A KULLUM Kannywood cika ta ke ƙara yi ta da tumbatsa da sababbin jarumai, musamman mata. Yanzu haka a Kaduna an samu sabuwar jaruma, kyakkyawa, son kowa ƙin wanda ya rasa.
Fatima Sa’idu, wadda aka fi kira da Fanan Buzuwa, yarinya ce mai ƙarancin shekaru, ga ta da ladabi da biyayya ga na gaba da ita, ga ta fara, matsakaiciya. Ta na ɗaya daga cikin jarumai mata da tauraruwar su ta fara haskawa a wannan lokaci. Sai dai kuma ta bambanta da sauran jarumai mata ‘yan’uwan ta, domin ban da fim, ta na kasuwanci, kuma malamar asibiti ce.
Mujallar Fim ta zanta da Fanan inda ta feɗe mana biri har wutsiya a game da yadda ta shigo harkar fim, da sauran su, kamar haka:
FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ki a taƙaice.
FANAN: To, ni dai suna na Fatima Sa’idu, amma an fi sani na da Fanan Buzuwa. An haife ni a Malali, Kaduna, amma na girma a Badarawa, yanzu kuma ina zaune a Unguwar Rimi.
Na fara ƙaramin ajin yara a Malali, na firamare na a Badarawa, sannan na yi sakandare na a Unguwar Rimi.
FIM: Wace ƙabila ce ke?
FANAN: Ni Buzuwa ce. Baban mu Buzu ne, mahaifiya ta kuma ‘yar Jigawa ce.
FIM: Me ya ba ki sha’awar shiga harkar fim?
FANAN: Gaskiya tun ina makaranta a firamare haka idan ana abubuwan al’adu, abin na burge ni, sai ta kai na fara son in yi fim. Idan ina kallon fim sai in ce da a ce ni ce na ke yin haka zan yi farin ciki sosai.
FIM: Ta wace hanya ki ka bi don ganin kin samu shiga masana’antar?
FANAN: Gaskiya ni hanyar da na bi shi ne da na gama makarantar sakandare ɗi na, ina son fim, amma kuma ina so in zama ‘yar jarida. Buri na shi ne in zama ‘yar jarida ko likita. Sai aka kai ga matakin da kawai da akwai wata ƙawa ta, Najma, ita ta na yin fim, irin in mu ka je lokeshin da sauran ƙawaye na ‘yan fim haka, in su na yin abubuwan su sai in ga abin na burge ni, amma ina jin tsoron in faɗa a gida; idan na faɗa a gida ta yaya za a yarda da cewa in yi, don baba na ba shi da burin ya ga a cikin ‘ya’yan sa akwai wadda ta zama mai aikin asibiti, ni kuma ina da burin zama ‘yar jarida. Ni kuma a lokacin ban yi jarabawar kammala sakandare ba ballantana in nemi gurbin karatu a makarantar gaba da sakandare. A lokacin sai na yi tunanin in je in samu Daddy in faɗa masa, amma ina jin tsoro ta yaya zai yarda, kuma ba na son abin da zai ɓata masa rai. Sai na zo na same shi na ce yanzu kamar a ce na zama, sai ya ce shi ba shi da burin da ya wuce in zama likita. Ba a yi sati biyu ba, na je na nemi ‘admission’ a makarantar koyon aikin asibiti ta Funtuwa, na je na karɓo komai da komai. Mu na zaune da shi kawai na ce masa ga shi zan fara makaranta. Sai na ga ya ji daɗi sosai. Sai na yi tunanin idan na zo masa da tawa buƙatar nan gaba zai amince min.
To a daidai wannan lokacin ina yin karatu, sai na fara yin waƙa, na yi bidiyon waƙa guda biyu, sai kuma na ga karatu ba zai yiwu ba ina harkar kuma ina waƙa, sai na ci gaba da karatu na. Da na yi jarabawar ƙarshe sai na fara komawa ina so in yi fim, na kuma kira na aiki tunda da ma na san mutane. Haka dai ina asibiti in na tashi aiki, in ina da wani aikin fim sai in wuce. Yadda aka yi kenan.
FIM: Wanene ubangidan ki?
FANAN (dariya): ubanningida na ai su na da yawa.
FIM: Ma’ana wanda ya kawo ki harkar ko kuma ya fara saka ki a fim.
FANAN: A gaskiya na san ina zuwa Shareef Studio, na san su sosai. Wata rana Abdul M. Shareef ya na zaune a ofis, sai wani Khaleed ya ce in je mu gaisa da oga. Ina zuwa mu ka gaisa, sai ya ce masa, “Ai ita ma jaruma ce.” Sai ya ce in nuna masa ayyukan da na taɓa yi. Na nuna masa a waya ta, na kuma shiga YouTube na nuna masa wasu, sai ya ce ba damuwa, mu yi musayar lambar waya. Na tura masa hotuna na. Shi kenan, su ma su ka fara kira na aiki. Ba mu daɗe da yin magana da shi ba sai ya kira ni aikin fim ɗin sa, ‘Da Za Ki So’.
FIM: Zuwa yanzu kin yi finafinai za su kai kamar nawa?
FANAN: Gaskiya za su kai takwas ko goma.
FIM: Za ki iya tuna sunayen wasu daga ciki?
FANAN: Gaskiya na manta sunan wasu, amma akwai ‘Ni Da Iyali Na’, ‘Sanadin Ki Ne’, ‘Duk Mata Ne’, ‘Da Za Ki So Ni’, da sauran su.
FIM: Ya batun kan-ta-waye?
FANAN: Gaskiya ana yi, ba zan ce ba a yi ba, saboda ina jin labari a wurin wasu in an zauna, amma dai ni ba a yi min ba, don na riga na san su tun lokacin da na ke raka ƙawaye na lokeshin su ke ce min in gwada ni ma zan iya.
FIM: Ko kin fuskanci ƙalubale bayan shigowar ki masana’antar?
FANAN: Gaskiya ni ba ƙalubalen da na fuskanta na damuwa tsakani na da wasu.
FIM: Ɓangaren nasarori kuma fa?
FANAN: Nasarorin da na samu, da ma ka ga kamar Abdul ya na burge ni tun can asali, sai kuma irin yadda mu ka yi magana da shi bai sa na karaya ba, ya ƙarfafa min gwiwa a kan cewa in ɗauki abin a matsayin sana’a ne. Duk irin wannan nasara ne. Na san irin su Jamil Nafseen, Najib Marubuci, duk su na kira na aiki. Duk nasarori ne.
FIM: Yawancin sababbin jarumai ire-iren ku a yanzu sun fi maida hankali a kan bidiyon waƙoƙi maimakon fim. Ke a ɓangaren ki, wanne ya fi kwanta miki a rai?
FANAN: Ni duka ina so. Amma fim abin da ya sa na fi son shi, ana shan wahala, amma bai kai bidiyon waƙa wahala ba.
FIM: Menene burin ki game da wannan sana’a?
FANAN: Buri na in zama fitacciyar jaruma sosai, irin duk inda na je a riƙa nuna an san ni. Zan ji daɗin haka sosai.
FIM: Wace jaruma ce ki ke son ki zama kamar ta?
FANAN: Nafisa Abdullahi.
FIM: Wane jarumi ki ka fi so ki ga an haɗa ki aiki da shi?
FANAN: Ba ni da zaɓi, domin zan iya aiki da kowa. Saboda ina da ‘confidence’ (dariya).
FIM: Kin taɓa aure?
FANAN: Ban taɓa aure ba.
FIM: Idan aure ya zo maki a yanzu a matsayin ki na sabuwar jaruma da ke son cimma burin ta na zama kamar Nafisa Abdullahi, za ki yi auren ki bar burin naki?
FANAN: E, zan aje harkar fim in yi aure. Amma yanzu wanda na ke tare da su su na ganin cewa yadda na ke son fim ba zan iya yin aure ba.
FIM: Ki na da burin yin fim a Nollywood?
FANAN: Sosai, domin ya na burge ni. Amma kuma ba na tunanin zan iya yi. Matsala ɗaya ce, shigar da su ke yi ba irin tamu ba ce. Wannan dalilin ne ya sa ba zan iya ba.
FIM: Wanene saurayin ki a Kannywood?
FANAN: Saurayi kuma? Ba ni da saurayi a masana’antar nan.
FIM: Za ki iya auren ɗan fim?
FANAN: Da kamar wuya.
FIM: Ki na ‘yar fim, amma ba za ki iya auren ɗan fim ba, mecece illar hakan?
FANAN: Babu wata illa, amma a yanzu dai ba na jin zan iya auren ɗan fim.
FIM: Ba ki ganin cewa mutanen gari za su ce ke ma ki na gudun ɗan fim, ballantana su?
FANAN: Abin na ba ni sha’awa in ga ana auren juna, amma ni dai a’a.
FIM: Mecece shawarar ki ga abokan sana’ar ki?
FANAN: Shawara ta ita ce kada su ce fim kawai za su riƙe a matsayin sana’a, su yi ƙoƙari su haɗa da kasuwanci, sannan kuma da karatu domin karatu na da matuƙar muhimmanci a rayuwa. Ka ga kamar ni ina fim ina kasuwanci, sannan ga karatu na yi, nan gaba aikin asibiti zan kama.
Don Allah, ‘yan’uwa, kada mu ga cewa mun yi suna, mu riƙe fim kawai a matsayin sana’a, mu haɗa da wata sana’ar.
FIM: Menene saƙon ki ga masoyan ki?
FANAN: Ina yi masu fatan alheri da basarori a rayuwar kowa, kuma kowa Allah ya cika masa burin sa na abin da ya ke so ya zama.
FIM: Mun gode Fanan.
FANAN: Ni ma na gode Malam Abba.