ABUBAKAR Musa Anka ba baƙo ba ne a fagen shirin fim. Anka, kamar yadda kowa ke kiran shi a Kannywood, ya daɗe ana gwagwarmaya da shi a fagen.
Ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara, amma mazaunin Kaduna, Alhaji Abubakar ya shirya finafinai a baya, kuma a lokacin da gwamnan Zamfara mai ci a yanzu, wato Bello Muhammad Matawalle, ya na matsayin ɗan Majalisar Tarayya, Anka ne ke jagorantar ‘yan fim zuwa wajen sa.
To sai dai ya ɗauki tsawon shekara shida ba a jin ɗuriyar sa a masana’antar Kannywood. Shin ina ya shiga? Ya bar harkar fim ne kwata-kwata? Wace sana’a ya ke yi yanzu? Ya na tare da Matawalle har yanzu kuwa? Me zai ce game da harkar fim da ta koma YouTube?
Waɗannan da ma wasu tambayoyin su ne mujallar Fim ta yi masa bayan ta binciko shi, kuma ya amsa su cikin natsuwa kamar haka:
FIM: Tsawon lokaci an daina jin ɗuriyar ka a industiri. Ina ka shige?
ABUBAKAR ANKA: Assalamu alaikum. Kamar dai yadda aka sani, suna na Abubakar Musa Anka, shugaban kamfanin Anka Production, Kaduna, kuma darakta a kamfanin Smart Nigeria Limited, wanda ke sayen fim da buga shi da kuma saida shi a kasuwa.
A gaskiya, dalilin rashin gani na a harkar finafinai bai rasa nasaba da abu biyu. Matsala ta farko shi ne taɓarɓarewar tarbiyya da aka samu a masana’antar, ma’ana abin da aka sani da masana’antar fim ta na faɗakar da al’umma, ta na kuma sanar da al’umma abubuwan da ba su sani ba ko su ka sani su ka manta, zai tamake su a rayuwa; ma’ana, faɗakarwa da taimakon rayuwar al’umma.
Na biyu, an san masana’antar fim masana’anta ce da ta ke ɗauke da aƙalla duk Nijeriya, mu na zaton mutum miliyan ɗaya ne ke cin abinci a ƙarƙashin ta.
Amma duk da wannan cigaba ko kuma irin wannan al’amari da ke cikin ta, amma al’ummar da ke cikin ta ba su tsaya sun fahimci abin da su ke yi ba, sai su ka sakankance rashin tarbiyya ya shiga ciki. Idan ka zama ɗan fim, in aka kalle ka mutane sai su rinƙa ganin ba ka da tarbiyya, kamar mutumin banza.

Haka kuma shugabanci ya lalace, wanda ya kasance shugabannin sun bada gudunmawa wurin lalacewar harkar, saboda su kan su ba su riƙe girman su ba ga mutanen da su ke biye da su a harkar.
Wannan sai ya sa abubuwan su ka samu tarnaƙi, abu na kwan gaba, kwan baya, babu wani cigaba a ciki, har abu ta kai ga za ka zuba kuɗin ka a ciki, daga ƙarshe ka yi asara. Amma a da can baya, babu yadda za ka yi fim a ce ka yi asara.
FIM: Yanzu wace sana’a ka ke yi?
ABUBAKAR ANKA: Bayan na janye jiki na a harkar fim, sai na koma harkar siyasa, na kuma shige ta gadangadan, na yi takara ban samu ba. Sai dai na samu muƙami a gwamnatin Jihar Zamfara, inda aka ba ni S.A. a jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulazeez Yari. Na riƙe wannan muƙami na tsawon shekara biyu da rabi zuwa uku.
Sannan kuma na shiga dillancin motoci. Ni dillali ne na motoci, don yanzu haka ni cikakken memba ne a ƙungiyar masu saida motoci.
FIM: Yanzu tsawon shekara nawa kenan ka ɗauka rabon ka da Kannywood?
ABUBAKAR ANKA: Tun 2015 na bar harkar fim. Yanzu tsawon shekara shida kenan.
FIM: Ya ka ke kallon Kannywood a da da kuma yanzu?
ABUBAKAR ANKA: Gaskiya tsakani da Allah harkar fim ta samu naƙasu. Naƙasun kuma shi ne, an samu naƙasu ta ɓangaren masu satar fasaha da kuma ‘yan ‘downloading’, domin su su ka taimaka kasuwar finafinan Hausa ta durƙushe. Kuma wannan ɗabi’ar ta rashin haɗin kai ita ce ta haddasa wannan abu. Sai ya zama babu wani riba da za ka samu in ka shirya fim. Don haka magana ta gaskiya da ne aka more harka, ba yanzu ba.

FIM: Ta ɓangaren kayan aiki da sauran wasu abubuwa an samu cigaba. A ganin ka wannan ba cigaba ba ne?
ABUBAKAR ANKA: Lallai an samu cigaba ta ɓangaren kayan aiki. Kuma ai ko kafin in ja baya da harkar, akwai fim ɗin da na shirya mai suna ‘Dakta Matawalle’, babu wanda bai cikin fim ɗin a manyan jarumai, kuma har yanzu ban saida shi ba. A wannan lokacin kayan aiki na zamani na ɗauko haya daga kudu. Wannan fim ɗin kuma shi ne fim ɗi na na ƙarshe.
Don in dai maganar kayan aiki ne, an samu cigaba, amma har yanzu ‘yan Kannywood ba su yi dabara ba na zuwa su samu gwamnati don samun tallafi don gudanar da harkokin su.
Yau ka dubi ‘yan’uwan mu na Kudu har ‘international films’ su ke yi. Yanzu har Netflix na sayen finafinan su, sai ka ji sun sayi fim naira miliyan ɗari biyar, miliyan ɗari uku, miliyan ɗari biyu, har sama da waɗannan kuɗaɗen. Mu me ya hana mu? Mun ƙi mu shiga mu yi gogayya da su ‘yan Kudun, mu cire kuɗi mu je mu yi haɗin gwiwa da kamfanoni, bankuna da sauran su mu gani idan mu ma ba a yi alfahari da mu ba.
Amma kuma ta wani ɓangaren ina kallon ko saboda rashin karatu ne da ba mu maida hankali mu na yi ba, ban sani ba. Amma ni dai yanzu a gaskiya bai kama a ce mun tsaya an bar mu a baya ba.
Ni shawarar da zan ba ‘yan’uwa na, ya kamata a jajirce domin akwai alheri a cikin fim, duk sun sani, sai dai idan yau ka shigo masana’antar.
FIM: Haji Anka, ka yi maganar Netflix. Ka na ganin a Kannywood akwai wanda zai iya cire kuɗaɗe masu yawa don ya shirya irin fim ɗin da Netflix ke saye?
ABUBAKAR ANKA: Ah, haba Malam Abba! Akwai mana. Ai masana’antar Kannywood masana’anta ce mai albarka. Amma mu mu ka watsar da ita. Babu abin da ba za a iya yi ba a cikin masana’antar nan. Duk wata albarka da ake nema a ƙasa, Kannywood ta na da shi.
Yanzu mu na lissafin mutane sama da miliyan ɗaya ke cin abinci a ƙarƙashin ta duk da lalacewar harkar. Kuma ka na gani kashi 50 a cikin ɗari na zaɓe da ake yi a ƙasar nan Kannywood ke bada gudunmawa.
In da za a yi wa Kannywood adalci a gwamnatance, ko nawa aka ba ta ba a yi asara ba.Don haka ina da yaƙinin cewa akwai waɗanda za su iya jajircewa su yi abin da ya kamata.
Ni ɗin nan da na ke magana da kai a yanzu ba furodusin ba, ina ɗaya daga cikin wanda ba zan ji zafin cire kuɗi masu yawa in yi fim ba. Kuma ina mai tabbatar maka ba zan ce komai ba, amma in mai yiwuwa ta yiwu in na samu damar dawowa harkar fim, zan dawo da sabon salon da zai taimaki harkar fim.
FIM: A baya ka na ɗaya daga cikin mutanen gwamnan Zamfara na yanzu, wato Bello Muhammad Matawalle, wanda har ka yi wa ‘yan fim jagora a wurin sa. Har yanzu ka na tare da shi ne?
ABUBAKAR ANKA: Mai girma gwamna a baya ya na jam’iyyar PDP, ni kuma ina APC, bisa wasu dalilai su na da tsawo. Amma yanzu dai da ya dawo APC ban zauna tare da shi ba. Amma haƙiƙa akwai waɗanda su ke tare ni a cikin ‘yan fim sun fi mutum goma, domin sun yi alhinin barin Matawalle da na yi, domin sun san amfanar da su ka yi sakamakon zama na da Bello Matawalle. Waɗanda aka kai Makka, waɗanda aka saya wa motoci duk sun sani, kuma ta dalili na, ni ne sila na ba su.

Saboda haka na san ‘yan fim ba za su manta da sakamakon wannan abin ba da na yi masu na wannan taimakon. Don haka ina yi masu albishir da cewa kamar yadda aka saba a baya, duk da ba ni tare da Dakta Bello Matawalle, amma ina tare da tsohon gwamna Abdulaziz Yari, kuma zan bi mutanen domin su taimaka su ba mu goyon baya domin mu ga cewa Abdulazeez Yari ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Shi kuma Dakta Matawalle, in Allah ya ba ni iko mu ka zauna da shi, daga nan za mu sanar da su matsayar da mu ka tsaya.
FIM: Wane lokaci ka ke tunanin dawowa harkar fim?
ABUBAKAR ANKA: To, Malam Abba, abu biyu ne dai, kamar an ɗauki saiti. Saiti da na ke gani an ɗauko, ga shi an samu cibaya wurin saida fim ɗin, amma a ɓangare guda an samu cigaba a kayan aiki da yadda ake yin fim ɗin, domin ilimi ya fara shiga harkar. Game da wannan ina godiya ga Allah.
Saboda haka ina yi wa ‘yan Kannywood albishir da akwai tsare-tsare da za mu zo da shi, amma dai ba zan faɗi lokaci ba ko kuma in ce zuwa wane lokaci da wannan tsarin zai fito. Kamar yadda na faɗa a baya, zan dawo da tsarin da zai taimaki Kannywood da al’umma.
Amma har yanzu ban aje lokacin dawowa na ba, don ko da zan tafi ban sanar da kowa ba, haka kuma in zan dawo ba zan sanar da kowa ba, sai dai a gan ni da sababbin tsare-tsare na.
Ka san ita harkar fim ba a fita gaba ɗaya, don ko ka bar ta sai ka dawo. In ma ba ka dawo ba, har ka mutu kai ɗan fim ne, ba ka isa ka goge wannan sunan ba.
FIM: A wani ɓangaren, yanzu finafinan Hausa an koma yin su ne masu dogon zango (series), kuma ana ɗora su ne a YouTube. Ka na ganin harkar YouTube mafita ce ga Kannywood?
ABUBAKAR ANKA: Gaskiya tsakani da Allah a nawa basirar da tunani, harkar YouTube ba ta ɗaukar Kannywood. Saboda a irin fahimtar da na yi wa industiri daidai gwargwado, na san cewa YouTube ba zai ɗauki harkar fim ɗin Hausa ba.
Dalili kuwa, YouTube ɗin nan su na da ƙa’idoji wanda sai ka bi su daki-daki ka cika su. Ni abin da na ɗauki YouTube a wurin ‘yan Kannywood kamar bayin su ne kawai. Saboda duk ƙwazon da za ka yi, kashi hamsin YouTube ne su ke ƙaruwa da kai. Kawai dai YouTube ya zama ‘alternative’ ne na dole ga ɗan Kannywood, don babu yadda zai yi.
Ni a nawa tunanin, mafita ga Kannywood shi ne Netflix ɗin nan da sauran su. Kuma na san ‘yan fim ɗin da za su iya fitar da manyan kuɗaɗe su yi irin fim ɗin da ake buƙata a can ɗin. To kuma a yau kowa ya koma YouTube. Ka faɗa min mutum nawa ke amfana da YouTube a Kannywood? ‘Yan tsiraru ne kawai.

FIM: Haji Anka, a matsayin ka na furodusa, za ka iya neman wasu daga cikin abokan sana’ar ka ku yi haɗin gwiwa don ku shirya irin fim ɗin da Netflix ke so?
ABUBAKAR ANKA: Ai ko fim ɗin da na yi na ƙarshe a shekarar 2015, naira miliyan goma na kashe a wancan lokacin. Kamar Mandawari da ya ja fim ɗin ya sani, irin Zaharaddin Sani, Sani Danja, Jamila Nagudu duk su na ciki, kuma sun san abin da na kashe wa fim ɗin. Bayan abin da su ka samu, a kan fim na rabar da mota aƙalla za su kai guda goma ga ‘yan fim a dalilin wannan fim ɗin. Haka wanda aka biya wa Umura sun kai mutum goma dalilin wannan fim ɗin na ‘Dakta Bello’, wanda na san wannan kyauta ce daga Allah. A wannan lokacin Dakta Bello Matawalle ya bada motocin da kujerun Umura kuma duk na ba su.
To kuɗin da na kashe wa fim ɗin ya kai naira miliyan goma. To ka ƙirga daga lokacin zuwa yanzu shekara shida kenan. A yanzu ina mai tabbatar maka ina iya cire naira miliyan hamsin in yi fim, kuma na san ba za a yi asara ba in an bi ƙa’idojin da ya dace wurin yin fim ɗin, kuma aka samu goyon baya.
Ka je ka saida fim a kasuwar duniya in ka yi shi ya kai ‘standard’ ɗin da su ke buƙata. Ni kuma na tabbata ina da ‘confidence’ da zan iya yin wannan fim ɗin, da yardar Allah.
In kuma zan yi wannan fim ɗin zan nemi haɗin gwiwa ne da bankuna da kamfanoni da gwamnati. Saboda alhamdu lillahi mu ‘yan siyasa ne, mu na tare da gwamnati daidai gwargwado. Kuma na tabbatar da cewa su kan su gwamnati su na ƙaruwa da ‘yan fim.
FIM: A ƙarshe, mecece shawarar ka ga ‘yan fim baki ɗaya?
ABUBAKAR ANKA: Shawara guda uku ne. Na farko, a nemi ilimi, domin duk wanda bai yi karatu ba an bar shi a baya. Na biyu kuma, mutum ya dogara ga Allah. Na san matsalolin da ke cikin fim daidai gwargwadon sani na, gaskiya sai an yi gyara a kan kowa da kowa na masana’antar domin ana abubuwan da ba su dace ba a cikin ta. Na uku kuma, a nemi hanyar samun kuɗi a cikin ta, a haɗu a yi ƙungiya mai ƙarfi, a fitar da jadawali da tsare-tsare wanda zai taimaki mutanen da su ke cikin harkar.
Sannan ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shigo harkar nan domin ta taimaki mutanen nan, saboda su ma su taimaka mata.

Sai kuma mu yi ƙoƙari mu riƙe Allah, mu tsarkake zuciya. A daina bin juna da sharri da cin amana, a taimaka wa juna. A cire butulci; sai mutum ya taimake ka, a ƙarshe ka yi masa butulci. Wannan ba daidai bane. In kuma ba haka ba, ba za ka taɓa samun nasara a rayuwar ka ba. Wannan shi ne.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com
![]()







