SHUGABA Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga babbar furodusa kuma jaruma Funke Akindele saboda shirin ta mai suna ‘A Tribe Called Judah’ da ya zama fim ɗin Nijeriya na farko da ya yi cinikin zunzurutun kuɗi har naira biliyan ɗaya.
Funke ɗin ce ta bayyana labarin wannan nasarar da ta samu a shafin ta na Instagram inda ta wallafa fosta mai nuni da hakan tare da rubutawa cikin zumuɗi cewa, “Thank You LORD!!!, Thank NIGERIA!! Thank you GHANA!!” Wato: “Na gode ALLAH!!!, Na gode NIJERIYA!! Na gode maki ƙasar GHANA!!.”
Shi dai wannan fim an sake shi ne a gidajen sinima na Nijeriya a ranar 15 ga Disamba, 2023 inda ya samu karɓuwa wajen ‘yan kallo da ke ta yin tururuwa zuwa wajen kallon sa ta yadda babu fim ɗin da ya zarce shi wajen samun ciniki.
Tun a makon farko na sakin fim ɗin ya yi cinikin sama da naira miliyan 133.
Fim ɗin, wanda aka shirya da harshen Turanci, ya zamo fim ɗin Nollywood da ya zarce kowanne fim ciniki a shekarar 2023 bayan ya samu sama da naira miliyan 613 a cikin kwana 14 na farko da fitowar sa.
Bugu da ƙari, fim ɗin ya kafa tarihi a ranar 2 ga Janairu a matsayin fim ɗin Nollywood na farko da ya taɓa yin cinikin naira miliyan 854 a gidajen sinima cikin kwana 18 da fitowar sa.
Wannan nasarar ta zarce wadda furodusar ta samu a finafinan ta na baya, wato ‘Battle on Buka Street’ (inda aka samu naira miliyan 668.4), da ‘Omo Ghetto’ (naira miliyan 636.1) waɗanda a yanzu su ne finafinai na biyu da na uku a jerin finafinan Nijeriya mafi kawo riba a tarihin shirya fim a ƙasar. Na ɗayan shi ne ‘A Tribe Called Judah’.

Daraktan shirin ‘A Tribe Called Judah’ shi ne Adeoluwa Owu, wanda ake kira da Captain Degzy, kuma kamfanin FilmOne Entertainment ne ya yi kwangilar rarraba shi a gidajen sinima.
Fim ɗin na cike da manyan jarumai irin su Ikpe Etim, Funke Akindele, Timini Egbuson, Ebelle Okaro, Uzor Arukwe, Genoveva Umeh, da Nosa Rex.
Sauran su ne Boma Akpore, Ebele Okaro-Onyiuke, Etinosa Idemudia, Fathia Balogun, Jide Achufusi, Olayode Juliana, Olumide Oworu, Paschaline Alex, Tobi Makinde, Uzor Arukwe da Yvonne Jegede.
A cewar Funke Akindele, fim ɗin na bada labarin wata mace ne da ake kira Jedidah Judah, wadda ta haifi ‘ya’ya maza su biyar kuma kowanne da uban sa, sannan kowane uban ƙabilar sa daban.
Ta ce: “Ina matuƙar son labarin, kuma ya taɓo wani abu game da mahaifiya ta marigayiya, kuma ya na nuna irin faɗi-tashin da iyaye da mata masu ‘ya’ya amma babu mace ko miji su ke fuskanta a cikin al’umma.”
A yanzu haka ana nuna fim ɗin a gidajen sinima a Ghana da Ingila.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a saƙon taya Akindele murna da ya bayar, Shugaba Tinubu ya yaba mata kan gudunmawar da ta ke bayarwa ga bunƙasar masana’antar fim ta Nijeriya.
A saƙon nasa, wanda mai ba shi shawara kan aikin jarida, Cif Ajuri Ngelale, ya rattaba wa hannu, shugaban ƙasar ya kambama babbar rawar da masana’antar fasaha da ƙirƙira ke takawa a matsayin wata hanyar bayyanar da basira da kuma samar da ƙarfin tunani da abin fitarwa zuwa ƙasar waje.
Ya ce: “Masana’antar fasaha ta na daga cikin manyan guraben da ke samar da aikin yi, su samar da ayyuka ga matasan mu masu ƙoƙari tare da fasaha. Ma’aikata ce mai matuƙar muhimmanci ga gwamnati na.
“Ina yaba wa ‘yan Nijeriya saboda cikakken goyon bayan da su ke bayarwa da kuma sayen ayyukan basira da ake ƙoƙarin shiryawa a Nijeriya.
“Za mu samar da yanayin da ya dace don masana’antar ta ci gaba da bunƙasa.”