• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a ƙaddamar da littafin ‘Diwanin Waƙoƙin Aminu Ala’ bayan Sallah

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
April 17, 2021
in Mawaƙa
0
Za a ƙaddamar da littafin ‘Diwanin Waƙoƙin Aminu Ala’ bayan Sallah
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYAN Ƙaramar Sallah mai zuwa ne za a ƙaddamar da wani littafi mai ƙunshe da waƙoƙin fitaccen mawaƙi Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) a rubuce.

Wasu manazartan Hausa ne su ka rubuta kalmomin waƙoƙin daga rerawar da ya yi, su ka fitar da littafi mai taken ‘Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa’.

A wani saƙo da ya wallafa a Instagram, wanda mujallar Fim ta ɗauko, mawaƙin, wanda shi ne Ɗanburan Sarkin Gobir kuma Sarkin Waƙar Dutse, ya bayyana farin cikin sa kan wannan muhimmin aiki da aka yi.

Ya ce, “Mu na jaddada godiya ga Allah domin tarin ni’imomi tare da yassarewa da sahalewa ta irin wannan nasibi abin bugun gaba a raye da bayan wafati.

“Haƙiƙa wannan kundi wata manuniya ce ta sakamakon nagarta da jajircewa.

“Ashe martaba da mutunci su na daga abin nema a cikin rayuwar tauraro ba kankajere a wajen neman garin kuɗi ta kowanne hali ba.

“Sai na ke ganin abin kamar wata waibuwa irin yadda martabobi ke jeren farin ɗango kamar ana tisa ƙwayar carbi.

Aminu Ala ya na duba littafin ‘Diwanin Waƙoƙin Aminu Ala’ cike da sha’awa

“Alhamdu lillahi Rabbil alamina!Babu furuci na yabo da godiya sama da wannan. 

“A ƙarshe, ina miƙa godiya ga marubuta wannan littafi na ‘Diwanin Waƙoƙin Ala’, da su ka sami ikon hattama wannan kundi tun ina raye.

“Ina shaida wa masoya da manazarta cewa za a ƙaddamar da wannan littafi da ƙarfin Allah a jihar Kanon Dabo bayan Sallah da izinin Ubangijin kowa.

“Allah ya bada ikon halartar wannan gagarumin taron ƙaddamarwa da za a yi a Kano. Da zarar an saka lokaci, za a shaida maku masoya na haƙiƙa.”

A baya, an taɓa fitar da littafi mai ɗauke da waƙoƙin Ala a rubuce.

Ala dai ya na ɗaya daga cikin zaratan mawaƙan ƙasar Hausa na wannan zamanin.

Waƙoƙin sa sun zama abin nazari musamman ga ɗalibai manazarta harshen Hausa saboda yadda waƙoƙin su ke ƙunshe da hikimomin harshen Hausa. 

Ya samu karramawa iri-iri saboda gudunmawar da ya ke bayarwa ga adabin Hausa.

Kafin ya fara waƙa, Ala marubucin zube ne wanda ya wallafa littattafai a kan jigon soyayya.

Tags: Alan WakaAminu AlaAminuddeen Ladan AbubakarDiwanin Wakokin Aminu AlaFim MagazineKannywoodmawakan hausa
Previous Post

INEC ta fara horas da shugabannin harkar zaɓe kan yawaita rumfuna

Next Post

Ana amfani da suna na ana damfara a Facebook, inji Aisha Tsamiya

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Ana amfani da suna na ana damfara a Facebook, inji Aisha Tsamiya

Ana amfani da suna na ana damfara a Facebook, inji Aisha Tsamiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!