MASU sana’ar fassarar finafinan Indiya zuwa Hausa da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ba su cimma wata matsaya ba a taron da su yi a yau Alhamis a Kano kan dokar da ta haramta safarar finafinan wadda hukumar ta kafa.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin dambarwar da ta ɓarke a tsakanin ɓangarorin biyu dangane da dokar.
A yau hukumar ta yi wani taro a karon farko da masu safarar domin a samar da hanyar da za a fahimci juna a tsakanin su.
An yi zama na kusan wuni guda a ɗakin taro na hukumar da ke Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Titin Katsina.
Taron ya samu halartar dukkan ‘yan ƙungiyoyin da ke fassarawa da masu sayar da finafinan.
Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Arewa-maso-yamma, Alhaji Umar G. Fage, ya yi wa mahalartan jawabi, inda ya ce, “Mun kira ku ne domin ku faɗa mana abin da ya ke zuciyar ku, mu kuma mu faɗa maku abin da doka ta ce a game da yadda ya kamata ku gudanar da harkar kasuwancin ku.

“Saboda aikin wannan hukumar shi ne tace duk wani fim ko wani hoto mai motsi wanda jama’a za su kalla. Haka nan babu wani da zai yi wani kasuwanci na fim sai ya yi rajista da mu.
“Haka nan duk wani fim da za ka shigo da shi daga waje, dole ne sai ka yi rajista.
“Haka nan duk wata fasta ko tallar fim da za a yi dole ne sai ka kawo an tace. Don haka babu wata ƙasa da ake yin abu kara zube.
“Don haka doka ta ba ka damar ka je ka yi fim, amma ka zo ka yi rajista, kuma ka kawo a tace. Don mu aikin mu shi ne bayar da izini da kuma tabbatar da an yi aiki a bisa dokar ƙasa ba tare da an ci zarafin wani ko an shiga haƙƙin sa ba.”
Ya ƙara da cewa: “Ba hurumin mu ba ne mu kori kowa daga harkar kasuwancin sa ba. A’a, mu aikin mu shi ne mu gyara. Don haka mu burin mu, musamman a fim ɗin Hausa, mu ga ya samu karɓuwa a duniya, kuma babu wanda zai yarda da kai ba tare da ka yi rajista ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Fim ya na da ƙa’idoji da yawa, amma rashin bin dokar ya sa ba a cin moriyar sa, domin fim sana’a ne ba kwalliya ba ne. Sai ya zama mu mun ɗauki sana’ar kamar wata kwalliya. Wannan ya sa sai ka ga darakta ko jarumi ya na aiki, amma bai yi rajista da kowa ba.
“Saboda haka a yanzu za mu shiga kame. Don duk wani da ya ke aikin fim da ba shi da rajista da wata ƙungiya, to za mu kama shi. Don haka dole ne ɗan fim a yanzu ya zama ya na cikin wata ƙungiya yadda za mu yi magana da shi ta hanyar ƙungiyar sa.
“Don haka ya zame mana wajibi mu haɗa kai da ku domin mu kawo gyara a cikin harkar fim don ya zama zallar masu kishin harkar fim ɗin ne zai yi sana’ar.”
Ya ƙara da cewa, “A yanzu akwai shiri da mu ke da shi na samar da hanyoyin nuna finafinai a dukkan manyan sinimomi da mu ke da su a ƙasar nan wanda hakan zai bayar da dama masu harkar su rinƙa samun kuɗin shiga cikin lokaci.”
Da ya juya ga masu gudanar da harkar kasuwancin fassarar finafinan Indiya kuwa, Umar G. Fage ya ce: “Ba mu na son mu hana kowa harkar kasuwancin sa ba, amma dole ne idan mutum zai yi kasuwancin ya bi doka. Don haka ba mu da haƙƙin da za mu yi wa mai fassarar finafinan Indiya rajistar ya fassara ko ya sayar, saboda haƙƙin wani ne.
“Abin da dokar mu ta ce, duk wanda zai fassara finafinai na waje ya sayar – ba na Indiya ba, ko ma na wacce ƙasa ne – to ya kawo mana takardar izini daga furodusan fim ɗin, sai mu ba shi izini ya fassara kuma ya sayar. Amma in dai ba haka aka yi ba, to babu wani fim da aka fassara daga wani yare ko daga wata ƙasa da za mu bari a ci gaba da fassarawa ko sayar da shi, Saboda haƙƙin wani ne, ba naka ba, kuma kai ma ba za ka so a shiga haƙƙin ka ba.”
A daidai wannan lokacin, sai masu gudanar da sana’ar fassarar finafinan Indiya ɗin su ka so su tayar da hayaniya da nuna ba su yarda ba, su na faɗin za a hana su neman abincin su ne. Amma dai an yi ƙoƙarin kwantar masu da hankali tare da ba su dama su yi magana a game da abin da su ka fahimta.
A lokacin da ya ke bayanin sa, ɗaya daga cikin masu gudanar da harkar fassarar finafinan Indiya ɗin, Malam Abdulrazaq Sultan, ya yi kira ga hukumar da ta ba su lokaci domin su samu wata mafitar zuwa wani lokaci, ba wai daga kafa dokar a fara aiki da ita a nan take ba.
Sai dai Umar G. Fage ya ba shi amsa da cewa: “Ita wannan doka ba sabuwa ba ce, an samar da ita tun a shekarar 2002. Kuma batun a bayar da lokaci don a samar da mafita, wannan ba adalci ba ne ga waɗanda ake ci da gumin su.”
Ya ce don haka za su ci gaba da aikin su na tabbatar da an bi duk wata doka da za ta kawo cigaban masana’antar finafinai da kare dukiyoyin jama’a ta hanyar tabbatar da an bi doka.

Haka aka tashi daga taron ba tare da an kai ga fahimtar juna a tsakanin hukumar da masu fassarar finafinan Indiya ba.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa hakan ya faru ne musamman da yake su masu safarar fassararrun finafinan sun kafe a kan cewa a bar su su yi abin su yadda su ke yi, domin a matsayin su na ‘yan ƙasa bai kamata a kafa dokar da za ta hana su neman abinci ba, shi kuwa shugaban hukumar ya ce har yanzu ƙofar sa a buɗe ta ke da su masu gudanar da harkar su zo su zauna da shi, amma dai ba zai yiwu a ci gaba da irin wannan kasuwancin ta haramtacciyar hanya ba.