• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar El-Mu’az: Yadda ‘yan Kannywood suka ji

by MUKHTAR YAKUBU
December 5, 2024
in Labarai
0
Rasuwar El-Mu’az: Yadda ‘yan Kannywood suka ji

Marigayi El-Mu'az Muhammad Birniwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RASUWAR fuju’a da mawaƙi El-Mu’az Muhammad Birniwa ya yi a daren jiya ta girgiza ‘yan fim da mawaƙan cikin Kannywood, abin har ba a magana. Rasuwar ta ba zato ba tsammani ta sa jikin kowa a masana’antar ya yi la’asar.

‘Yan Kannywood da ma waɗanda ke wajen ta da dama sun wallafa ta’aziyyar su ga iyalai da masoyan El-Mu’az a soshiyal midiya, suna bayyana irin alhinin su. Da yawa sun yaɗa hotuna da bidiyoyin sa da ke nuna irin rayuwar sa.

Ga wasu kaɗan mun tsakuro maku:

Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa):

A madadi na da iyalai na da ɗaukacin masoya na nake miƙa wa Musulmin duniya ta’aziyyar rashin ɗan’uwa abokin aiki El-Mu’az Muhammad Birniwa, wanda ya rasu da misalin ƙarfe sha ɗaya da mintuna arba’in da ɗoriya na daren jiya Laraba da ta zo daidai da 04/12/2024.

Na shaida kyakkyawar mu’amalar sa da ta bayyana da ko waɗanne irin rukunin al’umma da suka haɗa da malaman addinin Musulunci na kowane ɓangare ba shi da gefe. Mutum ne na ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa, haka ɓangaren masu shirin fim da mawaƙa babu inda ba ya saka ƙafar sa da abin da ya shahara da shi zumunci.

Wani abu da nake tunawa na zumuncin mu da shi na ƙarshe, taron addu’ar Auwalu Garba Ɗanborno a inda har ya ba da gudunmawa ga iyalan mamacin.

Allah muna roƙon ka tare da yin tsani da salatin Annabin Ka Allahumma Salli ala Muhammad wa Ali Muhammad. Muna istigasa da ƙaunar wannan masoyi naka da neman taimakon Ka don rahama irin taka ya Allah, ka karɓi baƙuncin wannan bawa naka a cikin jinƙai irin naka da tausayi da kyustayi, Allah ka sa Aljannah ta zama masaukin sa a gobe alkiyama.

Allah ya sa zaman kabarin sa ya zamo zama a cikin dausayi daga dausayin Aljannah.

Allah ka kyautata ƙarshen mu, ka saka mu cikin ceton Manzon Allah SAW.

Yakubu M. Kumo:

Ba Rabo Da Gwani Ba…

El-Mu’az mutumin kirki ne. Ba ya gudun mutane, ba ya raina matsayin mutum, ba marowaci ba ne, mutum ne mai son zumunci, mutum ne mai tausayi, ba ya da saurin fushi, ba ya da riƙo, ba ya da girman kai, ba fasiƙi ba ne, ba ya son zalunci.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ka yi mashi rahama don girman Alƙur’ani.

Jamilu Jiddan Nafseen:

Ina cikin fili, bayan mun fara buga wasa aƙalla na mintuna talatin, na fito zan amshi ruwa. Muna gefe sai ga El-Mu’az Birniwa ya shigo. Ya tambaye ni,

“Wane ɓangare kuke?”

Na ce masa, “Ɓangaren ango”. Da zolaya ya ce, “Nafseen ba na tare da ku a yau”.

Muka yi dariya. Ya shiga fili. Muka koma tare. Bai daɗe ba ya fita. Ya ɗan yi danne-danne a waya tare da wasu al’amuran a gefe wurin masu kallo.

Can na ji an ce ya faɗi. Muka zo kan sa da sauri. Aka yi asibiti. Ashe mutuwar kenan!

Mun ji mutuwa! Allah ya gafarta maka, Chairman.

Nazir Adam Salih:

Duk inda kuka haɗu da shi a haka yake, cikin murmushi kamar gonar auduga. Idan yau kuka haɗu da El-Mu’az a karo na farko zai karɓe ka kamar kun yi shekara guda. Idan kuka sake haɗuwa da shi a karo na biyu kuwa, sai ka rantse da Allah tun kuna yara tare kuka tashi da shi.

Ka jima ba ka sami mutum mai kyauta da karamci da faran-faran kamar sa ba. Ba ko shakka, mun yi babban rashi, za mu jima muna tuna shi da halin sa na ƙwarai.

El-Mu’az, halin ka na ƙwarai ya bi ka, Allah ya jiƙan mutumin kirki.

 Rabi’u Dalle

Tabbas, na ji mutuwar nan. Wa inna ilaihir raji’un.

Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare ka aboki na El-Mu’az Birniwa.

Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un.

Ana yi wa gawar mamacin sallah kafin a kai shi maƙabarta
Dandazon mutane a maƙabarta

Nasir Nid:

Aboki na El-Mu’az Birniwa Allah ya jiƙan ka da rahama, ya sa mutuwa hutu ne a gare ka.

 Bilkisu Yusuf Ali:

Gaskiya na kaɗu da jin rasuwar mawaƙi El-Mu’az U Birniwa. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Duniyar nan zancen banza ce fa!

Allah ka gafarta masa. Allah ka shafe kurakuran sa. Allah ka ba mu guzirin tarar da su. Allah ka gafarta mana, amin.

Fauziyya D. Sulaiman:

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Kai na ji mutuwar El-Mu’az Birniwa.

Ya Allah ka gafarta masa. Allah ka jiƙan bawan ka. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!

 Hauwa Edita:

La ilaha ilallah, Muhammadur rasulallah! Sallallahu alaihi wa salam. Inna lillah wa inna ilaihir raji’un, la haula wa la ƙuwwata illa billahi aliyul Azeem!

Duniya ba a bakin komi muke ba.

Allah ya gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomar mu baki ɗaya. Babban rashi, tabbas mun yi babban rashin ɗan’uwa, amini.

Amina Auta:

Rayuwa kenan. Shekara ɗaya da ta wuce, ƙarshen gani na da shi kenan a Abuja na je aiki.

Inda na hango shi gurin da na je cin abinci. Ina ta da niyyar in karasa mu gaisa amma a lokacin, wani abin ya ɗauke min hankali.

Sai bayan na koma gida ne masa magana online na ce, “Yaya na na gan ka gurin cin abinci ina niyyar in ƙaraso mu gaisa.”

Ya amsa min da cewa, “Ba komai ƙanwa ta. Aiki kika zo?” Na amsa masa, “E wallahi.”

Ya ce, “To, Allah ya taimaka na gode da kulawa.

Hakika shi din mutumin kirki ne wlh, na ji mutuwar nan sosai Allah yasa ka huta.

Abdul Amart Mohammed:

Inna lillahi ma akhaza wa lahu ma aadaa wa kulli shai’in indahu bi’ajalin musammaa. Allahum maghfir lahu Allahuma arhamhu. Allahumma sabbithu.

Allah yarham El-Mu’az Birniwa.

Ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani, yana yi wa iyalan El-Mu’az gaisuwa a yau

Loading

Tags: El-Muaz Birniwamawakamutuwarasuwata'aziyya
Previous Post

Ɗimbin jama’a suka halarci jana’izar El-Mu’az wanda ya rasu sanadiyyar bugun zuciya

Next Post

Furodusa a Kannywood, Musty Fashion ya yi rashin mahaifi

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Furodusa a Kannywood, Musty Fashion ya yi rashin mahaifi

Furodusa a Kannywood, Musty Fashion ya yi rashin mahaifi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!