A GOBE Juma’a ‘ya’yan masana’antar shirya finafinan Hausa za su yi wani babban taro domin yin addu’o’i ga ‘yan’uwan su ‘yan fim da su ka rasu.
A sanarwar da ɗaya daga cikin jagororin masana’antar, Alhaji Mohammed Kabiru Maikaba, ya fitar a yau a madadin Gidauniyar Kannywood, ya bayyana cewa ban da ‘yan fim da iyayen su da su ka rasu, za a kuma yi addu’a ga manyan mutanen jihar da su ka riga mu gidan gaskiya.
A sanarwar, wadda mujallar Fim ta gani, fitaccen jarumin ya ce, “A madadin Kannywood Foundation Communications & Media Team, ina mai farin cikin gayyatar ka/ki izuwa gagarimin taron addu’o’i da za a yi wa ‘yan’uwa ‘yan wannan masana’anta da Allah ya yi wa rasuwa, da gwarazan mutanen da wannan jiha tai rashi, da iyayen mu da su ka riga mu gidan gaskiya.”
Ya ce za a yi taron ne a ranar Juma’a, 14 ga Janairu, 2022 da ƙarfe 3:00 na yamma a harabar Social Welfare da ke Court Road, Gyaɗi- Gyaɗi, Kano.
Ya yi nuni da cewa halartar ‘ya’yan masana’antar ta Kannywood wannan taro “ya na da matuƙar muhimmanci.”
Idan an tuna, a wani rahoto da mujallar Fim ta wallafa a ranar 31 ga Disamba, 2021, an nuna cewa manyan ‘yan fim da dama sun rasu a shekarar, sannan wasu kuma sun rasa iyayen su.
Rahoton ya ce ‘yan Kannywood da su ka rasu a 2021 sun haɗa da Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina (Kasagi), Alhaji Yusuf Barau, Alhaji Sani Ciyaman Ɗangiwa, Malam Ahmad Tage, da Alhaji Ibrahim Mu’azzam.
Akwai kuma Alhaji Isyaku Forest Sani Garba SK, Hajiya Zainab Musa Booth, Hajiya Umma Ali, Khadija Abubakar Mahmud da Rabi’atu S. Haruna.
Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa iyayen membobin Kannywood da su ka rasu sun haɗa da Alhaji Isa Jibril Kibiya (mahaifin Ali Isah Jita), Alhaji Muhammadu Sani Zangon Daura (mahaifin Asma’u Sani), da Alhaji Jibrin Giɗaɗo (mahaifin Maryam Jibrin Giɗaɗo).
Akwai kuma Hajiya Bilkisu Sharif Adam (mahaifiyar Aminu Ala), da Hajiya Hauwa S.U. Garba (mahaifiyar Fati S.U. Garba).