JARUMI a Kannywood, Alhaji Tijjani Usman Faraga, shi ma ya shiga sahun ‘yan Kannywood masu sarautar gargajiya.
Ɗansararin Sarkin Bauchi, Alhaji Labaran Ahmed Maƙera, shi ne zai naɗa shi sarautar Zannan Ɗansararin Sarkin Bauchi.
Jarumin ya sanar da mujallar Fim cewa za a naɗa shi sarautar ne a jibi Lahadi.
Ya ce, “Cikin hukuncin Allah za a naɗa ni sarautar Zannan Ɗansararin Mai Martaba Sarkin Bauchi. Don haka ina farin cikin sanar da kai da kuma wannan ‘magazine’ tamu mai albarka.”
Ya ci gaba da cewa, “Yadda abin ya kasance shi ne, shi Alhaji Labaran Ahmed Maƙera (Ɗansararin Mai Martaba Sarkin Bauchi) shi ne ya ba ni wannan sarauta ta Zannan Ɗansararin Bauchi sakamakon ƙauna ta musamman da ya ke yi min da kuma samun yabawa da ayyukan da na ke yi na yin finafinai masu ma’ana na faɗakarwa da kuma nishaɗantar da al’umma.

“Yanzu haka mutane da dama sun nuna sha’awar zuwa garin Bauchi domin gane wa idon su irin yadda naɗin da kuma yadda bikin zai kasance.”
Katin gayyatar bikin ya nuna cewa za a yi wannan naɗi ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 a Unguwar Nasarawa da ke bayan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi (Ministry of Higher Education) a birnin Bauchi.