauka a wani wuri da ake kira Kuluba.
DANGANTAKAR SHEHU ZUWA MUSA JOKOLLO
Ma’anar “Fodiyo” ita ce “malami”, kuma wandamalami ya haifa. Shi ne Fodiyo ɗan Usmanu ɗan Salihu, ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ɗan Jaɓɓo ɗan Mamman Samba ɗan Masirana ɗanAyuba ɗan Baba ɗan Abubakar ɗan Musa Jakollo wanda ya ke da ɗiyan Imamu Demba.

Idan har ingancin wannan tarihin ya tabbata, mu na iya kallon sa a matsayin sabuwar fuska saɓanin wanda ake yaɗawa mai cewa Fodiyo aljana ce kuma ita ce ta haifi Shehu Usmanu.
Koda yake har yanzu na lura da cewa Fulani da yawa su na ji a ran su cewar asalin su gamin gambiza ne tsakanin Larabawa da aljannu.
Wataƙila dai abin da ya ke a kan mu bai wuce binciko tarihin salsala ko a ce rarrabuwar ƙabilun Fulanin ba, kamar misalin Sulluɓawa, Danejawa,Natirawa, Agalawa, Holma, Bongwa, Naturɓe, Ba’awa (an faɗi salsalar su a sama), Rudunnawa, Magawa da dai sauran su.
MAHANGA TA HUƊU: TSAKANIN FULANI DA RUMAWA
Shi ma Malam Khalid Musa ya faɗa mana cewa akwai mahanga ta huɗu mai cewa asalin Fulani Rumawa ne. A wannan mahangar, an ce ƙabilun Rome ne makiyaya da su ke zaune a karkara. Lokacin basasar Rome bayan kisan Julius Caesar sai ya zamana babu tsaro a ƙasar.
A dalilin haka, da yawan su su ka riƙa kwararowa cikin Afrika don kuɓutar da dukiyoyin su. Cuɗanyar su da wasu ƙabilun Afrika ne ya samar da yaren Fulatanci.
Lokacin wannan ƙaura tare su ka shigo Afrika da mazauna yankin Sisley makiyaya. Waɗannan ƙabilun mazauna Sisley su Fulani ke kira Sissilbo, wato mutanen Sisley; da Hausa mu na kiran su Sulluɓawa.

Har a yau ɗin nan da yawa daga cikin Sulluɓawa ba sa amsa sunan Fulani. Su na inkarin ka ce masu su Fulani ne a ko da yaushe. Malam Khalid ya ce ya jarraba wannan da kan sa.
Ya ƙara da cewa wannan mahangar ita ma daga Malam Ahmad Usman Bello Torob ta ke.
* Malam Sadiq Tukur marubuci ne, manazarci, mazaunin Kano
To aci gaba da neman tarihi saboda naga wosu tsiraru sunason gurbata tarihi
Masha Allah, Madallah da wannan kokari naku,hakika tarihin ya kayatar dani kuma ya Karan Ilimi akan abinda nasani.
Ina muku fatan Alheri, Allah ya bada Lada.