HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fayyace wa kafafen yaɗa labarai dokoki da ƙa’idojin bai wa jam’iyyun siyasa lokuta daidai da juna a yayin ba da labaran kamfen.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi masu wannan bayani dalla-dalla, lokacin da ya ke jawabi wajen taron ƙara wa kafafen yaɗa labarai na talbijin da rediyo ilmin sanin makamar yayata jam’iyyun siyasa a yayin kamfen.
An shirya taron ne a cikin makon nan a Abuja domin ƙara ɗora su kan hanyoyin da doka ta tanadar wajen tabbatar da bin ƙa’ida yayin yaƙin neman zaɓen 2023.
A ranar 28 ga Satumba ne INEC ta amince aka fara kamfen, kamar yadda Sashe na 94 (1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.
Ya ce: “Yayin da za a fara yaƙin neman zaɓen 2023, ya na da muhimmanci dukkan jam’iyyu, ‘yan takara, magoya bayan su da kafafen yaɗa labarai su sani cewa su na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen tabbatar da an gudanar da komai bisa yadda doka ta gindaya.
“Kada a riƙa yayata kalaman ƙiyayya, zage-zage, sakin baki, kalaman tunzura jama’a ko harzuƙa wani ɗan takara, aibantawa ko muzantawa, cin zarafi, lahanta wani ko lalata kayan kamfen ɗin wata jam’iyya.
“Sashe na 95 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya fayyace komai dangane da ƙa’idojin da ba a yarda a karya ba.
“Mun sha samun ƙorafe-ƙorafen hana jam’iyyun adawa samun damar yin amfani da kayayyaki mallakar gwamnati, kamar kafafen yaɗa labarai ko filayen yin kamfen.
“Ina jaddada cewa yin amfani da ƙarfin mulki a hana jam’iyyar adawa dama daidai da jam’iyya mai mulki a kafafen yaɗa labarai na gwamnati haramun ne a dokar INEC Sashe na 95 (2,3,4,5,6).
“Kada kafafen yaɗa labarai na gwamnati su hana wata jam’iyya damar yayata manufofin ta daidai da lokacin da su ka bai wa jam’iyya mai mulki.”
Yakubu ya ce akwai hukuncin da dokar INEC ta tanadar ga kafar yaɗa labaran, wanda ya haɗa da cin tara ta naira miliyan biyu.
“Amma idan aka sake karya dokar, to sai an biya naira miliyan biyar. Shi kuma shugaban kafar yaɗa labarai ko ma’aikatan da su ka karya dokar za a ci su tara ta naira miliyan ɗaya, ko ɗaurin wata shida a kurkuku.”