SHUGABAN Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar Neja domin jajanta wa gwamnati da al’ummar da ambaliya ta shafa a garin Mokwa da kewaye.
Ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150, ta raba dubban mutane da muhallan su, kuma ta lalata ɗimbin gidaje, hanyoyin mota da gadoji a sassan da abin ya shafa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Ministan Harkokin Jinƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, su ne suka jagoranci tawagar, inda suka kai ziyarar ta’aziyya ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Malam Yakubu Garba, a madadin Shugaban Ƙasa.
“Mu zo nan ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin saduwa da al’ummar Jihar Neja, musamman Gwamna da jami’an gwamnatin jihar, domin jajanta maku; domin nuna tausayawa da jimami kan abin da ya faru a Ƙaramar Hukumar Mokwa,” inji Idris.
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa ya kaɗu sosai bisa wannan lamari, kuma jiya ya bayar da umarnin cewa a tura duk wasu kayan aikin gwamnati da ake da su zuwa Mokwa.
“Shi ya sa kuka gan ni tare da ɗan’uwa na, Mai Girma Ministan Harkokin Jinƙai.”
Ministan ya ce Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta riga ta gudanar da cikakken bincike kan halin da ake ciki, kuma tana aiki tare da gwamnatin jihar wajen kai agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa.
Ya ce: “Mun san cewa NEMA suna aiki tare da gwamnatin jihar nan domin tabbatar da gudanar da ayyuka cikin sauƙi.
“Haka kuma, sun tabbatar da cewa an tattara gawarwakin waɗanda suka rasa rayukan su cikin mutunci; an kula da waɗanda kuma suka samu raunuka iri daban-daban, sannan duk wani abu da ake buƙata daga ɓangaren gwamnati an tanada domin tallafa wa ‘yan’uwan mu maza da mata a Mokwa.”
Ya ce Shugaban Ƙasa yana matuƙar damuwa da girman wannan lamari, musamman ganin cewa kusan shekara guda da ta gabata irin wannan ambaliya ta auka wa wasu yankuna na Jihar Neja.
Ya ce Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar matakai domin kada a sake fuskantar irin haka nan gaba ba tare da an yi wani tanadi ba.
Har wa yau, ya ce Shugaban Ƙasa ya umurci Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin ƙara faɗakar da al’umma, musamman mazauna yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya.
“Wannan kuma kira ne ga jama’ar mu da su ɗauki wannan a matsayin gargaɗi kan yiwuwar faruwar irin wannan al’amari a nan gaba, musamman ga waɗanda ke zaune a yankunan da irin wannan iftila’i yake yawan faruwa,” inji Idris.
Ministan ya yaba wa gwamnatin Jihar Neja bisa yadda ta gaggauta ɗaukar matakai domin rage raɗaɗin ambaliyar.

A nasa jawabin, Ministan Harkokin Jinƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Yilwatda, ya bayyana cewa ana duba yiwuwar ƙara taimaka wa waɗanda aka raba da muhallan su.
Ya ce an umurci Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, ‘Yan Cirani da Mutanen da Rikici ya Raba da Muhallan su ta Ƙasa da ta karɓi ragamar daga NEMA wajen ci gaba da tallafa wa waɗanda suka rasa matsuguni.
Da yake mayar da martani, Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Malam Yakubu Garba, ya bayyana godiyar sa ga Shugaban Ƙasa bisa yadda Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kawo ɗauki.
Ya ce hoɓɓasan gaggawa da aka yi daga Gwamnatin Tarayya alamar ƙarfin kishin gwamnatin Tinubu ne wajen kula da rayuwar ‘yan ƙasa a lokacin da suke cikin buƙata.
Garba ya bayyana cewa yanzu haka an riga an binne gawarwakin mutane 151 da ambaliyar ta kashe.
Ya ce gidaje 264 da iyalai 503 ne abin ya shafa a cikin ƙauyuka uku, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsugunin su.
Haka kuma, tituna da dama da gadoji uku da ke Mokwa da Raba sun lalace, lamarin da ya janyo tsaiko a zirga-zirga a yankin.