• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yartsana: Ninƙaya cikin kogin karuwanci

by DAGA AMINA HASSAN ABDULSALAM (AHA)
September 29, 2021
in Marubuta
1
Littafin 'Yartsana da marubuci Ibrahim Sheme

Littafin 'Yartsana da marubuci Ibrahim Sheme

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MARUBUCI: Ibrahim Sheme
SHEKARA: 2003. An ƙara bugawa a 2007 da 2016
KAMFANIN WALLAFA: Informart Publishers Ltd., Kaduna
ISBN: 978-35786-5-0
SHAFUKA: 270
ƊAB’I: De Young Printers, Kaduna

IDAN ka cire sunan marubucin, za ka zaci wata riƙaƙƙiya, shahararriya kuma gogaggiyar tsohuwar karuwa ce ta rubuta labarin ”Yartsana’, domin za a lula da kai wani zamani da karuwai su ke cin karen su ba babbaka, karuwanci irin na zamanin da, yadda rayuwar karuwa take, da sababbin harkar da maneman su da makomar su da ribar su in ma akwai da kuma asarar rayuwar su.Ba komai ne ya sa haka ba illa bincike mai zurfi wanda aka lulluɓe da basirar iya kwararo labari tare da kanannaɗe makaranci cikin shafukan littafin. Jigon littafin ya kasance karuwanci.

KARUWANCI
A shekarun baya, ƙarshen zagi ko ƙasƙanci ga ‘ya mace shi ne ka ce mata karuwa. Ko waye kai sai dai hukuma ta raba ku, musamman ma idan matar aure ce. Karuwar ce kaɗai za ka zaga da kalmar ka kwana lafiya kuma ba za ta damu ba.

Wacece karuwa? Karuwa ita ce matar da ta ke amfani da jarin jikin ta wajen biya wa mazan banza buƙatar su ta jaraba ko sha’awa, su kuma su biya ta kuɗi. Masu wannan harka sun ɗauke ta sana’a. Karuwa ita ce matar da take kwana da maza don su biya ta kuɗi.

ZAINAB (ASABE)

Littafin ”Yartsana’ labari ne a kan wata yarinya mai suna Zainab wacce ta rasa auren saurayin ta wanda ta ke so sakamakon auren dole da mahaifin ta ya yi mata da wani ɗan’uwan ta. Saboda ƙiyayya, Zainab ba ta yarda sun yi kwanciyar aure ba har na tsawon wani lokaci, a ƙarshe ta yi yaji, uban ta ya hana ta zama a gidan sa, sai gidan kakar ta ta koma da igiyar aure a kan ta. 

Kwatsam! sai juna biyu ya bayyana a gare ta alhalin ita da mijin nata ba su gudanar da sunnar aure ba. Da zaman garin ya ƙi daɗi sai ta bar ɗan ta, ta gudu ta fantsama duniya, ta shiga karuwanci da sabon sunan Asabe.

A zamanin da, yawancin yara mata kan auka harkar karuwancin ne saboda auren dole da ake yi musu, tare da gudunmuwar iyaye, da malaman addini da mahukunta da ma sauran mutane daga fannonin rayuwar al’umma. 

Bari mu sharara gudu cikin littafin mu ga me ya auku. 

‘YAN DUNIYA

Kafin nan ga sunayen wasu daga cikin taurarin littafin, wasu sunaye ne da ‘yan bariki ke sanya wa kan su ko a sanya musu.

Zainab (Asabe), Abu Maijigida, Lado Acibilis, Tijjani Ahmed, Magajiya Dije, Bebi Sai-Tumoro, Halidubu Mai Kan Tasa, Gambo Ruwan-Abarba, Gaje Tatsula, Audu Dara, Indo Ƙayar-kifi (“Ba haɗiyar yaro ba!”), Hajiya Binta Suga, Indon Bichi (“‘Yar gajerar gwanda mai hana yaro barci!”), Fati Gidauniya, Alhaji Maidogonsoro, Bart Ike, Basiru, Bilkisu ‘Yarguguwa, Lawai Maiɗanmaciji, Tahir, Manjo, Tawurno, Malam Tukur, ds.

MUGAYE UKU

i) Malam Tukur:
Duk da cewa ya taɓa ce wa matar sa ba zai bari ‘yar sa ta auri Tijjani Ahmed ba, amma bai taɓa kiran Tijjanin ya gaya masa ga-da-ga ba, ya bari soyayyar tasu ta yi nisa ta yi ƙarfi. Ba shi da ƙwaƙƙwaran dalilin hana auren, kawai kamar yadda ya ce, dalili nasa ne “ba don ban ƙaunar sa ba, a’a sai don shi ba ɗan zuri’ar mu ba ne, mu kuwa Fulanin asali ba mu son mu ba bare ‘yar mu aure ko mu auro ɗiyar bare” (shafi na 44).

ii) Kandala:
Kakar Zainab kenan. Duk da cewa ita kaɗai ce a dangi ta goyi bayan Zainab na ƙin auren dole, amma daga baya ta tafka babban kuskure da ta bari da igiyar auren Zainab ta dinga kula Alhaji Maidogonsoro.

Hasali ma ita ta ƙarfafa mata gwiwa da ta dinga karɓar kyaututtukan sa.

iii) Alhaji Maidogonsoro:
Irin tsofaffin nan ne masu kuɗi da suke yaudarar ƙananan yara su ɓata su, su kuma wurgar da su. Ya fi ga ‘yanmata da matan aure. 

NAGARI DA ƁATATTU

Karuwa ita ke ɗauke da abin kunyar da ta ke yi, ita ake ƙyama ita a ke kyara, wata ma ko ta tuba da ƙyar ake samun mai auren ta saboda kowa ya na tunanin ta zama motar da kowanne matuƙi ya yi irin tuƙin da ya ga dama a kan ta, kowa ya zuba mata irin ƙazantar sa. 

Bahaushe na cewa duk abin da namiji ya yi ado ne, tsohon ɗan bariki na iya neman natsattsiyar budurwa a kuma ba shi ba tare da an yi bitar karatun baya ba. Amma a wajen kamashon alhaki ba mace ba namiji, idan ko Bahaushe zai ci gaba da riƙe wancan karin magana, ashe kenan maza za su ci gaba da tafka tsiyar su da tunanin al’umma za ta tsarkake su a duk lokacin da buƙatar hakan ta zo. 

Kusan a kowanne fanni na rayuwa akwai ɓatattu waɗanda su ke kamar awakai a cikin fatun kuraye, kamar yadda za mu gani a wasu shafuka na wannan littafi. Su kuma mutane ne waɗanda ba sa yawo gidajen karuwai amma idan sun samu sarari ko dama sai su yi amfani da shi wajen fidda maitar su a fili. 

i) Malamin asibiti:
Malam Ɗahe ya latsa Zainab (Asabe) lokacin da ta kai Bebi Sai-Tumoro asibiti san da ita Bebin suka yi faɗa da Maijigida ta kusan cizge mata kan nono da cizo (shafi na 61).

Idan mu ka kwatanta da abin da ke faruwa cikin al’umma mun san cewa akwai likitocin da ke karya dokar aiki su nemi marasa lafiyar su, ko malaman makaranta da ke neman ɗaliban su ta qarfi da yaji.

ii) Maigadi – a filin asibiti inda Asabe da Bebi ke zama su huta, tsoho da shi ya zo ya latsa Bebi ya ce wai ta ba shi ko minti goma ne a ɗakin sa. Da ta ƙi sai ya juya ga Asabe (shafi na 62).

Wannan ya na nuni da irin tsofaffin da ba su san Annabi ya faku ba; maimakon istigifari, sai ma abin da ya ƙaru.

iii) Maigari:
An ambace shi da baduniyi (shafi na 66). 

Daga masu unguwanni da masu gari ba inda ba ‘yan duniya.

iv) Dakta Ado:
Mai asibitin ‘Ba-Damuwa Clinic’ wanda zai cire wa Asabe ciki, ba ta ankara ba sai ga shi ya yi zindir. Wato sai da ya yi amfani da ita kafin ya yi mata aikin, wai kuma kafin nan shi ya gama yi wa wata yarinya nasiha a kan bin maza! (shafi na 109).

v) Difi’o: 
D.P.O. san da aka yi kamen karuwai aka kai su caji ofis sakamakon hana karuwanci da aka yi, sai Difi’o ya zubar da ƙimar kayan ɗamarar sa ya ce ya na son Asabe. Ta ce masa ita ma ta na son sa, to amma babu yadda za ta yi tunda an hana karuwanci.

Ga amsar da ya ba ta: “Haba, duk da haka akwai gidan da zan ajiye ki. Ai karuwai suna da ɗaurin gindi a nan qasar. Ke dai ki amince kawai da ni, kuma zan kula da ke da kyau.”

Kamar yadda mu ka sani ne cewa masu dokar barci ke ɓigewa da gyangyaɗi, sai ka ga wasu jami’an tsaro sun kama masu sayar da kayan maye, amma su amshe su sha. 

Ko wasu daga cikin ‘yan sanda su tsare mace a bisa wani dalili, sai a samu wasu bara-gurbi su nemi keta mata haddi, da sauran su.

AUKAWAR ZAINAB KARUWANC:

Sa’ilin da ta je Tashar Kuka a Kano don ta hau mota, a nan ta ga wani mai tallar magani, Alhaji Kabiru Ba- ka-kwana-da-wando. A labarin haka ya na mana nuni da abu uku: 

i) Fifikon jima’i a rayuwar malam Bahaushe. A kan jima’i ko rashin sa ma’aurata na iya zuwa kotu don neman haƙƙin su. Za a gane hakan da irin kalaman da ya ke amfani da su wajen tallata maganin nasa (shafi na 6).

ii) Mutumin nan wani mahaɗi ne na yadda qarshen Zainab zai kasance amma mai karatu ba zai san da haka ba sai ya iso wajen.

iii) Ga shi dai a zahiri maganin ƙarfin maza ya ke sayarwa, amma a ƙarshen labarin, da Asabe ta nemi maganin cutar da ya san ba shi da shi sai ya amshi kuxin ta ganin cewa ta zo gaɓar nan ta mai neman tsira ko takobi aka miqa masa zai kama.

iv) Ta hau mota ta haɗu da wani direba wanda ya yi mata alƙawarin taimaka mata amma sai ya zarce da ita wani gida ya ajiye ta, ya dinga amfani da ita tamkar matar sa, daga baya ta gudu daga gidan. 

TARON BARA-GURBI

A ƙarshe, kowanne lungu da saƙo ka shiga akwai ɗan iska, akwai ɓatattu, akwai bara-gurbi. Iskancin wasu ya fi na wasu, wasu su yi a ɓoye, wasu kuma a fili, amma a ƙarshe marubucin ya yi nuni da cewa in wani ya yi rawa ya sha liƙin kuɗi wani kuwa idan ya yi zai ci na jaki kamar yadda duniya ta yi ƙuli-ƙulin Kubura da Zainab sannan ta ɗaga ta sama kana ta maka ta da ƙasa, amma ta yi wa Bebi Sai-Tumoro liƙin bazata.

YABO

Marubucin ya yi namijin ƙoƙarin fiddo da zahirin rayuwar karuwanci da karuwai da darussan da ke cikin yi wa rayuwa riqon sakainar kashi da kuma uwa-uba gudunmawar muhimman mutane wajen lalacewar mutum ko mutane a al’umma.

‘Yan kurakuran da na ci karo da su ba su taka kara sun karya ba, shi ya sa ban bi ta kan su ba.

*Amina Hassan Abdussalam (AHA) fitacciyar marubuciya ce da ke zaune a Kano

Loading

Tags: Adabin HausaAmina Hassan Abdulsalam AHAHausa novelsIbrahim ShemeInformart Publisherskaruwancilittattafan HausaYartsana
Previous Post

MOPPAN ta fitar da ƙa’idojin tsayawa takara

Next Post

Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Charles Henry Robinson a cikin shigar Hausawa

Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Comments 1

  1. Asma'u bature. says:
    4 years ago

    Allah ya shirya masu hali irin na zaenab ya shirya al’umma annabi gaba daya, da iyayen da ke jawa ya’yan su irin wannan rayuwar Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!