• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu ya himmatu wajen kammala hanyar Abuja zuwa Kano cikin watanni 14, cewar Ministan Yaɗa Labarai

by WAKILIN MU
January 17, 2025
in Nijeriya
0
Tinubu ya himmatu wajen kammala hanyar Abuja zuwa Kano cikin watanni 14, cewar Ministan Yaɗa Labarai

Alhaji Mohammed Idris tare da Ministan Ayyuka Dave Umahi da sauran jami'ai a garin Tafa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da jajircewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi na kammala aikin titin Abuja zuwa Kano cikin wata 14.

Da yake magana yayin wata ziyara ta duba aikin a garin Tafa, Jihar Neja, a ranar Alhamis, Idris ya bayyana cewa jajircewar Shugaban Ƙasa wajen hanzarta aikin ya sa aka bai wa wani kamfani kwangilar wasu sassan aikin da aka fara bai wa kamfanin Julius Berger PLC.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya himmatu matuƙa wajen ganin an kammala aikin titin Abuja zuwa Kano da ta ratsa Kaduna da Zariya, kuma ya dage cewa dole a kammala wannan aiki. Ba za mu bari wani ɗan kwangila ya tilasta wa gwamnati ta bi sharuɗɗan shi kan wannan aiki ko wani aiki ba. Ba mu da isasshen lokaci na jira na tsawon wasu shekaru uku kafin a kammala wannan titi.

“Ministan Ayyuka ya bayyana cewa sun sanya wa kan su wa’adin watanni 14 don kammala wannan titi.

“Ganin irin ƙwazo da jajircewar da suke nunawa, mun yi imani za a cika wannan wa’adi.

“Ga waɗanda suke siyasantar da wannan aikin titi, don Allah ku ajiye siyasa a gefe. Wannan titi dole ne a kammala shi. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya himmatu matuƙa wajen ganin wannan babbar hanyar da ke haɗa Abuja da Kano da sauran jihohi an kammala ta. Babu abin da zai hana hakan.”

Idris ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya ƙi amincewa da wa’adin shekaru uku da kamfanin Julius Berger ya bayar, inda ya ba da umarnin kammala aikin a cikin gaggawa.

An raba aikin zuwa kashi uku domin sauƙaƙa gudanarwa da tabbatar da cewa an kammala shi cikin lokaci.

Idris, wanda ya samu rakiyar Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, da wasu manyan jami’ai, ya yaba wa jajircewar Umahi, inda ya jinjina masa kan ƙoƙarin sa wajen rage kuɗin kwangilar da kuma wa’adin kammalawa.

Ya bayyana cewa da farko Julius Berger sun nemi ƙarin kuɗin kwangilar daga Naira biliyan 797 zuwa Naira tiriliyan 1.5 tare da ƙarin wa’adi zuwa shekaru uku.

Sanata Umahi ya bayyana cewa ma’aikatar ta samu amincewa daga Hukumar Kula da Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (BPP) kan sabon kuɗin kwangilar Naira biliyan 252.89, wanda za a gabatar wa Majalisar Zartaswa ta Tarayya domin amincewa.

Sabon tsarin ya haɗa da ƙarin wasu kilomita a ɓangaren Kano, sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da kuma tanadi don kula da titin a nan gaba.

Idris ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina siyasantar da aikin, su mayar da hankali kan ganin an kammala shi, yana mai jaddada muhimmancin sa wajen haɗa Babban Birnin Tarayya da Kano da sauran jihohin arewa.

Loading

Tags: Dave Umahihanyar Abuja-KanoMohammed Idris
Previous Post

Ba mu buƙatar amincewar Sanusi kan tsare-tsaren mu na tattalin arziki, inji Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Mawaƙiya a Kannywood, Ummi BY, ta yi rashin mahaifi

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Mawaƙiya a Kannywood, Ummi BY, ta yi rashin mahaifi

Mawaƙiya a Kannywood, Ummi BY, ta yi rashin mahaifi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!