• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za mu sake dasa wa ‘yan Nijeriya ɗabi’ar gaskata kalaman shugabanni a zukatan su – Minista

by DAGA WAKILIN MU
October 17, 2023
in Nijeriya
0
Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya nuna damuwar sa ganin yadda akasarin ‘yan Nijeriya sun daina yin amanna, yarda ko gaskata kalaman da ke fitowa daga bakin shugabannin su.

Ministan ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Abuja.

“Abin da mu ke so shi ne a bar ‘yan Nijeriya su san gaskiya daga waɗanda suka wajaba su bayyana masu gaskiyar. Ina ganin muhimmin abu ne sosai a ga cewa an ɗora tsarin isar da saƙo a kan turbar faɗa ko bayyana gaskiya, ta yadda wanda ake faɗa wa gaskiyar zai yi amanna da abin da mai faɗa masa gaskiyar ya ke faɗa.

“Wannan haka ne, saboda mun ga irin yadda amanna da gwamnati da kuma amincewa suka gushe ko suka zaizaye a zukatan jama’a, a ƙasar nan.

“Mun kai matakin da akasarin ‘yan Nijeriya ba su yin amanna da abin da shugabannin su ke faɗa masu. Kuma fa su mutanen su suka zaɓi shugabannin  da hannun su.

“Saboda haka akwai matuƙar buƙatar mu fara ganin mun kankaro wannan gwamnati daraja, ta hanyar samun amincewa da amanna daga wurin ‘yan Nijeriya.

“Za mu yi wannan aikin haiƙan, bakin ƙarfi da iyawar gwamnati, domin ganin jama’a sun dawo su na gaskata kalamai da bayanan gwamnati,” cewar Idris.

Ya ƙara da cewa faɗin gaskiya shi ne matakin farko na nagartar mutum, domin idan jama’a suka san gwamnati na faɗar gaskiya, to su ma fa masu bada rahotannin bayanai tsakanin tilas su riƙa faɗar gaskiya.

Idris ya ce gwamnati na ƙoƙarin ƙara zaburar da jama’a  cewa ko wa ya kasance ya na faɗar gaskiya.

“Za mu fito mu yi kamfe na daƙile masu yaɗa labaran bogi da ƙarairayi, waɗanda hatsarin su zai iya kaiwa ga ruguza al’umma ko kawo rabuwar kai.

“Kuma za mu ci gaba da kwaɗaitar da kafafen yaɗa labarai su tsaya kan turbar bayyana gaskiya, wadda dama ita ce kyakkyawar ɗabi’ar da aka san kafafen yaɗa labarai ke kan ta, kuma suke kan koyarwar ta,” cewar Minista Idris.

Dangane da labaran bogi, Idris ya ce wannan matsala ba ta Nijeriya kaɗai ba ce, abu ne wanda ya game duniya. Ya ce idan aka haɗa hannu za a iya kawar da yaɗuwar su, ba tare da an take haƙƙin kowa ba.

Loading

Previous Post

‘Yan jarida sun cancanci samun rayuwa mai inganci a Nijeriya – Idris

Next Post

Furodusa a Kannywood, Hamisu Bawasa, ya yi rashin mahaifiya

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Next Post
Hamisu Bawasa tare da mahaifiyar sa, marigayiya Malama Fatima

Furodusa a Kannywood, Hamisu Bawasa, ya yi rashin mahaifiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!