• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa na ke zana hotunan ‘yan Kannywood – Ibrahim Kabir Magaji

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 27, 2021
in Rayuwa
0
Ibrahim Kabir Magaji (Ibee Graphics)... yadda ya zana kan sa da komfuta

Ibrahim Kabir Magaji (Ibee Graphics)... yadda ya zana kan sa da komfuta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

IBRAHIM Kabir Magaji gwanin tsara hotuna ne da komfuta, abin da ake kira ‘digital painting’. Matashin, wanda Bazamfare ne, ya fara yin fice wajen zana hotunan ‘yan fim ya na wallafa su a Instagram a shafin sa na @ibeegraphics.

Shin me ya sa ya fi damuwa da ‘yan Kannywood? Ya na samun kuɗi da wannan abu da ya ke yi ko kuwa sha’awa ce kawai? Kuma me ya sa a cikin ‘yan fim duka ya fi son Rahama Sadau? Ko ya taɓa yin magana da ita kuwa?

Wannan fasihin matashin ya tattauna da mujallar Fim kwanan nan, inda ya amsa waɗannan tambayoyin da ma wasu, kamar haka:

FIM: Ka faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ka a taƙaice.

IBRAHIM: To, suna na dai Ibrahim Kabir Magaji. Ni haifaffen garin Zamfara ne, Ƙaramar Hukumar Gusau. Na yi karatun firamare na a Alheri Nursery and Primary School, sannan na yi sakandare na a Alheri Royal Collage, Gusau. Na wuce na yi ‘Professional Diploma’ a ‘Computer Studies’. A nan na tsaya gaskiya, ban ci gaba ba.

FIM: Ya aka yi ka fara zane?

IBRAHIM: Gaskiya na fara ganin su ‘online’, nan na koya a YouTube. To ina ganin abin kuma ya na burge ni sosai. Ni kuma sai na ga gaba ɗaya a nan Arewa ban ga mai yin irin wannan zanen ba. Sai na ce ai mu ma za mu iya, bari in gwada in gani, wataƙila zan cimma abin da na ke so. A hankali ina yi tun ina ganin abin ma ba na samo shi, har dai na fara yin ‘posting’ a Instagram, na ga mutane su na jin daɗi.

Ibrahim ya ce ya na son Rahama Sadau sosai, amma ba ta amsa gaisuwar sa. Wannan ita ce ya zana

FIM: Me ya sa ka fi zana ‘yan fim?

IBRAHIM: Gaskiya abin da ya sa na fi zana ‘yan fim, ka ga su na yin hotuna masu kyau. Kuma ba ma haka ba, ina son harkar fim sosai, shi ya sa.

FIM: Akwai wata alaƙa tsakanin ka da ‘yan fim?

IBRAHIM: To, ba na dai ce ba, mu na gaisawa, amma ba wata alaƙa sosai ba. Kamar furodusa Gwammaja Entertainment, wato Yakubu furodusa kenan, shi mu na chatting da shi a WhatsApp, mu na magana sosai saboda akwai abubuwa da mu ke gabatarwa tare da shi.

FIM: Akwai ɗan fim ɗin da ka zana hoton sa, kuma ya damu har ya neme ka ya yi maka kyauta?

IBRAHIM: Gaskiya ba a taɓ ba. Amma ban dai sani ba ko nan gaba. 

FIM: Mun ga wasu ‘yan fim ko su kwafa su tura a shafin su ko su yi ‘liking’ ko su ce wani abu a ƙasan zanen naka ba su yi idan ka zana hoton su. Ko wannan abin na damun ka?

IBRAHIM: Kai, ina! Bai taɓa damu na ba. Abin da na damu da shi mutane na son abin da na ke yi. Ko da na yi mutum bai yi ‘reposting’ ba ban damu ba, saboda mutane sun yaba.

FIM: Ka ɗauki zanen da ka ke sana’a? Kuma ka na samun kuɗi da shi?.

IBRAHIM: Alhamdu lillahi! Gaskiya ina samun kuɗi sosai. 

Wasu jarumai da Ibrahim Kabir Magaji ya zana: Adam A. Zango, Umar M. Shareef da Abdalla Amdaz
Surorin Mansurah Isah da Samira Ahmad da Ibrahim Kabir Magaji ya zana da komfuta

FIM: Ban da ‘yan fim, akwai wasu da ka ke zanawa waɗanda ba ka ɗora su a Instagram? Misali ‘yan siyasa ko masu hannu da shuni, su kan kira ka su ba ka aiki?

IBRAHIM: Gaskiya har yanzu tukunna dai. Ka ga abin ai ba wani daɗewa ya yi ba, bai jima ba. Ina dai ƙoƙarin yaɗa sana’ar a hankali, har na cimma abin da na ke so nan gaba.

FIM: A wace shekara ka fara zane?

IBRAHIM: Na fara a shekarar 2019

FIM: Bayan zane, akwai wata sana’a da ka ke yi ne?

IBRAHIM: Gaskiya shi ne dai abin da na ke yi.

FIM: Menene burin ka a harkar zane?

IBRAHIM: Buri na ina son in zama ‘professional artist’ a nan gaba. Ba ma Nijeriya ba kaɗai, duk duniya na ke so in shiga da harkar ‘graphics’.

FIM: Ko ka na da sha’awar zama ɗan fim?

IBRAHIM: E to, nan gaba in Allah ya ce in zama ɗan fim, zan zama.

FIM: Ka na da iyali?

IBRAHIM: A’a, tukunna dai.

FIM: Shekarun ka nawa a duniya?

IBRAHIM: Gaskiya shekara na 23.

FIM: Da me ka ke yin zanen? Da hannu ne ko da komfuta?

IBRAHIM: A’a, ba da hannu ba ne. Shi wannan ana ce masa ‘digital painting’. ‘Digitally’ ake yin shi; in ka na da ‘laptop’ za ka yi, amma shi zane da za ka yi aiki sosai. Ka ga za ka yi aiki a kan idanu, a kan gashi, a kan haƙora, komai sai ka gyara su, haka kayan ma komai daban za ka yi shi. 

Ummi Rahab da Fati Shu’uma daga zanen Ibrahim Kabir Magaji
Yadda Ibrahim Kabir Magaji ya zana Ali Nuhu da matar sa da Garzali Miko da matar sa

FIM: Ka taɓa burin ka zana wani babban ɗan siyasa, kuma ka neme shi ka kai masa?

IBRAHIM: Gaskiya ina da wannan burin, sai dai yanzu yanayin ‘yan siyasan, ta ina za ka ga mutum ballantana har ka ba shi? Kwanaki akwai aikin da mu ka yi wa Rarara, har yanzu dai ba a samu an kai masa ba.

FIM: Wane ɗan fim ka ke da burin haɗuwa da shi?

IBRAHIM: Gaskiya ina da burin haɗuwa da Rahama Sadau domin ni masoyin ta ne, ta na burge ni ƙwarai da gaske. 

FIM: Ka taɓa zana hoton ta?

IBRAHIM: Sosai, ina zana hoton ta. 

FIM: Amma ta taɓa yi maka magana?

IBRAHIM: Ba ta taɓa magana ba, ko na yi mata ‘dm’ ba ta amsawa. Amma ban ga laifin ta ba, saboda ta na da mabiya sama da miliyan biyu a Instagram. Ka ga kuwa ta ina za ta fara? Wataƙila ma saƙo na ba za ta gan shi ba. 

Asiya Ahmad da Sadiq Sani Sadiq daga komfutar Ibrahim Kabir Magaji
Ibrahim Kabir Magaji… yaro mai basira

FIM: Ka taɓa neman lambar wayar ta?

IBRAHIM: Gaskiya ban taɓa ba, don na san zai yi min wahala.

FIM: Malam Ibrahim, mun gode.

IBRAHIM: Ina godiya ƙwarai.

Loading

Tags: artistdigital paintingGusauhausa actorshausa filmsibeegraphicsIbrahim Kabir MagajiInstagramKannywoodRahama SadauZamfara
Previous Post

Cewar Abubakar Anka: Me zai hana ‘yan Kannywood su yi fim don Netflix?

Next Post

Abdullahi Ubangari ya zama angon Zulaihat

Related Posts

Mace na yin wanki (Hoto daga: Deposit Photos)
Rayuwa

Zamantakewa: Tsakanin darajar namiji da mace

July 11, 2023
Ambasada John Mamman Garba
Rayuwa

Ɗan’uwa ko ka taɓa jin labarin Ambasada John Mamman Garba?

August 12, 2022
Tsohuwar da ke buƙatar taimako
Rayuwa

In da ran ka…!

June 13, 2022
Alfanun albasa ga lafiyar jiki
Rayuwa

Alfanun albasa ga lafiyar jiki

September 7, 2021
Tsakanin shahara da jarraba
Rayuwa

Tsakanin shahara da jarraba

April 5, 2021
Matsalar almajirai ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Arewa
Addini

Mu dai a Arewa an sha mu mun warke!

October 2, 2019
Next Post
Ango Abdullahi da amarya Zulaihat a wurin dina

Abdullahi Ubangari ya zama angon Zulaihat

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!