A BINCIKEN wata harƙalla bayan ta ginin filin jirgi a Zamfara, gwamnatin jihar ta fitar da sababbin hujjoji waɗanda ke fallasa yadda tsohon gwamna kuma Ƙaramin Ministan Tsaro a yanzu, Bello Matawalle, ya rattaba hannu kan fitar da biliyoyin kuɗi don aikin gidajen saukar gwamna.
Tsohuwar gwamnatin ta Matawalle ta ƙirƙiri aikin ginawa tare da sayo kayayyaki don gidajen saukar gwamna a ƙananan hukumomi 14 da ake da su a jihar.
Wata takardar sanarwar manema labarai da Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Lahadi a Gusau ta bayyana cewa takardun da aka fitar su na cikin jerin salsalar fallasa irin ɓarnar da Matawalle ya tafka a lokacin ya na gwamna.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Dauda Lawal ba za ta yi shiru ko kawar da kai kan satar rashin imani da tsohuwar gwamnatin ta aikata ba, musamman inda aka bayar da ayyuka, aka kwashi biliyoyi kuma aka yi watsi da ayyukan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ya saɓa wa ƙa’idar gudanarwa a tsarin gwamnati, haka kawai mutum ya biya kuɗi ɗari bisa ɗari kan kwangilar da ba a fara aiwatarwa ba.
“Za ka taras da irin waɗannan kwangiloli, ga su nan birjik an sace kuɗaɗen al’umma da sunan yin su.
“Za mu bibiyi duk waɗanda suka tafka irin wannan sata, domin mu dawo wa da al’umma haƙƙin su.
“Daga cikin irin waɗannan ayyuka da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta kwashe kuɗaɗe da sunan su akwai batun ginin gidajen saukar gwamna a Ƙananan Hukumomi 14 na jihar, wanda tun kafin ma a fara aikin aka kwashe biliyoyi da sunan kuɗin sayo kayan gidajen.
“Bello Matawalle ya fitar da kuɗi don biyan mafi yawa daga cikin ‘yan kwangilar. Misali, ya tura wa kamfanin BES BELMON Nigeria Limited Naira 1,966,035,160.00 a ranar 27 ga Disamba, 2021 domin aikin katangewa, sayo kayayyakin cikin gida, da sanya wutar lantarki ga waɗannan gidajen saukar gwamna guda 14, tun ma kafin a fara aikin su.
“An biya gaba ɗaya kuɗaɗen aiki ga ‘yan kwangilar da ke aikin gina gidajen na saukar gwamna a ƙananan hukumomin Ƙaura Namoda, Zurmi, Bakura, Maradun, Bukkuyum, Bunguɗu da Gummi, tun kafin a fara aikin.
“A ranar 30 ga Afrilu, 2020 gwamna ya rattaba hannu don a fitar da kuɗi Naira 324,410,211.00 ga kamfanin SWAT AGA Construction Limited domin a gina gidan saukar gwamna a Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda. An fitar da wannan kuɗin ne daga Ma’aikatar Kananan Hukomomi da Masarautu.
“Haka kuma a ranar dai 30 ga Afrilu, 2020 ɗin an sake fitar da naira 324,410,211.00 ga kamfanin na SWAT AGA Construction Limited, a matsayin kuɗin aikin ginin gidan saukar gwamna a Ƙaramar Hukumar Zurmi.
“Ƙarin abin haushi, wannan kamfanin na BES BELMON wanda aka biya sama da biliyan ɗaya don sayo kayan gidajen da ba a kammala ginawa ba, shi ne a ranar 30 ga Afrilu, 2020 aka sake fitar da 324,410,211.00 aka ba shi don ya gina gidan saukar gwamna a Ƙaramar Hukumar Maradun.
“Mu na so a fahimci irin badaƙalar da kamfanin BES BELMON Nig. Limited ke ciki, musamman tarayyar da ya yi wurin fitar da kuɗaɗe daga baitilmalin Jihar Zamfara ba tare da ƙa’ida ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A dai ranar 30 ga Afrilu, 2020 ne Bello Matawalle ya sake fitar da naira 324,410,211.00 ga BES BELMON don gina gidan saukar gwamna a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum. Abin tambayar shi ne, wanene ke da wannan kamfani na BES BELMON?
“Duk dai a ranar 30 ga Afirilu, 2020, Bello Matawalle ya sa aka fitar da naira 324,410,211.00 aka ba BES BELMON a matsayin kuɗin gina gidan saukar gwamna a Ƙaramar Hukumar Bunguɗu.
“Gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da bankaɗo sama da faɗi da rashin gaskiyar da aka tafka, ba don komai ba sai domin tabbatar da adalci.
“Saboda haka ne ma mu ke kira ga kamfanin BES BELMON Nigeria Limited da ya gaggauta dawo wa gwamnatin da naira 1,966,035,160.00 da Bello Mohammed Matawalle ya biya shi ba tare da ƙa’ida ba. Aikin ceto mu ka zo yi, ba za mu ɗaga wa maha’inta ƙafa ba.”
Haka sanarwar ta bayyana a shafin Facebook na Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Dauda Lawal, wato Sulaiman Idris.