• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi

by DAGA IBRAHIM SHEME
January 1, 2013
in Mawaƙa
0
Waƙar ‘Musa Na Ƙasar Ɗan’ali’ ta Kassu Zurmi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ya san hanyah hwaɗa,

A’a Musa na ƙasaɗ Ɗa’ali mai tauri!

Kai mutane, tauri ya koma ga gadadde.

Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, wan ƙarhi!
Aha!

Na so zuwa gidan Mani Akaye ina woba, ba ‘yan yara wari na.

Sai yac ce ɗiya nai ba su son tauri.
Tsohon kau ya yi yayi nai,
Nic ce sai nai kiɗi in dai hanyak kiɗi ta taho.

Jama’a, na so zuwa gidan Mani Akaye ina sauna,
Ba hanyak kiɗin tauri.

Ɗan yaro ne Musa,
Ashe ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba.

Rannan sai yaɗ ɗauki kwashe nai,
Yat tasam ma gona tai,
Ya iske Sulluɓawa yab bi ya na bugun shanu,
Yab bi ya na kashe shanu,
Yab bi ya na kashe shanu.

Ashe Musa ya ci magani bai samu wurin gwadi nai ba!
Su na ta bugu su na sara,
Duk dai ba a huda kai nai ba.

Ku am manyan hwaɗa, Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali, mai tauri!

‘Yan kai kurwar hwaɗa, mata, kuma sun sheƙa su na kuka:
“Ku yo gudammawa Hillani sun kashe Musa!
“Ku yo gudammawa Hillani sun sabarta shi!”

Har Ɗan’ali zai yo hawa,
Yac ce, “Ko ba ka ji, Mani, Hillani sun kashe ma ɗa?”

Tsoho bai ɓata rai nai ba.
Bai ko kau da kai nai ba, sai yai ta jiƙon ƙarera nai,
Ya san ya shiryi yara nai.

Yac ce, “Ko ba ka ji, tsoho, Hillani sun sabarta ka,
Sun kashe ma ɗa.”

Yac ce, “Ɗan’ali koma gida, ja dan nan ba ni son ƙarya!
Ba ta bugu ba, ba sara, ba kau yaƙin takobi ba,
Don su, Musa na tahowa gida!”

Manyan hwaɗa Musa na ƙasaɗ Ɗan’ali wan ƙarfi!

— KASSU ZURMI, a waƙar Musa na ƙasar Ɗan’ali

Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme, a ranar 1/1/2013

Hoto daga: Chapter One Bookshop, Kano

Loading

Tags: Adabin HausaHausa literatureHausa musicKassu Zurmimawakan hausaTauriWakar Musa na Kasar Dan'ali
Previous Post

Bugu Da Guduma

Next Post

Alamomi 40 na da’irar Adabin Kasuwar Kano

Related Posts

Tijjani Gandu ba zai iya amsa gayyatar hukuma ba, inji lauya
Mawaƙa

Tijjani Gandu ba zai iya amsa gayyatar hukuma ba, inji lauya

October 5, 2026
Hukumar Tace Finafinai za ta hukunta Tijjani Gandu saboda sakin waƙa ba tare da izini ba
Mawaƙa

Hukumar Tace Finafinai za ta hukunta Tijjani Gandu saboda sakin waƙa ba tare da izini ba

October 3, 2026
Mawaƙin yabon Annabi, Kamsusi Bala Maiyafe, ya kwanta dama
Mawaƙa

Mawaƙin yabon Annabi, Kamsusi Bala Maiyafe, ya kwanta dama

September 7, 2026
An zaɓi Bashir Yahuza Malumfashi shugaban sha’iran Jihar Katsina
Mawaƙa

An zaɓi Bashir Yahuza Malumfashi shugaban sha’iran Jihar Katsina

September 2, 2026
Hassada da gasa ne matsalar sha’irai mata – Shamsiyya Khadimar Ma’aiki
Mawaƙa

Hassada da gasa ne matsalar sha’irai mata – Shamsiyya Khadimar Ma’aiki

August 30, 2026
Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar
Mawaƙa

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar

August 23, 2026
Next Post
Alamomi 40 na da’irar Adabin Kasuwar Kano

Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!