• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tinubu ya sadaukar da kai ga manufofin Nijeriya da Afrika a duniya – Minista

by DAGA WAKILIN MU
October 21, 2023
in Nijeriya
0
Alhaji Mohammed Idris a wajen walimar da aka yi a Ofishin Jakadancin Angola a daren Alhamis

Alhaji Mohammed Idris a wajen walimar da aka yi a Ofishin Jakadancin Angola a daren Alhamis

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa sadaukar da kai da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bai tsaya ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da dukkan nahiyar Afrika.

Ya ce: “Tun daga lokacin da ya kama aiki, an gan shi sosai a faɗin duniya ya na yayata manufofi da burukan Nijeriya da ma nahiyar Afrika.”

Ministan ya faɗi haka ne a wurin wata walimar cin abincin dare wadda Ofishin Jakadancin ƙasar Angola ya shirya a Abuja a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya na da shauƙin ganin ya inganta mu’amalar da ke tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika, ciki har da Angola.

Idris ya ce yanzu ana kallon Shugaban Ƙasa a matsayin uba a faɗin Afrika, wanda ke jagorantar ƙasar da ta fi kowace yawan jama’a da ƙarfin arziki a nahiyar.

A cewar sa, wannan ne ya sa aka naɗa Tinubu shugaban ƙungiyar ƙasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS, jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Ya ce: “A jawabin sa a wajen babban taron farko da ya halarta na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a watan jiya, ya yi magana mai gamsarwa ƙwarai kan dalilan da su ka sa Afrika ta ke buƙatar sauran ƙasashen duniya su yi mata adalci, da abin da ya sa cigaban duniya ya na tattare ne da cigaban Afrika.

Ya ce, “Wato dai manufa, idan har duniya ta ɗauki batun samun cigaba da gaske, to tilas ne kuma ta ɗauki batun cigaban Afrika da gaske.”

Ministan ya ƙara da cewa mafarkin Shugaba Tinubu da burin sa su ne ƙasashen Afrika su haɓaka dangantaka mai zurfi da ƙarfi a tsakanin su wanda “zai ba da dama ga nahiyar ta samu matsayi da ya fi na da girma da ƙarfi a fagen duniya da kuma samun dama mafi girma wajen samun ‘yanci mai ɗorewa da arziki. Duk abin da ya gaza kan wannan, to ba za mu yarda da shi ba.”

Alhaji Mohammed Idris (na 5 daga hagu) tare da sauran manyan baƙi a wajen walimar da aka yi a Ofishin Jakadancin Angola a daren Alhamis

Ya yi la’akari da cewa idan har ba a haɗa kafaɗa aka yi mu’amala da haɗin kai tare ba, Afrika ba za ta cimma nasarar warware matsalolin ta ba.

Idris ya ce: “Ƙoƙarin magance ɗimbin ƙalubalen da ke fuskantar nahiyar a wannan zamani  – irin su rashin tsaro, fatara, rashin aiki, labarai marasa daɗi, ƙarancin hada-hadar kasuwanci a tsakanin nahiyoyi, da sauran su – duk ya na buƙatar yin aiki kafaɗa da kafaɗa a matakin yanki da na nahiya baki ɗaya.

“Duk da yake akwai bambance-bambancen harsuna da al’adu da tsarin zamantakewar al’umma da na siyasa, tilas ne mu samo hanyoyin da za mu amince da su domin gabatar da matsaya ɗaya kan al’amurran da su ka shafi mu su waye a matsayin nahiya, da abin da mu ke so mu cimmawa a dukkan ɓangarori na rayuwa.

“Tilas mu haɗu mu tattaro tunani kan batun cigaban ƙasa, kafa masana’antu, cinikayya, samar da aikin yi, da kuma matsayin nahiyar mu a ƙarni na 21. Yanzu haka an yi nisa wajen aiki kan hakan, don a fitar da matsaya ɗaya haɗaɗɗiya wadda za a yi aiki da ita a matakai daban-daban.”

Loading

Previous Post

Tinubu ya naɗa sababbin shugabannin hukumomin yaɗa labarai

Next Post

Gwamnan Neja ya taya Ndace murna kan naɗin sa a matsayin shugaban Muryar Nijeriya

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Next Post
Jibrin Baba Ndace

Gwamnan Neja ya taya Ndace murna kan naɗin sa a matsayin shugaban Muryar Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!