ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa fitacciyar zabiya Magajiya Ɗambatta rasuwa, ta na da shekara 85 a duniya.
Ta rasu a yau Juma’a, 8 ga Oktoba, 2021 a garin su, wato Makoɗa da ke cikin Jihar Kano.
Magajiya ta yi fice ne a ƙarshen shekarun 1970 zuwa shekarun 1980 musamman saboda waƙar ta mai suna ‘Soriyal’ mai yin kira ga iyaye da su sanya ‘ya’ya a makaranta.
Idan kun tuna, mun taɓa ba ku labarin yadda a cikin Disamba 2019 fitaccen ɗan jaridar nan Malam Jaafar Jaafar ya jagoranci ƙaddamar da gidauniyar neman agaza wa mawaƙiyar saboda ganin halin ƙunci da ta ke ciki.
Dalili shi ne Magajiya ta makance, kuma sai ta yi bara sannan ta samu abin da za ta ci.
Jaafar, wanda shi ne Babban Editan jaridar ‘Daily Nigerian’, ya yi rubutu a lokacin da ya gano cewa Magajiya ta na raye amma ta na cikin ƙunci, ya bada labarin halin da ta ke ciki.
A rubutun, ya bayyana cewa makaɗin kalangun zabiyar, Ya’u Nakuki, da ɗan kuntukun sa sun daɗe da rasuwa, amma mawaƙiyar da wasu ‘yan amshin ta na nan da ran su.
Ya ambato rubutun da fitaccen ma’aikacin rediyo ɗin nan Alhaji Adamu Salihu ya yi a kan faifan waƙoƙin ta, inda ya ce waƙoƙin ta sun taimaka wajen saka yara makaranta da iyaye su ka riƙa yi a farkon shekarun 1970 da sama da yara 3,000 a Kano.
Jaafar ya ambato irin gudunmawar da ta bayar ga cigaban harkar ilimi, ya ce ya tabbatar wasu daga cikin yaran da iyayen su su ka sanya a makaranta a wancan lokaci yanzu sun zama farfesoshi.
Ya ce abin baƙin ciki ne a ce wadda ta yi wannan gagarumin aikin ta ƙare rayuwar ta a haka.
Sakamakon rubutun da ya yi, sai mutane su ka dinga kiran sa, su na so su bada tallafi da za a ba zabiyar.
Ganin haka, sai ɗan jaridar ya haɗa ƙarfi da wasu abokan sa guda biyu wajen gudanar da gidauniyar agaza wa Magajiya, wato Musa Abdullahi Sufi da Ibrahim Sanyi-Sanyi.
Nan da nan kuwa mutane su ka shiga tura kuɗin taimako a asusun da su Jaafar su ka buɗe, aka tara kimanin naira miliyan 5.
Su Jaafar sun yi amfani da kuɗin wajen gina wa zabiyar gida tare da saya mata kayan abinci da yi mata tanadi na aƙalla shekara ɗaya.
Tun daga lokacin kuwa ba a ƙara jin ɗuriyar mawaƙiyar ba sai a yau da aka ji labarin rasuwar ta.
Mutane da dama sun yi baƙin cikin rasuwar Magajiya Ɗambatta tare da yi mata addu’ar samun rahama.
Allah ya rahamshe ta, amin.