• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yaƙin Badar tsakanin Buba Marwa da ‘yan ƙwaya

by DAGA IBRAHIM SHEME
February 26, 2021
in Tsokaci
0
Yaƙin Badar tsakanin Buba Marwa da ‘yan ƙwaya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR Litinin da ta gabata, sabon shugaban hukumar yaƙi da safara da shan muggan ƙwayoyi (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya), ya yi wata magana wadda ya kamata ta farkar da duk ɗan Nijeriya game da matsalar da fataucin muggan ƙwayoyi ke janyo wa ƙasar nan. Cewa ya yi kashi 90 cikin ɗari na muggan laifukan da ake aikatawa a Nijeriya, sakamakon ɗirkar muggan ƙwayoyi da wasun mu ke yi ne. A cewar sa, laifuka irin su hare-haren ‘yan bindiga, ta’adda, satar mutane, fyaɗe da sauran su duk ‘yan ƙwaya ne ke aikata su. 


Marwa, wanda ya yi wannan maganar a tashar ruwa ta garin Onne na Jihar Ribas lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga ma’aikatan hukumar sa, ya ce: “Babu wani wanda ke cikin hayyacin sa da zai ɗauki makami ya saci mutum, ya yi fyaɗe kuma ya kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Saboda haka idan mu ka samu nasarar magance matsalar shan ƙwayoyi, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta a yau.” 


A wani jawabin da ya yi wa shugabannin addini a jihar kuma, Marwa ya yi gargaɗin cewa, “Idan har ba mu tashi gaba ɗayan mu mun yaƙi wannan bala’i ba a yanzu, to ya zuwa shekara ta 2050, za a samu aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 30 da ke shan ƙwaya, wanda hakan babban haɗari ne ga ɗorewar wannan babbar ƙasar tamu.”


A gaskiya, waɗannan maganganu ba abin yadawa ba ne. Janar Marwa ya yi magana wadda ya kamata ta dami kowa, domin kuwa matsalar shan muggan ƙwayoyi babba ce, musamman a tsakanin matasa. A yau, kusan babu garin da matsalar ba ta yi katutu ba, ana ta tirka-tirka da ita. Matasa da dama (wai har da mata!) sun zama ‘yan ƙwaya, wanda hakan ya na jawo matsaloli daban-daban a cikin al’ummar mu.

Matsalolin sun haɗa da na rashin tsaro kamar yadda Janar Marwa ya faɗa. To kuma akwai rashin kunya da ƙin bin iyaye ko shugabanni da yin watsi da addini da rashin maida hankali ga aiki ko sana’a da dabar siyasa da cin zarafin mata da ‘ya’ya a cikin zaman aure. Uwa-uba kuma ana samun ƙarin taɓuwar hankali. Allah kaɗai ya san illar da haɗakar waɗannan matsalolin ta ke janyo wa qasa ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.


Nauyin yaƙi da ‘yan ƙwaya ya rataya ne a wuyan hukuma da ita kan ta al’umma. Shi dai Marwa, tun daga lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi matsayin shugaban NDLEA a farkon watan jiya na san an an aje ƙwarya a daidai gurbin ta. Dalili shi ne an daɗe ya na shugabantar wani kwamiti da Buhari ya kafa kan shawarta yadda za a kawar da amfani da ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba (wato ‘Presidential Advisory Committee for the Elimination of Drug Abuse’, PACEDA) daga 2018 zuwa Disamba 2020. Wannan aikin ya ba shi masaniya mai zurfi kan yadda ake safarar muggan ƙwayoyi da yadda ake shan su, kuma ya fahimci hanyoyin da za a bi domin a tunkari matsalar. 


Da ma can Marwa ya yi kyakkyawan suna a wajen yaƙi da ɓatagari a lokacin da ya riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Legas a zamanin gwamnatin Abacha. A lokacin, laƙabin sa ma shi ne ‘Gwamna Ba-wasa’ duk da yake mutum ne mai fara’a. Akwai wani shiri da ya gudanar a Legas mai suna ‘Operation Sweep’ inda ya yi amfani da binciken sirri wajen yaƙi da ‘yan fashi da makami, ya sa su ka kwashi kashin su a hannu.


Ilai kuwa, tun da ya hau wannan sabuwar karagar, bai tsaya nawa ba, ya shiga yaƙin babu ƙaƙƙautawa. Da alama, allurar sa ta soja ba ta yi sanyi ba duk da yake yanzu shekarun sa 67 a duniya. Ya sha alwashin sai ya ga bayan manyan fataken muggan ƙwayoyi – masu shigo da su daga ƙasar waje da masu safarar su zuwa waje. 

Abin burgewa, ana naɗa shi aka fara ganin canji. Marwa ya ƙwace muggan ƙwayoyi da kuɗin su ya kai naira biliyan 30 a Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas. Akwai mutumin da aka same shi da kilogiram 26.840 na ƙwayoyi shi kaɗai, wanda an shekara sama da 15 rabon da a kama mutum guda da ɗaurin ƙwayoyi mai girman haka.


Ya aka yi haka ta faru? Saboda jami’an NDLEA sun fara sauya rawa, tunda sun ji Marwa ya sauya musu kiɗa. Sanin kowa ne cewa ana haɗa baki da wasu ɓatagari a hukumar ana yin safarar ƙwayoyi, musamman ta hanyar jiragen sama da na ruwa da kuma kan iyakokin mu. Marwa ya ce wannan ‘sabuwar NDLEA’ ce; ba waje ba ne da ma’aikaci zai zo domin ya kuɗance ta hanyar wannan muguwar safarar.


A jihohi da yawa, jami’an hukumar sun tashi tsaye. Misali, a Jihar Neja kaɗai an kama ƙwayoyin da su ka kai kilo 603.24 a cikin ‘yan kwanakin nan. Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Isaac Aloye, ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a jiya Alhamis cewa ƙwayoyin da aka kama su ne: kilo 601.443 na kannabis satiba, kilo 0.0024 na Tramadol da kilo 1.8 na Exol-5. An ƙiyasta kuɗin su ya kai naira miliyan 18.7. Kuma jami’an hukumar sun kama mutane da yawa; sun kai wasu kotu, wasu an miƙa su ga iyayen su don su ja masu kunne, yayin da kuma ana ci gaba da bincikar wasu.


Su ma ƙasashen duniya, sun ga abin da Marwa ya zo da shi, don haka sun nuna cewa za su goyi bayan hoɓɓasan sa. A wata ganawa da ta yi da shi lokacin da ta kai masa ziyara a ofishin sa a Abuja, Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, ta nanata wa Marwa ƙudirin gwamnatin Amurka na tallafa wa Nijeriya wajen yaƙi da waɗannan ɓatagarin. Shi ma Jakaden Faransa a Nijeriya, Jerome Pasquier, ya ziyarci Marwa, kuma ya faɗa masa cewa a shirye ƙasar sa ta ke ta haɗa gwiwa da Nijeriya a kan matsalar muggan ƙwayoyi, musamman koken da kannabis.

Furucin waɗannan jakadun ya ƙara tabbatar da cewa yaƙi da safarar muggan ƙwayoyi ba alhakin Nijeriya kaɗai ba ne, yaƙi ne na ƙasa da ƙasa. Dillalan ƙwayoyi ‘yan kasuwar ƙasa da ƙasa ne, kuma burin su shi ne su kai hajar su ƙasashen da su ka ci gaba inda za su wazgi ƙazamar riba. Ta haka, bayan sun lalata rayuwar mutanen mu, sai kuma su lalata rayuwar mutane a waɗancan ƙasashen. Saboda haka tilas sai an haɗa hannu da hannu sannan za a iya tunkarar su.


Amma ya kamata mu sani cewa duk irin kiɗan da gwamnati da ƙasashen ƙawancen ta za su yi, su ma al’ummar ƙasa akwai tasu rawar. Kamar yadda Janar Marwa ya ce, “Ya kamata mu ɗauki wannan yaƙi a matsayin wani gumurzu na ceton ‘ya’yan mu da matan mu, da kuma al’ummar mu da ƙasar mu baki ɗaya.” 


Don haka tilas ne iyaye da shugabannin addini da na al’umma su bada tasu gudunmawar wajen wannan yaƙi. Su sanya ido a kan ‘ya’yan su da sauran jama’a, su hana sayar da ƙwaya a cikin unguwa ko makaranta ko wurin aiki; ‘yan siyasa kuma su daina tallafa wa ‘yan daba wajen shan ƙwaya. Kamar yadda Jiniya Bambo ya ce a wata waƙa: “mu san ƙwaya masifa ce, ta kan sa mutum ya lalace”.


Hausawa sun ce hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Don haka mu taru mu taimaka wa Janar Buba Marwa a wannan yaƙin Badar ɗin. Kuma mu taya shi da addu’a, domin ‘yan ƙwaya muggan mutane ne, musamman da yake su na da ɗaurin gindi da tanyo fiye da yadda ake tunani. Allah ya ceci ƙasar mu, amin.

Ma’aikatan NDLEA a cikin gonar wiwi
Tags: Ambassador Jerome PasquierAmbassador Mary Beth LeonardBuba marwacannabis sativadrug abusedrug moneyExol-5Jiniya BamboLagos Operation SweepNDLEANigeria crimesNigeria drugs warTramadolwiwi
Previous Post

Daraktan Kannywood Sheik Isa Alolo ya zama angon Basira

Next Post

INEC za ta yi wa ma’aikatan faɗakarwa bita kan faɗakarwa

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
INEC za ta yi wa ma’aikatan faɗakarwa bita kan faɗakarwa

INEC za ta yi wa ma'aikatan faɗakarwa bita kan faɗakarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!