Ya san hanyah hwaɗa,
A’a Musa na ƙasaɗ Ɗa’ali mai tauri!
Kai mutane, tauri ya koma ga gadadde.
Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, wan ƙarhi!
Aha!
Na so zuwa gidan Mani Akaye ina woba, ba ‘yan yara wari na.
Sai yac ce ɗiya nai ba su son tauri.
Tsohon kau ya yi yayi nai,
Nic ce sai nai kiɗi in dai hanyak kiɗi ta taho.
Jama’a, na so zuwa gidan Mani Akaye ina sauna,
Ba hanyak kiɗin tauri.
Ɗan yaro ne Musa,
Ashe ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba.
Rannan sai yaɗ ɗauki kwashe nai,
Yat tasam ma gona tai,
Ya iske Sulluɓawa yab bi ya na bugun shanu,
Yab bi ya na kashe shanu,
Yab bi ya na kashe shanu.
Ashe Musa ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba!
Su na ta bugu su na sara,
Duk dai ba a huda kai nai ba.
Ku am manyan hwaɗa, Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, mai tauri!
‘Yan kai kurwar hwaɗa, mata, kuma sun sheƙa su na kuka:
“Ku yo gudammawa Hillani sun kashe Musa!
“Ku yo gudammawa Hillani sun sabarta shi!”
Har Ɗan’ali zai yo hawa,
Yac ce, “Ko ba ka ji, Mani, Hillani sun kashe ma ɗa?”
Tsoho bai ɓata rai nai ba.
Bai ko kau da kai nai ba, sai yai ta jiƙon ƙarera nai,
Ya san ya shiryi yara nai.
Yac ce, “Ko ba ka ji, tsoho, Hillani sun sabarta ka,
Sun kashe ma ɗa.”
Yac ce, “Ɗan’ali koma gida, ja dan nan ba ni son ƙarya!
Ba ta bugu ba, ba sara, ba kau yaƙin takobi ba,
Don su, Musa na tahowa gida!”
Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali wan ƙarfi!
— KASSU ZURMI, a waƙar Musa na ƙasar Ɗan’ali
Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme, a ranar 1/1/2013
Hoto daga: Chapter One Bookshop, Kano