AKWAI yiwuwar Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano za ta hukunta shahararren mawaƙi, Tijjani Gandu, saboda zargin karya dokokin hukumar da ya yi, bayan sakin wata waƙa ba tare da samun izinin ta ba.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar 3 ga Oktoba, 2026, a madadin Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, an bayyana cewa hukumar ta gayyaci mawaƙin domin amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.
Sanarwar ta ce wajibi ne ga duk wani mawaƙi ko marubuci ya gabatar da aikin sa ga hukumar kafin sakin sa ga jama’a.
Ta ce manufar wannan tanadi ita ce bai wa hukumar damar tantance ayyukan, tare da tabbatar da cewa ba su ƙunshi kalmomi ko abubuwan da ka iya haifar da tashin hankali, tada zaune tsaye ko kawo barazana ga zaman lafiya a cikin al’umma ba.
Hukumar ta ce dokar da ta kafa ta ba ta ikon tantance waƙoƙi da sauran ayyukan da suka shafi harkokin tace finafinai da ɗab’i, don haka ba za ta ci gaba da yin biris da yadda wasu suke karya dokokin ta a ƙarƙashin hujjar ‘faɗin albarkacin baki’ ba.
Ta jaddada aniyar ta ta tabbatar da bin doka da oda a cikin ayyukan ta, tare da tabbatar da adalci ga dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da nuna wariya ko son kai ba.
Saboda haka, hukumar ta yi kira ga Tijjani Gandu da ya mutunta gayyatar da aka yi masa, tare da girmama dokokin da suka shafi harkar nishaɗi da adabi a jihar.
Ta kuma yi gargaɗin cewa rashin amsa gayyatar na iya tilasta mata ɗaukar matakan da suka dace kamar yadda doka ta tanada.
Hukumar ta kuma yi kira ga sauran mawaƙa, marubuta da masu ruwa da tsaki a harkar nishaɗi da adabi da su ci gaba da bin dokoki da ƙa’idojin da aka shimfiɗa, domin tabbatar da zaman lafiya, daidaito da cigaban masana’antar nishaɗi da adabi a Jihar Kano.
![]()






