• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 22, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: APC tantagaryar mayaudara ne, inji Atiku

by DAGA WAKILIN MU
January 28, 2023
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar a Abakaliki

Atiku Abubakar a Abakaliki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake nanata ƙudirin sa na rage wa Gwamnatin Tarayya ƙarfin iko tare da sauya fasalin ƙasar nan idan ya ci zaɓe.

Haka kuma ya zargi jam’iyyar APC da ke mulki da cewar ta ƙi cika alƙawarin da ta yi na sauya fasalin ƙasar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan maganar ne a dandalin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki, Jihar Ebonyi, lokacin da ya je can yaƙin neman zaɓe.

Atiku ya ce ‘yan ƙabilar Ibo sun sha yin kira da a sauya fasalin ƙasa (wato ‘restructuring’ a turance) domin su magance matsalolin da ke addabar yankin su, don haka ya ce sauya fasalin ƙasa na daga cikin manyan ƙudirorin da zai sa a gaba idan ya kafa gwamnati a matsayin shugaban Nijeriya.

Ya yi iƙirarin cewa ita  APC ta gaza wajen cika alƙawarin da ta yi na sauya fasalin ƙasa, ya ce ya na kira ga al’ummar Ibo da ke Jihar Ebonyi da su yi watsi da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi. 

Atiku ya samu babbar tarba a filin wasan inda ɗimbin jama’a su ka taru domin su saurare shi.

Ɗan takarar ya gode wa jama’ar jihar saboda goyon bayan da su ke ba PDP tun da aka kafa ta a cikin 1999.

Atiku ya na amsa gaisuwar masoyan sa a taron Abakaliki

Ya ce: “Na ƙudiri aniyar sakar wa matakan gwamnati da ke ƙasan Gwamnatin Tarayya ƙarfin iko da kuma sauya fasalin ƙasar nan; al’ummar yankin Kudu-maso-gabas sun daɗe su na ƙawazuci tare da yekuwar a sauya fasalin ƙasa saboda su na so su samu ƙarin ƙarfin iko da ƙarin kuɗi domin magance matsalolin da ke damun su.

“Mun amince da hakan kuma wannan ne ya sa hakan zai kasance wani babban ginshiƙi na gwamnatin mu. Saboda haka, ku ba mu goyon baya har ku ka ba mu damar zama shugaban ƙasa na gaba.”

Ya ƙara da cewa, “APC sun yi maku irin wannan alƙawarin. Shin amma sun yi? Sai su ka yi watsi da wannan batun na sauya fasalin ƙasa. Jam’iyyar su ta manyan ‘yan yaudara ce, kuma haɗakar su ta tantagaryar yaudara ce.

“Mun ƙudiri aniya kuma gaskiya ce mu ke faɗa, don haka idan ku ka ba mu goyon baya, za mu aiwatar da alƙawarin da mu ka ɗauka.”

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, zai kara da Atiku Abubakar na PDP a babban zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.

Loading

Tags: 2023 electionsAbakalikiAPCAtiku AbubakarBola Ahmed TinubuPDPrestructuring
Previous Post

Yadda ɗaurin aure da taron bikin jarumin Kannywood Abale ya gudana

Next Post

‘Yan sanda sun kama jarumar Kannywood Murja Kunya

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Murja Ibrahim Kunya

'Yan sanda sun kama jarumar Kannywood Murja Kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!