YAYAN mawaƙi a Kannywood Ado Gwanja, wato Alhaji Sa’idu Gwanja, ya bayyana ra’ayin sa game da auren da ƙanen nasa ya yi a yau Juma’a, 21 ga Yuli, 2023.
Sa’idu Gwanja ya yi magana ne a hirar da ya yi da mujallar Fim jim kaɗan bayan an ɗaura auren.
Shi dai Ado Isah Gwanja, an ɗaura masa aure ne da abar ƙaunar sa, Maryam Zubair Muhammad Paki, da misalin ƙarfe 1:00 na rana a Masallacin Juma’a da ke cikin Jami’ar Yusuf Maitama Sule (Northwest University), Kano, a kan sadaki N100,000.
‘Yan fim da mawaƙa da dama sun halarci ɗaurin auren.
Wannan shi ne aure na biyu da ya yi. Idan kun tuna, ya yi auren fari ne da wata yarinya mai suna Maimunatu Ɗan’auta, amma su ka rabu bayan sun haifi ‘ya guda ɗaya.

Kafin ranar ɗaurin auren na yau, an yi walima a ranar Laraba, sannan kuma jiya Alhamis an yi dina, inda mawaƙa da ‘yan fim su ka nuna wa abokin sana’ar nasu kara.
Mawaƙan da su ka baje kolin su a wurin dinar sun haɗa da Nura M. Inuwa, Auta Waziri, Ali Namenj, da Kawu Ɗansarki.
Ra’ayin da Alhaji Sa’idu Gwanja ya bayyana a kai shi ne tsantsar farin ciki tare da fatan alheri.
Ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Gaskiya ina matuƙar farin ciki da alfahari da wannan aure da aka yi. Ka san shi ba ɓoyayye ba ne, ba ta yadda za a yi abu babu wanda ya sani. In ka lura ko matar ba a nuna ta a bidiyo ko hoton ta, inda abin da aka saba na wancan ‘party’ ɗin.
“Kuma alhamdu lillahi, ɗaurin auren ya yi armashi fiye da yadda ba ka zato. Na ji daɗin sa ta sigar da aka bi aka ɗaura auren, kamar ba na ‘celebrity’ ba.

“Cikin ikon Allah ma sai da mu ka gama ɗaurin auren sannan shi ango ya zo, wuri ya ƙara taruwa, don mu a nan mu ka bar su ma ya na karɓar gaisuwar mutane. An yi ɗaurin aure yadda aka saba bisa Kitabu wa sunna.
“Ina fatan Allah ya ba su zaman lafiya.”





