FITACCEN mawaƙi Nura M. Inuwa ya raɗa wa jaririyar da aka haifa masa sunan matar sa, wato Amina. Sai dai ya yi mata laƙabi da Mifrah.
A jiya Juma’a ne, wato 10 ga Oktoba, 2021, Allah ya albarkaci ma’auratan da samun ‘ya mace.
Nura, ɗan shekara 32, ya bayyana wannan abin farin ciki a saƙon da ya wallafa tare da hoton jaririyar a Instagram kamar haka: “Alhamdu lillah. Allah ya azurta mu da jaririya mace. Allah ya raya mana, ya albarkace ta. Mom and baby are doing fine masha Allah.”

Haka kuma a yau ya wallafa ƙarin hotuna biyu na samɓaleliyar jaririyar tare da bayyana sunan ta da nema mata addu’ar fatan alheri daga masoya. Ya ce, “Assalamu alaikum, ‘yan’uwa da abokan arziki. Ga Amina (Mifrah) a yi mata addu’a Allah ya albarkace ta, ya tsare ta daga dukkan abin ƙi, alfarmar Manzo sallallahu alaihi wa sallam. Allah ya albarkace mu da ‘ya’yan mu duka. Na gode.”
Ɗimbin masoya sun taya Nura murna, kuma sun yi wa Mifrah addu’ar fatan alheri a rayuwar ta.
Yanzu dai Nura da Amina, wadda ya auro daga Katsina a cikin 2017, su na da ‘ya’ya biyu kenan, duk mata. Babbar ɗiyar tasu sunan ta Aisha, amma ana mata laƙabi da Farrah. Shekarun ta uku.
Allah ya albarkaci rayuwar su, ya raya su a bisa sunnar Manzon Allah (s.a.w.), amin.


![]()







