TASHAR talbijin ta Africa Magic, mallakar kamfanin MultiChoice, na duba yiwuwar shirya fim kan rayuwar matar Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Halilu Buhari.
Shugabar kamfanin a yankin yammacin Afrika, Dakta Busola Tejumola, ita ta bayyana hakan a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2021 a yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da tashar ta shirya a wajen kasuwar bajekoli a Kano, wadda aka kammala a ranar.
A takardar da kamfanin ya fitar, MultiChoice ya ce taron da ya shirya ya samu haɗewa da taron shekara-shekara na ƙungiyar gidajen rediyo da talbijin ta Nijeriya, wato ‘Broadcasting Organisation of Nigeria’ (BON).

Ya ce taron ya samar da dama ga furodusoshi su tattauna kai-tsaye da Africa Magic domin samun tallatawada sayar da hajojin su.
Taron, wanda ya samu halartar sama da furodusoshi 200 daga arewacin Nijeriya, na son samar da hanyar samun riba da nasara ga dukkan masu ruwa da tsaki, a cewar Dakta Tejumola.
Sai dai ba ta bada cikakken bayani kan fim ɗin da ta ce za su shirya kan Aisha Buhari ba.