ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa matashin jarumi a Kannywood kuma mamallakin shafin ‘Kannywood Celebrities’, Malam Abdoulfatah Omar, rasuwa.
Allah ya karɓi ran sa a yau Laraba da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, Jihar Kaduna, bayan gajeruwar jinya.
Marigayin mai kimanin shekara 30 a duniya ya rasu ya bar iyayen sa da matar sa da ‘ya ɗaya, wato Ilham.
An yi jana’izar sa da ƙarfe 2:30 na rana a filin ƙwallo na layin su, wato Titin Mora, a Tudun Wada, Zariya.
‘Yan fim da suka halarci jana’izar sun haɗa da Mukhtar SS, Salisu Ɗan Sanda da Yahaya Rayyan.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ‘yan fim sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah, suka yi ta ɗora hotunan sa suna yi masa addu’ar neman gafarar Allah.
Abdoulfatah yana ɗaya daga cikin matasan da suka yi kyakkyawar mu’amala da Manajan Daraktan Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu.
Allah ya jiƙan sa, ya albarkaci abin da ya bari, amin.
