AL’UMMAR Musulmi, musamman ma mazauna Kano, sun wayi gari cikin jimami a safiyar ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, sakamakon rasuwar fitaccen mawaƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.), Malam Kamsusi Bala Maiyafe.
Marigayin ya rasu ne a daren ranar Asabar, 5 ga Satumba, 2026, a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke cikin garin Kano, bayan fama da rashin lafiya.
Malam Kamsusi, mai shekaru 57 a duniya, ya rasu ya bar mata guda ɗaya da ‘ya’ya bakwai.
Marigayin na daga cikin fitattun mawaƙa da mawaƙan yabo da suka yi fice musamman a lokacin da waƙoƙin Madihu suka yi tashe. Ya shahara matuƙa da waƙarsa mai suna “Manzona Sayyadi”, wadda ta samu karɓuwa sosai a tsakanin masoya waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.) tun a shekarun baya.
Baya ga haka, Malam Kamsusi Bala Maiyafe ɗa ne ga fitaccen malamin ilimin addinin Musulunci kuma masani a fannin ishiriniya, Marigayi Malam Bala Maiyafe.
Da yake bayyana yadda rashin lafiyar Malam Kamsusi Bala Maiyafe ta fara da kuma yadda ta kai ga rasuwarsa, wani babban makusancinsa, Malam Umar Tauraruwa, ya ce marigayin ya fara fama da rashin lafiya tun kusan watanni shida da suka gabata.
A cewarsa:
“Malam Kamsusi Bala Maiyafe ya samu rashin lafiya ne tun kusan watanni shida da suka wuce, bayan mun kammala hidimar bikin ‘yarsa. Daga nan ya fara zuwa asibiti ana duba lafiyarsa.
“Amma kusan makonni biyu da suka wuce ne rashin lafiyar ta ƙara tsananta, inda har aka kai shi sashen kulawa ta gaggawa na Asibitin Ƙwararru na Murtala. Bayan ya yi kwanaki biyar a can, sai aka mayar da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda ya yi kwanaki uku kafin Allah ya karɓi ransa a daren ranar Asabar.”
An gudanar da jana’izar marigayin a gidansu da ke Unguwar Gwammaja, kafin daga bisani aka kai gawarsa makabartar Ƙofar Mazugal da ke cikin garin Kano, inda aka yi masa jana’iza.
Rasuwar Malam Kamsusi Bala Maiyafe babban rashi ne ga al’ummar Musulmi da kuma masoya waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.), musamman waɗanda suka taso suna sauraron waƙoƙinsa masu ɗauke da saƙonnin yabon Annabi Muhammadu (S.A.W.).
![]()







