WANI fim mai suna ‘Ngoda’ shi ne ya lashe manyan kyaututtukan da aka ci a gasar Biki Da Baje-kolin Finafinan Harsunan Gadon Afrika na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF) wanda aka yi a daren jiya.
Fim ɗin ya yi nasara a matakai har bakwai, ciki har da Gwarzon Sauti, Gwarzon Hoto da Gwarzon Kwalliya.
Sai dai kuma darakta a Kannywood, Sir Hafizu Bello, shi ne ya lashe matsayi biyu a gasar, ciki har da Daraktan Daraktoci.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a daren jiya Asabar aka kawo ƙarshen bikin baje-kolin na bana tare bayyana zakarun gasar bikin a babban ɗakin taro na Bristol Palace da ke kan Titin Guda Abdullahi a unguwar Farm Centre a Kano.
Bikin, wanda ya samu halartar manyan baƙi daga ƙasashe daban-daban na Afirka, an fara shi da misalin ƙarfe 7:30 na dare.

A lokacin da ya ke jawabin maraba da baƙi, shugaban kamfanin Moving Image, wanda ya ɗauki nauyin shirya bikin, Alhaji Abdulkarim Mohammed, ya nuna farin cikin sa da samun nasarar gudanar da taron wanda shi ne karo na 6 da aka yi a jere tun daga 2018, ya ce wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.
Ya ce: “Shi wannan taron wani ƙudiri ne da na ke da shi tun farkon fara aikin jarida ta a 1979, na samar da wani tsari na inganta al’adu da kuma yarukan Afrika. Kuma alhamdu lillahi mafarki na ya fara zama gaskiya, domin a yanzu a wannan taro za mu iya cewa Afrika ce ta haɗu, ba ma Nijeriya ba, saboda a wannan ɗakin taron a yanzu akwai mutanen Zimbabwe, Malawi, Ghana, Nijar, Afrika ta Kudu, Uganda, Botswana, da sauran su.
“Don haka wannan abin farin ciki ne a gare mu, musamman da ya zamo a Kano ake yin wannan gasa don ta zama wata cibiya ta Afrika baki ɗaya.

“Don haka taken taron ba ya canzawa a duk shekara mu ke yi masa taken ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ saboda Kano ita ce cibiyar kasuwanci da al’adu ta Afirka.
“Duk da yake dai duk shekara mu mu ke ɗaukar nauyin shirya wannan taron, amma mu kan samu tallafi da gudunmawa daga wasu hukumomi na gwamnati da ƙungiyoyi da kamfanoni masu zaman kan su, wanda a wannan lokacin za mu yaba da gudunmawar Bankin Manoma da Bankin Masana’antu da Gidauniyar Ahmadu Bello da sashin koyar da aikin jarida na Jami’ar Bayero da sauran duk waɗanda su ka bayar da gudunmawar su wajen gudanar da wannan taron.
“Mu na fatan Allah ya ƙara ba mu damar ci gaba da gudanar da wannan taron yadda ko bayan babu mu za a ci gaba da gudanar da shi.”

Shi ma da ya ke nasa jawabin a wajen, shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa (ACF), reshen Jihar Kano, Dakta Gwani Umar Faruk, ya nuna farin cikin sa da samar da wannan taron duk shekara wanda ya zama wata cibiya ta samar da haɗin kai da kuma tattaunawa da mutanen da su ke ƙasashen Afrika ba ma iya ƙasar Nijeriya ba kaɗai.
Ya ce, “Wannan aiki ne babba wanda kuma shi ne manufar samar da ƙungiyar mu ta Dattawan Arewa. Don haka mu na goyon bayan duk wani yunƙuri da zai haɗa kan ƙasar mu Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.”
Manyan baƙi da dama sun yi jawabai kuma aka nishaɗantar da mahalarta taron da rawar ƙoroso da kuma wasan daɓe. Daga ƙarshe kuma aka bayyana sunayen finafinan da su ka yi nasara a gasar.
An shafe tsawon kwana biyar ana gudanar da tarurruka da su ka haɗa da taron sanin makamar aiki a kan sana’ar fim da kasuwancin sa, baje-kolin kayayyakin al’adu na Afrika da cin abincin gargajiya na Afrika da yawon shaƙatawa da baƙi don a nuna masu muhimman kayayyaki da kuma na tarihin ƙasar Hausa.
Wani abin burgewa kuma shi ne an shirya taron hawan bori da kiɗan garaya inda mutane su ka ga yadda ake hawan bori, wanda ya na ɗaya daga cikin al’adun ƙasar Hausa.
Finafinan da su ka yi nasara a gasar su ne:
- Gwarzon Labari – ‘Ngoda’
- Gwarzon Tsara Wajen Aiki – ‘Herdsmen‘
- Gwarzon Kwalliya – ‘Ngoda’
- Gwarzon Tsara Hotuna – ‘Kikum Spirit’
- Gwarzon Sauti – ‘Ngoda’
- Gwarzon Tace Labari – ‘Enonil’
- Gwarzon Jarumi – Adam Juma da fim ɗin – ‘Eonii’
- Gwarzuwar Jaruma – Radeeya Jibril da fim ɗin ‘Eonii’
- Gwarzon Jarumi Mai Tasowa – Taurai Kawara da fim ɗin ‘Ngoda’
- Gwarzuwar Jaruma Mai Tasowa -Caroline Mashindaize, da fim ɗin ‘Ngoda’
- Gwarzon Darakta – Hafizu Bello da fim ɗin ‘Aisha’
- Gwarzon fim ɗin tarihi – ‘Lobola’
- Gwarzon Gajeren Fim – Deor ward’
- Gwarzon Harshen Gida Na Afrika – ‘Aisha’
- Gwarzon Fasalin Fim Mafi Kyau – ‘Ngoda’
- Gwarzon Hoto – Ngoda’
Nasarar da fim ɗin ‘Ngoda’ daga Zimbabwe ya samu a bikin shi ne ya yi fice a cikin dukkan matakai na gasar domin ya yi nasara a matakai har bakwai. Wannan shi Hausawa ke ce wa “Mun zo garin ku mun fi ku rawa, to in kun zo garin mu yaya za a yi?
Mahalartan bikin sun ce hakan ya nuna cewa tsarin da aka bi wajen fitar da gwarzayen ba a yi son zuciya ba, kawai dai an nuna tsantsar cancanta.