• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Rarara ya waƙe Tinubu, ya saka gasar bidiyon waƙar inda zai raba motoci

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 12, 2022
in Labarai
0
Daga hagu: Rarara, Tinubu, Baban Chinedu da El-Mu'az Birniwa

Daga hagu: Rarara, Tinubu, Baban Chinedu da El-Mu'az Birniwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya taya ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe zaɓen fidda-gwani da ya yi a ranar Asabar ta makon jiya.

Haka kuma ya rera masa waƙa tare da bayyana gasar bidiyo inda zai ba gwaraza kyautar motoci da manyan wayoyi samfurin Iphone-13.

Rarara, wanda shi ne shugaban mawaƙan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na Arewa, ya miƙa saƙon taya murnar ne kwana ɗaya da bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyya a babban zaɓen 2023 a wani bidiyo da mai taimaka masa a harkar soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya fitar a dukkan shafukan sada zumunci na mawaƙin.

Da farko dai Rarara ya ce, “Babu abin da za mu ce wa Allah sai godiya. Babbar nasara da aka samu an yi zaɓe lafiya, an gama lafiya. Wanda mutum ya tara mutane dubunnai ko miliyoyi a wuri ɗaya don a haɗu a yi wani abu da ya fuskanci ƙasa, a ce an samu dama Allah ya yi mana iko, Allah ya taimake mu an yi an gama lafiya, babu abin da ya fi wannan daɗi.”

Ya ƙara da cewa, “Sai kuma godiya da zan yi ga su daliget, waɗanda su ka yi namijin ƙoƙari wurin turzawa da zakuɗawa su zaƙulo mana nagartaccen mutum ɗan siyasa, wanda ya san darajar siyasa, ya san mutuncin ‘yan siyasa. Ka ga wannan ba ƙaramin jin daɗi za a yi ba. 

“Ina godiya ga shugaban ƙasa, shugaban jam’iyya, shugabannin wannan gwamnati, waɗanda su ka gabatar da wannan zaɓe, dole a yi masu ban-gajiya. Mutane sun kwana a wuri don a tabbatar da zaɓe cikin adalci.”

Rarara ya ci gaba da cewa, “Ni kowa ai nawa ne. Ina kira ga su ‘yan takara, ai da ma abu ne jam’iyya da aka yin zaɓe wanda Allah ya ba shi ne. Allah ba ya sabon aiki, da ma Allah ya riga ya zaɓi Malam Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar APC da yardar Allah kuma shugaban ƙasar Nijeriya. 

“Ni kira na ga ‘yan takara, mu zo mu haɗa kan mu jam’iyya mu dai jam’iyyar mu ce, duk inda za ka je babu inda ya fi gidan ka. Saboda haka mu zo mu yi ƙoƙari duk bakin ƙoƙarin da za mu yi, mu yi ƙoƙari mu ga mun haɗa kan jam’iyyar nan, yadda bakin gwargwado mu ga mun ɗora wannan ɗan tahaliki ya zama shugaban ƙasa, wanda kuma mu zo mu fuskanci Nijeriya da kuma abin da ya kamata mu taimaki ƙasar mu da ‘ya’yan mu.”

Dangane da waƙa da ake zaton kila zai fitar nan ba da daɗewa ba, Rarara ya ce, “Ai da ma na ce duk wanda ya ci zaɓe za a ji waƙar da zan yi masa. Ai da ma ɗan jam’iyya ta ne, duk ɗan jam’iyya ta idan ya ci da ma haka mu ke fata. 

“Mu abin da mu ka so da mu ka yi magana, ai da ma cewa mu ka yi a yi dimokiraɗiyya, kuma ita da ma dimokiraɗiyyar nan ita ta kawo kowa. Saboda duk lokacin da aka ce wane, wani zai ce shi ba a kyauta masa ba, inda an bari an yi zaɓe, inda kaza, to yanzu zaɓen aka ce a yi. 

“Inda shugaban ƙasa ya burge ni, inda ya ce a’a ai gaba ɗaya kowa ma ya dawo a yi zaɓe. Da an ce an sasanta an bar wa Kudu, sai aka ce a’a kowa ma ya na da damar ya shiga, ka ga yanzu an ba wa kowa ƙuri’a, wani ma ya cewa ai shi zai ci zaɓe, shi zai yi kaza, amma ana shiga zaɓen sai Allah ya nuna wanda ya riga ya tsara zai zama. Nan da zuwa gobe za ka ji abin da ni kuma zan faɗa.”

Ko yaya batun sauran jam’iyyu? Sai ya kada baki cikin dariya ya ce, “Duk wata jam’iyya da ta ke rara-gefen ta ko kuma tashen kumfar kilin, ai ana faɗa masu Bola Tinubu ne kowa hankalin sa ya tashi, duk wata jam’iyya yanzu – ba jam’iyyar PDP kawai ba, duk wata jam’iyya irin masu tashen kumfar kilin ɗin nan – yanzu hankali ya tashi, saboda an ce Asiwaju ne. Shi kuma Asiwaju an san ɗan siyasa ne gogagge, ‘grassroot’ ɗin siyasa, wanda duk inda ka je akwai tushen sa ko kuma akwai furen shi ko kuma akwai jijiyar shi. Saboda haka mutum ne wanda shi ɗan siyasa ne, ya san darajar ‘yan siyasa, ya kuma iya tafi da ‘yan siyasa. Saboda haka ba za a samu tasgaro ba a wannan tsarin, zaɓe ‘full’ na gaya maka, cin zaɓe da wuri ma in Allah ya yarda. 

“Ni da ma ko a jiki na, duk wanda da ma ya ci zaɓe shi ne nawa. 

“Ina yi mana fatan alkhairi gaba ɗaya. Ina ƙara yi wa daliget godiya na wannan ƙoƙari da su ka yi, dole a gode masu. Mun gode, mun gode! 

“Kuma in Allah ya yarda za su ga amfanin wannan abu da su ka yi, za su ga amfanin zaɓen Asiwaju da su ka yi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. 

“Akwai abin da ya sa na ke cewa daliget sun mana ƙoƙari, saboda mun ɗan samu matsala. Akwai waɗanda aka ba muƙamai wanda in ka je wurin su sai su ce su ba ‘yan siyasa ba ne. Asiwaju ko shi ba zai yi maka haka ba. Idan za ka ce kai ba ɗan siyasa ba ne, ba ka isa ka shiga ‘system’ ɗin gwamnatin shi ba, saboda siyasa ne ta kawo ‘yan jam’iyya dukkan mu kan mu a haɗe ya ke. Ba za ku gane wannan ba sai an shiga akwatin zaɓe, duk wani ɗan takara da ya ke rawar ƙafa (dariya) zai gane da ruwa ake shayi! Na gode.”

Rarara dai ya saki sabuwar waƙar Tinubu mai taken ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ a daren Juma’a, 10 ga Yuni, 2022. 

A ranar Alhamis, Rabi’u Garba Gaya, mai taimaka wa mawaƙin a ɓangaren soshiyal midiya, ya fara gutsura wa duniya ‘yar guntuwar waƙar da ba ta wuce ta sakan goma ba. Nan da nan jama’a su ka fara tambayar cikakkiyar waƙar, inda a safiyar Juma’ar su ka sanar da lokacin da za su saki cikakkiyar waƙar.

Duk inda ka leƙa yanzu a shafukan sada zumunci za ka ji waƙar kawai ake ɗorawa.

A wannan karon ma dai mawaƙin ya yi abin da ya saba yi lokaci zuwa lokaci idan ya saki sabuwar waƙa na saka gasa.

Fitaccen furodusa Abubakar Bashir Maishadda da fitacciyar jaruma A’ishatul Humaira sun sanar da saka gasar waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ a jiya Asabar, 11 ga Yuni, 2022. Ga yadda gasar waƙar za ta kasance.

‘Yan TikTok, za su yi bidiyo su na mamin ɗin waƙar, inda za su ɗora a shafukan su na TikTok ɗin. 

Waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3, za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 kuma zuwa na 10 za a ba su kyautar wayar hannu ƙirar Iphone-13.

Su kuma ‘yan Instagram da Facebook bidiyon waƙar za su yi wanda bai wuce ƙasa da minti biyu ba ‘standard’, a gefe da gefe kuma za su saka hoton Tinubu da hoton APC. Su ma waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3 za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 zuwa na 10 kuma kyautar waya ƙirar Iphone-13. Duk wanda ya yi bidiyon zai ɗora a shafin sa, sannan ya yi amfani da hashtag kamar haka #jagabashinegaba.

Loading

Tags: Abubakar Bashir MaishaddaAisha Ahmad IdrisAishatulhumairaBola TinubuDaudu Kahutu Rararagasamawaƙataya murnawaƙaZaɓen 2023
Previous Post

Jama’a a yi rijista, kar mata ta kada mijin fa!

Next Post

In da ran ka…!

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post
Tsohuwar da ke buƙatar taimako

In da ran ka...!

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!