• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda ɗa na, Garkuwa, ya rasu a cikin kogi – Mawaƙi Abubakar Yarima

by DAGA ABBA MUHAMMAD
April 14, 2022
in Labarai
0
Alhaji Abubakar Yarima tare da marigayi Garkuwa

Alhaji Abubakar Yarima tare da marigayi Garkuwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa wani yaro mai kimanin shekaru 15 ɗan fitaccen mawaƙi Abubakar Yarima rasuwa.

Yaron, Muhammad Sani (Garkuwa), ya rasu ne da yamma a ranar Lahadi, 10 ga Afrilu, 2022, sanadiyyar shiga Kogin Kaduna da ya yi.

Alhaji Abubakar Yarima ya shaida wa mujallar Fim yadda abin ya faru, ya ce, “Bayan ruwan sama da aka yi a ranar Juma’a, 8 ga Afrilu, kasancewa ruwan shi ne na farko a Kaduna, wannan ya sa su ka tafi kamun ki fi a washegari, wanda ni da iyayen su mata ba mu sani ba. Ka san a Kinkinau mu ke da zama, kuma akwai Kogin Kaduna ta unguwar.

Marigayi Muhammad Sani (Garkuwa)

“A ranar farko an ce sun je da abokan, sun yi wanka. Shi aka ce ya shiga, sai ya ƙi shiga. Da su ka dawo sai su ka shiga maƙwabta, a nan su ka gyara kifin su da su ka kamo su ka ci. 

“An ce wata daga cikin maƙwabtan ne ta ba su dukkan abin da su ka yi amfani da shi, sai dai ni ban gamsu da maganar ba. In ma da gaske ne, ta yi kuskure. Kamata ya yi ta faɗa wa iyayen su don a tsawatar masu.”

Yarima ya ƙara da cewa, “Garkuwa shi ne ɗa na na biyar a cikin ‘ya’ya na. Saboda halin rayuwa, idan ina gida duk yadda aka yi mintuna goma ban gan shi ba sai na sa an kira mani shi, don ba na son ya na yin nisa.”

Ya ce a ranar da aka yi rasuwar ma ba ya gida. Ya ce: “Game da yadda na samu labarin lamarin, ba na gida, gwamnan Zamfara ya kira ni ya sa ni wani aiki. Da yamma aka kira ni ake ce mani wani yaro ya faɗa ruwa, ga ma rigar sa nan shi ba a gan shi ba. Na ce a siffanta mani kamannin sa. Aka faɗa mani, sai na ce shi ne.

“Na zo da kai na na shiga ruwan ban gan shi ba. Sai mu ka yi wa wasu masunta magana, su ka yi mana kwatance wasu da cewa su ke yin irin wannan binciken.

Yarima tare da Garkuwa da ƙannen sa

“Kafin mu je gare su, wasu yara su ka shiga su ka fito da shi a mace. Mu ka ɗauke shi a mota, mu ka koma gida, aka yi masa jana’iza yadda addinin Musulunci ya tanada.”

To, Allah ya jiƙan Muhammad Sani (Garkuwa), amin.

Loading

Tags: Abubakar YarimaGwamnan Zamfarakamun kifiKinkinauKogin KadunamawakaMuhammad Sani GarkuwamutuwaRiver Kaduna
Previous Post

Tsohuwar jaruma Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa

Next Post

Adam A. Zango ya yi wa aminan sa, Kochila da Sabzor kyautar motoci

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Safzor (sama, a hagu) da Zango da kuma motar da aka bayar

Adam A. Zango ya yi wa aminan sa, Kochila da Sabzor kyautar motoci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!