• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Wai shin wanene Bahaushe?

by DAGA ABDALLA UBA ADAMU
October 24, 2021
in Tsokaci
0
Wani dattijo a bakin aiki a marinar Birnin Kano

Wani dattijo a bakin aiki a marinar Birnin Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN abin da za a fara tambaya a nan shi ne, wai shin wanene Bahaushe? 

Wannan tambayar ta na da ban-mamaki domin ganin cewa babu wata ƙabila da ake tantamar salsalar ta a Nijeriya. Misali, idan aka ce Yarabawa, an san waɗanda ake nufi. Amma da zarar ka ce Hausawa, sai a fara musu domin ana ganin yawan gaurayar al’ummomi, da kuma iya yaren Hausa na mutane da yawa ya sa ba ma za a iya cewa ga Bahaushe ba. 

Wannan tunani ya ƙarfafa a bisa nazarin wani mai nazarin harshe da ake kira Joseph Greenberg, wanda ya rasu a Amurka a ranar 7 ga Mayu, 2001 ya na ɗan shekara 85. A turbar nazarin da ya gina, Greenberg ya jagoranci ra’ayin cewa babu wata ƙabila Hausawa, domin su kan su Hausawan, a wajen su kalmar “Hausa” ta na nufin yare – misali za ka ji mutum ya ce, “ba na jin hausar wancan mutumin” – watau a nan, Hausa yare ne kenan.  Sannan kuma kusan kowane Bahaushe za ka ji ya ce da kai ai shi ainihin iyayen sa Fulani ne, Buzaye ne, Barebari ne, da dai sauran su. Amma kuma in ka tambaye shi ko ya na jin yaren na waɗancan mutanen, sai ya ce da kai ba ya ji. Wannan shi ke daɗa dagula Hausa da Hausanci, a rasa ma wai shin wanene Bahaushen.  

A wani hasashen an danganta samun ƙabilar Hausawa da auratayyar al’ummomi daga Afrika ta Arewa inda zaunannun waɗannan wurare su ka gauraya da Buzaye, sannan aka samu Hausawa. Wannan kuwa ya faru ne a tsakanin 1050 da 1100. Amma kuma wani manzarcin ya ƙalubalanci wannan hasahen inda ya ce babu wata tabbatacciyar hujja da ta nuna samun Hausawa bisa wannan auratayyar al’ummomin. A ganin wannan manazarcin, in an ce “Ƙasar Hausa”, to ana nufin yankin da ake magana da yaren “Hausa”, ba wai wata ƙabila ba. 

Sauran ra’ayoyin manazarta su ma sun ginu ne a kan wannan ra’ayin. Ta haka, misali, Niven ya ce kalmar “Hausa” asalin ta ta Buzaye ce, domin da wannan sunan su ke kiran duk wanda ya fito daga arewancin Kogin Kwara. A wannan nazarin, Hausa kalma ce wadda Buzaye ke kiran duk baƙar fatar da ke inda Larabawa ke kira Sudan. 

Abin mamaki, ita wannan kalmar ma ta na nufin mutanen Abissiniya, watau Habasha, wanda wannan ya kawo hasashen cewa Hausawa daga Habasha su ke; yanzu kam mun gane cewa kiran Hausawa da Hausa da kuma kiran Habashawa da Hausa, duk aikin Buzaye ne. 

Sannan kuma yin amfani da kalmar ma ƙasƙanci ne na wariyar launin fatan da Buzaye ke yi wa ɗuk wani baƙin mutum. Misali, tunda Hausa ta na nufin Bahaushe da kuma Bahabashe, sai aka samu wata danganta ta yadda a harshen Habashanci, “habshi” na nufin haushin kare. Saboda haka a wajen Buzayen wancan lokacin, duk wanda ke magana da waɗannan yarurrukan, to Bahabshi ko Bahaushe ne. 

A taƙaice dai, an daidata furucin Hausa da haushin kare, wanda kuma su Hausawa su na yin haka ga waɗansu ƙabilun inda in mutum ba ya jin Hausa, sai su ce, “Bagwari ne”.  

Neil Skinner kuwa cewa ya yi kalmar “Hausa” ta fito daga mutanen Songhai (inda Mali ta ke a yanzu) ne, domin su ne su ke kiran duk ƙauyukan da ke gabas da su “hausa” ko “aussa”, daga nan ne su “Hausawan” su ka ari wannan kalmar su ke kiran kan su da ita – watau kafin wannan ba su da wani suna da su ke kiran kan su! 

Sannan kuma manazartan tarihin ƙasashen Larabawa sun ziyarci ƙasar Hausa amma duk a rubutun su ba su ambaci kalmar “Hausa”  a matsayi sunan ƙabilun da su ka haɗu da su ba. 

Marubuta kamar su Leo Africanus wanda ya ziyarci ƙasar Hausa wajen shekarar 1513 zuwa 1515, bai ambaci mutanen da sunan Hausawa ba, sai dai ya ce “Mutanen Kano”, “Mutanen Katsina”, da sauran su. Yaren su kuma sai ya ce su na magana da yaren “Mutanen Gobir”.  

Wannan ya nuna cewa jimlar kalmar “Hausa” a matsayin nuni ga wata ƙabila sabon abu ne wanda bai wuce shekaru 400 ba. 

Amma kuma akwai daulolin Hausawa da masarautun Hausawa da ake magana da harshen Hausa fiye da shekaru 1,000 da su ka wuce. Idan haka ne, ashe Hausanci ba a yaren ya tsaya ba, akwai ƙabila wacce ta ke da salsala. Maƙala sunan “Hausawa” a matsayin masu magana da yaren “Hausa” abu ne wanda waɗansu su ka yi wa Hausawan, amma ba su Hausawan da kan su ba, kamar yadda Hausawa ke cewa da ƙabilar Igbo na Nijeriya “Inyamurai”, wanda kuma ba haka su Igbo su ke kiran kan su ba.  

Wasu makaɗan Hausa a kan aikin su

Saboda haka ko da lokacin da Leo Africanus ya zo Kano, daular Kano ta yi fiye da shekaru 500 da kafuwa, kuma da Hausa ake tafiyar da ita. Ashe Hausanci ba yare ne ba, akwai ƙabila Hausa. A nan, na fi karkata ga Muhammad Sani Ibrahim inda ya ce, Hausa suna ne da ya ke da ma’anar Harshe, da mutanen da su ke magana da shi, da kuma ƙasar da ake magana da shi. 

Saboda haka sai mu koma tambayar farko, shin wanene Bahaushe? 

Amsar a nan ita ce duk wanda salsalar sa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe ba ne, to kai ma ba Bahaushe ba ne. Na aro wannan ma’aunin bisa cewa Hausanci ƙirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali, a ƙasar Turawa, in a cikin iyaye da kakannin ka akwai baƙar fata, to ko ka fi madara fari a matsayin baƙar fata ka ke. A wannan ma’aunin, babu maganar zama a wata al’umma da kuma sanin yaren ta, domin ka zama ɗan wannan al’ummar (a nan, ƙabilar). Misali, duk iya Larabcin baƙar fatan da ya zauna a garin Makka, ba za a taɓa kiran sa Balarabe ba, ba wai kawai don akwai bambancin tsakakin fatar Balarabe na aihini da baƙar fata ba, a’a, kawai ba Balarabe ba ne, kuma shi ma ya san haka. Haka duk iya Turancin baƙar fata a Ingila ba za kira shi Ingilishi ba, sai dai ɗan ƙasar Ingila, domin Ingilishi (English) ƙabila ce a Ingila tare da Sikotawa (Scottish), Airishawa (Irish) da kuma Walshawa (Welsh), kuma duk waɗannan Turawa ne, farar fata; babu baƙi a cikin su. Su kan su a Ingila ɗin, za ka ji mutum na alfahari da ƙabilar sa – misali, duk da cewa shi fari ne, amma zai ce maka shi Ba’airishe ne, ba Ingilishi ba. 

Saboda haka kamar Hausa, in ka ce “English” to ana nufin yaren da kuma Ƙabilar. Ta haka za a bambanta cewa “wannan mutumin British ne, amma fa ɗan ƙabilar Walshawa ne”. 

Bari in dawo Nijeriya. Idan misali wani Bayarabe da matar sa su ka bar ƙasar Yarabawa fiye da shekaru 100 da su ka wuce, su ka yada zango a wata unguwa a Kano su ka yi zuri’a, to komai nisan zuri’ar da waɗannan iyayen zuri’a, duk a Yarabawa su ke. Halin zamantakewar su zai iya sa waɗanda aka haifa daga baya ba su ma san yaren iyayen nasu na asali ba, sai Hausa. Duk da haka, Yarabawa ne, domin salsalar su ce. Idan dole sai an danganta su da Hausa, to a iya kiran su abin da na ƙirƙiro da HAUSAWAN ZAMANTAKEWA. Amma ba Hausawa ba ne, domin Hausa ta wuce yare, ƙabila ce, tare da al’adun ta na musamman, da kuma ɗabi’o’in ta. 

Mutum zai iya rungumar waɗannan domin ya zama Bahaushen Zamantakewa, amma ba zai zama Bahaushe ba, kamar yadda mutum zai iya karɓar rayuwar Larabawa domin ya zama ɗan, misali, Dubai, amma ba zai taɓa zama Balarabe ba in ba shi ba ne. 

Wannan misalin ma ya fi kusa da Fulani. Kusan a ƙasar Hausa da yawa mutane na iƙirarin su Fulani ne – amma ba su iya yaren Fillanci ba. Ƙirar halittar su da kuma riƙe aƙidar pulaaku (aƙidar Fillanci) su ne za su tabbatar da su a Fulani, duk da yake ba su iya yaren ba, sai Hausa zalla.  Idan iyayen salsalar sun ƙi su koya wa zuri’ar su yaren su domin su na son su ɓace su zama Hausawa (ko kuma mazaunan inda su ka sami kan su), wannan ruwan su, amma wannan ba zai kankare masu Yarabancin ko kuma Fulatancin ba. 

Mu danganta da cewa komai daɗewar Bahaushe a Shagamu, ba zai taɓa tsammanin shi Bayarabe ne ba. Ta haka za a ga Hausawan Kamaru da Ghana da Kwango, misali, waɗansu ba sa jin Hausar sosai, ko kuma su na yin Hausar wata iri, wacce ta bambanta da Hausar ƙasar Hausa, amma kowane daga cikin su zai danganta salsalar sa da wani gari a ƙasar Hausa.  

Wannan ya na daga cikin ban-mamakin albarkar da Allah ya yi wa Hausa da Hausawa – kullum waɗanda ba Hausawa sai so su ke a ɗauke su a matsayin Hausawa, duk da cewa su na da tasu ƙabilar – da aƙidojin – wacce ya kamata su ɗaukaka. 

* Farfesa Abdalla Uba Adamu babban malami ne a Jami’ar Bayero, Kano

Loading

Tags: Abdalla Uba AdamuAbissiniyaasalin HausawaBagwariBahausheBarebariBuzayedaular KanoFulaniHabashahausanciIngilishiInyamiraiJoseph GreenbergkabilaKogin KwaraLarabawaLeo AfricanusMakkaMuhammad Sani IbrahimNeil SkinnerTurawaYarabawa
Previous Post

Ƙasidatu Tarihin Sarakunan Kano (Waƙar Bagauda)

Next Post

Umaru Ɗan Ɗanduna, direban da Shata ya waƙe, ya rasu ya na da shekara 88

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Alhaji Umaru Ɗan Ɗanduna a cikin Janairu, 2000. Hoto daga: Mukhtar Yakubu

Umaru Ɗan Ɗanduna, direban da Shata ya waƙe, ya rasu ya na da shekara 88

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!