ALLAH ya yi wa Alhaji Umaru Ɗan Ɗanduna rasuwa, shahararren direban nan wanda Alhaji Mamman Shata ya waƙe shekaru hamsin da su ka gabata.
Ya rasu a gidan sa da ke unguwar Kwanar Jaba a cikin garin Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya. Shekarun sa 88 a duniya.
A wata hira da ya taɓa yi da mujallar Fim a gidan sa a cikin shekarar 2000, Alhaji Umaru ya bayyana cewa shi haifaffen Gwandu ne ta Jihar Kebbi.
An haife shi a cikin 1931.
Ya ce tun ya na yaro matashi ya biyo wani direban babbar mota mai suna Ɗanduna zuwa Kano daga Gwandu, lokacin da direban ya je ɗauko kaya a can.
A Kano, Umaru ya zauna a gidan Ɗanduna Direba a Fagge a matsayin yaron sa har ya koyi tuƙin babbar mota.
A lokacin, shi Ɗanduna ubangidan Shata ne ta hanyar wani babban direban, Jibo Ɗanmaimota, a Fagge.
Ta hanyar waɗannan iyayen gida ne Umaru ya sabu da Shata, wanda ya kan zo gidan a kai a kai.
Ta haka ƙauna ta ƙullu a tsakanin su, har Shata ya kasance mai shawartar Umaru.
A lokacin da Shata ya fara ganin Umaru ya na jan mota, abin ya ba shi mamaki tare da burge shi lokacin da su ka yi wata haɗuwa a Zariya.
Ba lungun da Umaru Ɗan Ɗandyna bai shiga da mota ba a Nijeriya, har ma ƙasashen Afrika da dama ya je da harkar tuƙi, kuma ya yi fice tare da nasara a harkar.
A cikin 1971 ne Shata ya ƙera masa waƙa mai taken ‘Umaru Ɗan Ɗanduna Na Gwandu’, wadda ta kasance ɗaya daga cikin manyan waƙoƙin sa.
Waƙar ta buɗe wa Alhaji Umaru ƙofofi da dama, duk inda ya shiga ana yi masa alfarma, sannan ya zama abin kallo ga kowa.
Shi kan sa ya zama ubangidan kan sa, ya mallaki motocin da ake tuƙa masa, amma daga baya Allah ya jarabce shi da karayar arziki.
Zumuncin su da Shata ya ɗore har zuwa rasuwar Shatan a cikin Yuni, 1999.
A hirar sa da mujallar Fim, Umaru Ɗan Ɗanduna ya ce lokacin da ya ziyarci Shata a asibiti a Kano lokacin da ya kwanta ciwon ajali, su na su biyu Shata ya faɗa masa cewar ya san ciwon sa ba na tashi ba ne.
Shi kan sa Alhaji Umaru ya yi fama da rashin lafiya na tsawon shekaru, kuma ya kasance mai buƙatar taimako.

Idan kun tuna, a ranar 17 ga Janairu, 2020 mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wani daga cikin dattawan Arewa ya yi masa agajin kayan abinci da kuɗi bayan ya ji halin da ya ke ciki a wani shirin Rediyon Tarayya na Kaduna da aka yi da fitaccen marubucin nan kuma ɗan jarida Malam Ibrahim Sheme.
Dattijon, wanda tsohon gwamnan wata jiha ne wanda ba ya so a bayyana sunan sa, ya bada tallafin N100,000 ta hanyar Ibrahim Sheme, inda aka raba kuɗin aka sayi kayan abinci aka kai wa tsohon direban, kuma aka kai masa sauran tsabar kuɗin.
Wanda ya sayi kayan abincin tare da kai kuɗin shi ne fitaccen marubuci kuma ɗan jarida Maje El-Hajeej Hotoro.
A lokacin, wakilin mujallar Fim, Malam Mukhtar Yakubu, wanda tare da shi Maje ya sawo kayan aka kai, ya ruwaito cewa kayan sun haɗa da shinkafa, taliya, makaroni, man girki, sabulai, da sauran su.
A lokacin da ya ke karɓar agajin, tsohon direban ya yi godiya ga Allah dangane da wannan gudunmawa da aka ba shi, sannan ya gode wa mutumin da ya yi masa agajin.
Daga ƙarshe, ya gode wa duk waɗanda su ka yi ɗawainiya don ganin saƙon ya isa gare shi.
Wakilin mujallar Fim ya kira matar Alhaji Umaru Ɗan Ɗanduna a yau, wato Hajiya Zainab, domin yi mata ta’aziyya, inda ta faɗa masa cewa marigayin ya bar ita matar tasa ɗaya da kuma ‘ya’ya bakwai masu rai, sai jikoki sama da 40. Yawancin ‘ya’yan sa sun rasu.
Ɗaya daga cikin masu rai ɗin, Malam Babangida, a ƙasar Nijar ya ke da zama, kuma ya zo Kano jiya domin karɓar gaisuwa. Shi ne ɗan Hajiya Jamma, wata mutuniyar Nijar da marigayin ya taɓa aura, wadda Shata ya ke ambata a waƙar sa, da ya ce: “Umaru ya tai Nijar da Jamma.”
Allah ya jiƙan Alhaji Umaru, ya saka masa da gidan Aljannar Firdausi, amin.