A YAU Lahadi ne tsohuwar jaruma a Kannywood, Halima Yusuf Atete da mijin ta Mohammed Mohammed Kala su ka cika shekara ɗaya cif da aure.
Halima ta wallafa hotunan musamman guda tara a Instagram inda aka gan ta tare da Mohammed.
Ta tura hotunan tare da saƙo da Turanci, ta ce: “Alhamdu lillah, today marks a special day in my life, as I’m celebrate both my birthday and wedding anniversary together. It shall forever be getting better. May Almighty Allah increases and uphold our marriage.”
Mujallar Fim ta fassara shi da cewa: “Alhamdu lillah, yau rana ce ta musamma a cikin rayuwa ta. Ina murnar zagayowar ranar haihuwa ta da kuma zagayowar ranar aure na.
“Auren mu zai kasance cikin zaman lafiya har abada. Allah ya ƙara riƙe auren mu.”

In ba ku manta ba, an ɗaura auren Halima Atete da Mohammed Mohammed Kala ne a masallacin Juma’a da ke Abuja Sheraton Bus Stop, Maiduguri, Jihar Borno.
Duk da cewa ba a Kano aka yi shagalin bikin ba, amma ɗimbin ‘yan Kannywood sun halarta, musamman daga Kano.
Allah ya ƙara masu zaman lafiya, ya kawo zuri’a ɗayyiba.