• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yanzu masu kallo sun fara bambance finafinan Hausa da za su kalla – Alhaji Sheshe

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 15, 2022
in Labarai
0
Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe)

Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN furodusa a Kannywood, Mustapha Ahmad, wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe, ya ce sauyin zamani da aka samu a duniyar fim shi ne ya kai su ga sauya akalar aikin su zuwa aiki mai nagarta domin a yi tafiya irin yadda ake gudanar da harkar kasuwancin fim a duniya. 

Ya ce hakan ne ma ya sa su ka shirya fim ɗin ‘Hikima’ wanda ya ke ɗauke da labari mai ban al’ajabi.

A tattaunawar da ya yi da mujallar Fim, Alhaji Sheshe ya yi tsokaci kan tsawon lokacin da fim ɗin ya ɗauka ba tare da an sake shi ba, ya ce: “To shi da man wannan fim ɗin mun yi shi da wata manufa, don haka ne ma aka ga ba mu sake shi da wuri ba. Manufar kuma ita ce mu na son finafinan Kannywwod su riƙa shiga wasu manhajoji da su ke ‘international’, irin su Amazon da sauran su. Don haka duk fim ɗin da aka yi shi da irin wannan manufa, to za ka bi wasu hanyoyi domin ka ga ka cimma nasara. 

“To ƙoƙarin bin waɗannan hanyoyin ne ya sa har mutane su ke ganin mun ɗauki dogon lokaci ba mu sake shi ba. Kuma ga shi Allah ya kawo mu lokacin da a yanzu aka fara kallon sa a sinima, kuma da yardar Allah a yanzu mu na nan daf da kaiwa ga matakin da mu ke nufi.

“Amma dai a yanzu mu na gaɓar farko ta nuna shi a sinima a kalle shi don a ga irin aikin da mu ka yi.”

Furodusan ya ci gaba da cewa, “Duba da yadda aikin fim ya koma a duniya, shi ya sa mu ka tsaya mu ka tsara fim wanda zai iya zuwa ko’ina a duniya. Don haka duk da cewar fim ɗin Bahaushen fim ne, amma ba fim wanda shi Bahaushe ya saba kallo ba, don haka mun zo da wasu abubuwan da ba a saba ganin su ba wanda duk wanda ya kalla zai san cewar lallai an fara samun sauyi a cikin harkar finafinan Kannywood.”

Da mujallar Fim ta tambaye shi dangane da irin kuɗin da aka kashe wajen aikin fim ɗin, ko kwalliya za ta biya kuɗin sabulu kuwa, sai ya ce, “Gaskiya tun yanzu ma ta biya domin mu na son mu kai masana’antar Kannywood wani mataki ne. To ko a yanzu za mu iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu. 

“Don haka sai dai burin mu na gaba, wanda kuma babban burin mu shi ne mu ɗora ita masana’antar a harkar kasuwancin da ta fi ta yanzu. Kuma mu na fatan haƙar mu za ta cimma ruwa, don haka mu ke fatan abokan sana’ar mu masu shirya finafinan Hausa su yi koyi da abin da mu ka yi. 

“Kuma za mu so su yi wanda ya fi namu ma, saboda mu na son duka a gudu tare a tsira tare.”

Alhaji Sheshe ya yi kira ga masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin Kannywood da su daure su yi abin da ya kamata domin a samu a kai inda ake so a kai.

Loading

Tags: Alhaji ShesheFinafinaifurodusaHikimaKannywoodMustapha Ahmadsinima
Previous Post

Da an gan ni an san na mori miji – jarumar Kannywood Muhibbat

Next Post

Zargin ina nuna wariya ko na gaza yin aiki ba gaskiya ba ne – Minista Sadiya

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq ta na raba kayan tallafi ga mata a Dutse, Jihar Jigawa, a makon jiya

Zargin ina nuna wariya ko na gaza yin aiki ba gaskiya ba ne - Minista Sadiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!