• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda cutar korona ta jefa Kannywood cikin bala’i

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 26, 2020
in Nijeriya
0
A sama daga hagu: Maishadda, Sani Sule da Baharu. A ƙasa: El-Mustapha da Hadiza Kabara

A sama daga hagu: Maishadda, Sani Sule da Baharu. A ƙasa: El-Mustapha da Hadiza Kabara

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
TUN bayan ɓullar cutar korona (‘coronavirus’ ko ‘COVID-19’) a Nijeriya harkokin kasuwanci su ka samu kan su a cikin wani mawuyacin hali wanda ba a taɓa ganin irin sa ba.
 
Hausawa sun ce abin da ya ci Doma ba ya barin Awai, don haka masana’antar finafinan Hausa (Kannywood) ma ta na ɗaya daga cikin sana’o’in da su ka faɗa cikin halin ha’ula’i.
 
Kannywood waje ne inda mutane sama da miliyan biyu su ke cin abinci. Annobar korona ba ta bar ‘yan fim ɗin ba, domin kuwa sun faɗa cikin mugun yanayi sakamakon tsayawa cak da harkokin kasuwancin su su ka yi. 
 
A yau babu wani abu da ya ke gudana na kasuwanci a duk cikar masana’antar da batsewar ta. Wannan ya sa ‘yan fim sun yi asarar miliyoyin nairori, kuma su na cikin zaman haƙuri, musamnan ma da aka hana kowa fita.
 
Abubakar Bashir Maishadda, wanda babban furodusa ne, ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Magana ta gaskiya, yanayin da ake ciki a masana’antar mu tun bayan da aka hana zirga-zirga, musamman ma a Kano da Abuja, abin ya jefa mu cikin wani mawuyacin yanayi tare da yin asarar da ba za ta misaltu ba.
 
“Domin idan ka duba, a yanzu babu shutin ɗin fim, babu kasuwar da za ka je ka kai, ga gidajen talbijin sun daina karɓa, ga gidajen kallo duk an rufe. 
 
“Don haka abu ne mai wahala ka iya faɗar yawan miliyoyin kuɗin da aka rasa, domin idan ka duba ko ɗan guntun fim da ake yi ana sakawa a YouTube yanzu ya tsaya saboda babu fita, gari a kulle.
 
“Haka su ma waƙoƙi, duk babu yadda za a je a ɗauka. Don haka a fili ya ke masana’antar mu ta yi asarar miliyoyin kuɗin da ba za su lissafu ba.”
 
Shi ma babban mashiryin fim, Alhaji Sani Sule Katsina, cewa ya yi, “To gaskiya masana’antar mu ta shiga wani hali, sai dai addu’a, domin idan ka duba da man kasuwancin fim ya mutu, don haka sai ‘yan dabaru.
 
“Kuma a da mu na kai finafinan gidajen talbijin, su ma su ka dakatar. Sai mu ka koma ɗorawa a ‘online’; ta nan ake samun kuɗi. To kuma da wannan koronar ta zo sai ta tsayar da komai.”
 
A hirar sa da mujallar Fim, Sani Sule ya ce: “Don haka a yanzu babu wani abu da ya ke gudana. Kowa a zaune ya ke.
 
“Don haka ka zo maganar cewar masana’antar ta yi asara ai abu ne da ya ke a fili, kowa ya na gani, domin asarar dubban miliyoyin da aka yi ba za su lissafu ba.”
 
Balarabe Murtala Baharu ya na ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a masana’antar finafinai ta Hausa. Shi ma ya bayyana wa mujallar Fim cewa: “Idan ka duba, masana’antar finafinai tun kafin wannan annobar da man ta na cikin wani yanayi, amma da annobar ta zo sai ta sake durƙusar da ita. 
 
“Don haka idan mu ka kwatanta irin asarar da aka yi a zuwan wannan cutar, za mu iya cewa an yi asarar kuɗi aƙalla miliyan ɗari.
 
“Amma in da kamar lokacin da masana’antar ta na kan ganiyar ta ne, to asarar sai ta kai ta miliyan ɗari biyar.
 
“Don haka dai masana’antar ta yi babbar asara, musamman idan aka duba yadda komai ya tsaya a wannan lokacin.”
 
Shi kuma Hamza Dogo Ɗandago, shi ne mai kula da duk wani fim da za a nuna a gidan sinima na ‘FilmHouse’ da ke cikin harabar kantunan Shoprite a Kano. Mujallar Fim ta ji ta bakin sa dangane da halin da aka shiga. A nasa bayanin, ya bayyana mana cewar: “A yanzu komai ya tsaya, ba a haska fim a sinima, don haka babu wani kuɗi da ya ke shigowa masana’antar ta sinima. 
 
“Ka ga kuwa ba ƙaramar asara masana’antar ta yi ba ta wannan ɓangaren, domin kuwa a sati idan aka haska fim, in dai babban fim ne, ana yin cinikin miliyan biyu zuwa uku; kai, wani ma har biyar ana yi. To ka ga yanzu ba a haska fim, saboda haka masana’antar ta yi babbar asara ta wannan ɓangaren. 
 
“Don haka fatan mu a nan dai Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.”
 
A ɓangaren ‘yan wasa kuwa, mujallar Fim ta ji ta bakin fitaccen jarumi Abba Al-Mustapha, wanda ya bayyana halin da ake ciki da cewa: “Mu yanzu harkar mu a tsaye ta ke, don haka babu wani abu da ya ke gudana. An tsayar da komai. 
 
“Domin harkar mu ta haɗuwar jama’a ce; duk wani abu da za a yi sai an tara jama’a, to sai ya zamo ita wannan cutar ta na hana taruwar jama’a waje ɗaya. To ka ga dole harkar fim ta tsaya saboda komai ƙanƴantar aikin da za a yi mutum ɗaya ba zai yi ba sai da wani. Don haka ina aikin zai yiwu? 
 
“A irin wannan yanayi sai dai mu yi ta ƙirga asarar da ba za ta lissafu ba, domin a gaskiya masana’antar ta faɗa cikin ƙangi na asara da ba ta taɓa samun kan ta ba a ciki. 
 
“Sai dai kawai mu yi addu’ar Allah ya kawo ƙarshen lamarin.”
 
Ita ma fitaccoyar jaruma Hadiza Kabara ga abin da ta ce: “To da man harkar fim ta tsaya ne, sai ɗan abin da ba a rasa ba. 
 
“Wannan ya sa jarumai da dama iri na mu ka koma shirin ‘Daɗin Kowa’ da ‘Kwana Casa’in’ na Arewa 24. To shi ma sakamakon wannan annobar ga shi an tsayar.
 
“Saboda haka sai dai mu yi ta addu’a Allah ya kawo mana mafita, domin halin da aka shiga a yanzu ya wuce maganar ko asarar nawa aka yi, don ba ta lissafuwa.”
 
A binciken da mujallar Fim ta yi, ta gano cewa a halin yanzu mafi yawan fim su na shan wahala wajen ciyar da kan su. Masu iyali daga cikin su sun fi tagayyara.
 
Binciken ya gano cewa da ma can yawancin ‘yan fim ba su da wata sana’a in ban da harkar fim. To yanzu da harkar ta tsaya cak saboda korona, yawanci sun shiga cikin halin ha’ula’i.
 
Wani ɗan fim da ya ce a sakaya sunan sa ya bayyana cewa akwai ‘yan fim da su ka ɗaga kadarar su domin a saya, amma babu mai saye.
 
Ya ce da yawa sun koma rancen kuɗi domin su samu su tsira da mutuncin su.
 
“Ba kowa ba ne ya tara tsabar kuɗi a banki wanda zai cira ya riƙa sayen abinci,” inji shi. “Saboda haka lamarin sai du’a’i.”
 
In da matsalar ma ta ke shi ne ba a san inda wannan abu zai tsaya ba, musamman da yake cutar koronar ƙara yaɗuwa ta ke yi, ga shi an hana kowa fita.
 
Idan aka ci gaba da tafiya a haka har tsawon wani lokaci, to yawancin ‘yan fim za su tagayyara fiye da yadda ake tsammani.

Loading

Previous Post

Adam Zango bai fahimci dokokin hukuma ba, inji Afakallahu

Next Post

Mahaifin Farfesa Abdalla ya kwanta dama

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Marigayi Dakta Muhammadu Adamu

Mahaifin Farfesa Abdalla ya kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!