SANIN kowa ne cewa a yau mawaƙa masu tasowa sun mamaye zukatan samari da ‘yan mata, musamman saboda yadda su ka fi maida hankali ga waƙoƙin soyayya. Wani misali shi ne yadda wata sabuwar waƙa da matashi Ali Jibril Namanjo (Namenj) rera ta ke ɗaukar sabon salo a soshiyal midiya.Sabuwar waƙar, mai taken ‘Da Ma’, na ci gaba da haska wa masoyan waƙoƙin zamani na Hausa hanya, musamman a soshiyal midiya.
Waƙar, wadda ya gayyaci mawaƙi Hamisu Breaker don ya taya shi rerawa, an sake ta ne a YouTube mako biyu da su ka gabata, kuma ya zuwa yanzu yawan waɗanda su ka kalle ta ya haura mutum 100,000.
Namenj dai ɗan asalin Ibadan da ke Jihar Oyo ne. Tsarin waƙar sa shi ne ‘Afropop’ inda ya ke ɗaukar salon juya waƙoƙin Hausa, ya sauya masu fasali zuwa na zamani kama daga na wannan lokaci har zuwa na can baya.
Mujallar Fim ta gano cewa Namenj ya fi kwaikwayon waƙoƙin fitattun mawaƙa irin su Ali Jita, Nazifi Asnanic da wasu waƙoƙin da aka yi a wasu finafinan Hausa da ma na kudancin Nijeriya da na ƙasashen waje.
‘Da Ma’ ta ci gaba da haska wa masu saurare zuciya a soshiyal midiya. Samari da ‘yan matan su na amfani da ita wajen ɗorawa a ‘status’ ɗin su don faranta wa masoyan su rai.
Ga kaɗan daga cikin wasu baitukan waƙar:
“Baby ina kwana?
Baby ina gajiya?
Shin kin tashi lafiya……?
Rabin raina.
Tabbas kin iya soyayya.
Da ma da ke na fara haɗuwa,Da na yi aure tun tuni.
Zama da ke akwai ƙaruwa, tunda ni ki na burge ni.”
Za a iya kwatanta ficen waƙar da na waƙa ‘Jarumar Mata’ ta Hamisu Breaker wadda ta samu shiga fagen nazari a jami’a, inda mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya feɗe ta.
Wata waƙar Namenj mai taken ‘Fata Na’ wadda ya sake ta a watan jiya, ita ta fito da shi a idon duniya.
