• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙasidatu Tarihin Sarakunan Kano (Waƙar Bagauda)

by DAGA ABUBAKAR BAƘIN RUWA
October 22, 2021
in Marubuta
0
Surar birnin Kano da aka zana a cikin 1850

Surar birnin Kano da aka zana a cikin 1850

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Wanda ya rera: Abubakar Baƙin Ruwa
Wanda ya rubuta a ajami: Shu’aibu Kabuga
Farfesa Abdalla Uba Adamu ya alkin ta mana ita.
Sadiq Tukur Gwarzo ya kawo maku ita daga ajami zuwa hausar boko.

Bismillahir Rahmanir Raheem. Sallallahu Ala sayyidina Muhammad wa ahlihi wa sahbihi wa zurriyatihi wa sallim taslima.

Ta’ala Rabbuna sarkin sarauta,
Kariymu Rahiymu Allah ne da baiwa.

Idan roƙo gare ka ka roƙi Allah, 
Gama shi ne ya ba wa kowa.

Sarauta da dukiya da duniya ta ba ka,
Ka bar cira kai ka na rowa ciccikawa.

Ka bar hura hanci duniya ce, 
Abin da ta ba ka ba ya tabbacewa.

Ka duba sarakunan da aka yo a baya,
Da labarinu ya riƙa sai ɓacewa.

Bagauda shi ya sari Kano da fari, 
Ta na daji sa’annan babu kowa.

Ya na Gaya shi Bagauda gidan sa,
Maharbi ne riƙaƙƙe mai kashewa.

Ya zo cirani ya yi bukka Maɗatai, 
Ya zauna ‘yan’uwan sa su na tafowa.

Maharba gwargwado su ka ɗaura taro, 
Gun sa su na kisan zaki da giwa.

Da nama ya yi yawa ɗanye ƙafaffe, 
Fa ba mata maza ne ke dafawa.

Da Gwale da shi da Yakasai da Sheshe,
Da Guguwa manya-manyan Maguzawa.
 Ana cewa da su su ne sarakai, 
Na noma sun ka zo dawa gewayawa.

Su ka kulle dawa su ka kama gona,
Fa sai aiki iyali na tafowa.

Ga Malam Nuhu na ji babu ƙage,
Batu na ba shi tare da ƙaryatawa.

Manoman da sun ka tafo da fari,
Su kan sara su na kuma dandaɗewa.

Sa’annan sai ruwan bazara ya sauka,
Su kai shukar su ta rinƙa furfutowa.

Su kai dawa, gero ba misali, 
Aka samu ana kuma ribatawa.

Su kai ƙarfi na bayi har dawaki, 
Da su ne manya-manyan tajirawa.

Gabas ta taho da yamma har arewa,
Wajen kudu sun ka ɓarko Maguzawa.

Da Barnawa da Katsinawa da Daura, 
Da Zamfara can ta Habi da Gobirawa.

Mutan Zurmi da su da mutan Talata,
Bakura da su Anka su na tafowa.

Su kai ta awo su na kamun gidaje,
Kabawa da Kumburawa da Adarawa.

Da tun daga Yankatsari gida ya zaga, 
Ta Mariri ya kawo Gunduwawa.

Mutane na asarari sun yi shanya, 
Da babu sarki fa, babu wurin tsarewa.

Da Tunbi da Sudawa shashen-ga nayza,
Su na gama kai su na kame Kanawa.

 Da manya su ka ce sai an sarauta,
Su kai Sarki Bagauda mai tsarewa.

Loading

Tags: Abubakar Bakin RuwaajamiBagaudaBirnin KanobokoGayaMaguzawaProf. Abdalla Uba AdamuSadiq Tukur GwarzoShu'aibu Kabuga
Previous Post

Cewar INEC: Za mu ba maraɗa kunya a zaɓen Anambra

Next Post

Wai shin wanene Bahaushe?

Related Posts

Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye
Marubuta

Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye

August 30, 2026
Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta
Marubuta

Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

August 27, 2026
Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai
Marubuta

Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai

August 24, 2026
Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Next Post
Wani dattijo a bakin aiki a marinar Birnin Kano

Wai shin wanene Bahaushe?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!