DAGA ina zan ɗauki mataimaki na? Wannan ita ce damuwar Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, a yanzu.
Ba kamar Atiku na PDP ba, wanda kai-tsaye ya san daga kudancin Nijeriya zai ɗauko nasa, kuma Kirista, walau daga cikin Inyamurai ko daga ‘yan Neja Delta.
Shi Tinubu ya na cikin tsaka-mai-wuya. A Arewa wa zai ɗauka? Musulmi ko Kirista? Mutanen sa Kirista irin su Babachir Lawal sun ce idan ya ɗauki Musulmi tabbas ba zai ci zaɓe ba saboda Kiristoci za su gwammace zaɓar Atiku wanda ya ke da Kirista mataimaki. Su na ganin lokaci ya canza, ba kamar zamanin Abiola da Kingibe ba.
A ɗaya ɓangaren kuwa, idan Tinubu ya ɗauki Kirista, to Musulmi ‘yan Arewa, waɗanda su ne waɗanda su ka fi yawa a Arewa, za su ga cewa an mayar da su tsiraru, ‘yan kallo, abin da ba a taɓa yi ba a mulkin Nijeriya. Haka zai sa su runtuma wajen Atiku.
Da na saka wannan rubutun a Facebook, wani mai bibiya ta ya ce dole Tinubu ya zaɓi ɗayan biyu: idan adalci ya ke so, to ya ɗauki Kirista; idan kuwa cin zaɓe ya ke so, to, ya ɗauki Musulmi. A yanzu wanne ne Tinubu ke buƙata – adalci ko cin zaɓe? Kada kuma ya yi kamun gafiyar Ɓaidu!
Da alama dai duk inda Tinubu ya yi, Atiku zai ce gaba ta kai shi. Ga shi maguɗi ya na ƙara wuya. Ga shi ba zaɓen fid da gwani ba ne na mutane ƙalilan balle a ce Dala za ta yi aiki. Ga INEC ta matsa ta ce cikin sati guda kowane ya fito da mataimakin sa.
Gaba kura, baya siyaki. Ni Tinubu! Ina zan sa kai na?
In da kai ne Tinubu, ya za ka yi?
* Dakta Aliyu U. Tilde shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi