WANNAN tsohuwa da ku ke gani, Allah ya ba ta ‘ya’ya biyar, maza biyu mata uku, sai ya karɓi maza biyu mata biyu, ya bar mata babban ‘yar ta mai suna Ramatu. Ramatu ta yi aure har da yara ita ma, yanzun ɗiyar Ramatu na da yara biyu!
Abin mamaki da ya ɗaure wa kowa kai shi ne yadda Ramatu ta rasa wanda za ta ci wa mutunci sai mahaifiyar ta saboda abin da mahaifiyar ta mallaka. Ramatu da mijin ta sun lallaɓi mahaifiyar, ta bar inda ta ke a Suleja ta koma wajen su a Kaduna don ta taimaka masu duba yaran su sannan su ma su taimaka mata wajen samo lafiyar ta don ta na fama da ciwon ido da ɗaurewar bayan gida.
Zuwan ta ke da wuya, Ramatu ta karɓe kuɗin da ke hannun mahaifiyar ta, su ka yi sha’anin su da shi, ta bar mata kaɗan a hannun ta. Da ta fara maganar zuwa asibiti, Ramatu ta ɗauke ta zuwa asibiti, amma fa komai sai mahaifiyar ta ta biya daga kuɗin mota zuwa na abincin da Ramatu za ta ci a wajen jira a asibiti. Kuɗin sun ƙare, zuwa asibi ya tsaya.
Amma kafin nan Ramatu da mijin ta sun lallaɓi tsohuwar nan ta sayar da gidan ta na gado da ke Wuse Sabo a Jihar Neja don ta bai wa ɗan su rance ya yi sana’a, bisa alƙawarin cewa za a raba riba da ita. Duk da yake ba ta so ba, dole ta sayar da ta ga matsi, ta ba su kuɗin.
Bayan sun karɓe kuɗin, ga ciwon ido ya matsa mata babu magani, ga lalurar rashin bayan gida, sannan babu zuwa asibiti don ba kuɗi ga hannun tsohuwa. Mahaifiyar Ramatu a hirar mu da ita ta rantse cewa Ramatu sai ta yi abinci ta na jin ƙamshi ta hana ta, har ranar Sallah! Ta ce ruwan Lipton ta ke ba ta da biredi, tun safe haka za ta wuni.
Da ta ga azabtarwa ta fara yawa, sai ta nemi su ba ta kuɗin ta ta koma gida, amma Ramatu da iyalan ta sun buga ƙasa sun ce ba wanda ya isa. Duk ƙoƙarin da wasu su ka yi tun ma ‘yan’uwan mijin Ramatu su ka yi don shiga tsakani su ba tsohuwa kuɗin ta ya ci tura. A gaban su ta ke tijara mahaifiyar ta ta yi mata sharri iri-iri.
Daga bisani, da yunwa ta ishe ta, aka samu waɗanda su ka saka ta mota ta dawo Suleja, babu ido.
Yanzun haka tsohuwa na cikin wani hali na tausayawa inda aka ba ta shawarar ta shigar da ƙara tunda Ramatu ta yi rantsuwar cewa babu wanda ya isa ya karɓi kuɗin nan hannun ta.
Duk ƙoƙarin yin magana da Ramatu ko mijin ta ya ci tura don sai yara su ɗauki wayar su su ce ba su kusa.
Amma kafin ta samu mafita ta shari’a, wannan tsohuwa na buƙatar taimakon mu fisabilillah don ta samu ɗakin kwana, ta samu yarinyar da za ta taimaka mata wajen kai da dawowa da kula da ita, sannan da kuɗin zuwa asibiti don duba ta.
Mun buɗe mata asusun neman taimako na naira dubu casa’in (N90,000): N40,000 na gidan haya da aka samo mata na shekara guda, N30,000 na ‘yar aiki na wata biyar inda mu ke fatan kafin lokacin an ƙwato mata haƙƙin ta da za ta kula da kan ta, N20,000 kuɗin magani da abinci da za ta fara amfani da su kafin ta samu mafita.
Ga waɗanda za su taimaka, za ku iya turowa da sadakar ku ta wannan asusun: 0021004568 Media For Morals, Unity Bank.
Sadaka ba ta yawa, ba ta kaɗan. Duk wanda ya cire wani cikin ƙunci, Allah zai cire shi a ranar da babu mai kuɓutarwa face Shi sannan ya kare shi daga dukkan masifun duniya.
Ƙarin bayani: ga masu cewa in bincika kila akwai abin da wannan tsohuwa ta taɓa yi shi ya sa ta ke ganin wannan jarabawa, amsa ta ita ce ba zan binciki komai ba saboda in Allah ya tashi jarabtar bawan sa akwai hanyoyi da dama kuma babu wanda ya wuce jarabawa, sai dai mu yi addu’a kawai!
Allah ya kawo mata mafita da dukkan waɗanda su ka samu kan su cikin ƙunci.
* Hajiya Mairo Muhammad Mudi fitacciyar marubuciyar littattafai ce kuma ‘yar jarida da ke zaune a Suleja, Jihar Neja. Haka kuma ita ce mawallafiyar jaridar Zuma Times Hausa da ke da gidan yanar www.zumatimeshausa.com