ƊAN takarar zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi zama na musamman da masu shirya finafinai a Nijeriya.
Jaruman finafinan sun haɗa da na Kudu da na Arewa, wato Nollywood da Kannywood.
Ƙaramar Ministar Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ita ce ta jagoranci jaruman wajen wannan ganawa da ɗan siyasar ya yi da su.

Daga Kannywood akwai Saratu Giɗaɗo da kuma Rahama Hassan a wajen taron.
Yayin ganawar, Tinubu ya nemi haɗin kan su domin zamowar sa sabon shugaban Nijeriya a zaɓen shekarar 2023.
Idan za a iya tunawa, Tinubu ya taɓa zama gwamnan Jihar Legas a shekarun baya.
